Dubu Jikar Mai Carbi Hausa Novel


 

[7/1, 6:00 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com

FREE PAGE 1

     Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa.

  Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.

   Bisa ga al'adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.

   A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu,  ai ita ma Kakanta ne.

   Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, "Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace." Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, "Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?" Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune  kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, "Me ye a cen ɗin?" Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, "Baffa ne!" Cikin haɗin baki duka suka ce, "Baffa kuma? Wane Baffan?"

   Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, "Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!" Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.

   Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama'a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama'ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba'in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.

   Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.

   Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.

   DA DADDARE

    Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin  bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naɗa rawaninsa ta ɗauki zabgegen carbinsa ta maƙala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinƙa bi har fice daga sashen gabaɗaya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taƙarƙare ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga ƙarfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, "Tabbas rayuwar barzahu daɗi gare ta." Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.

   Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta ɓuya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da ƴar buta a riƙe za ta je banɗaki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durƙushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa ta fara motsa baki cikin addu'a don a zatonta mugun gamo ta yi.

  Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, "Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka." Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin." Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, "Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya." Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.

   Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, "Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa." Inna Furai ta saki salati tana cewa, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe." Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, "Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi'u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana."

    Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, "Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya." Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma'ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta.

   Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, "Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa." Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.

   Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, "Wa nake gani kamar Inna a ƙasa." Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture."

    Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, "Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare." Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.

   Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, "Kada ki yi magana za su yi sama da ke" Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, "Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi." Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,

  "To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu." Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, "Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, "Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita."Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.

Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, "Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?" Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, "Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni." Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya.

   Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma'aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, "Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji." Auwalu ya waigo ya ce, "Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo."

   Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, "Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan." Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari.  Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, "Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?" Dubu ta sake sauya murya ta ce, "Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin." Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, "Wallahi ku faɗa ko meye zan bi."

  Dubu ta maƙale murya ta ce, "Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama." Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, "Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni."

  Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, "Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?" Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, "Na rufe wallahi na rufe." Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, "Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna." A fili Dubu ta ce mata, "Maza tashi tsaye ki rungume bango."  Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango.

  A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, "Gargaɗin yan sama jannati kenan." Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin.

Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.

  Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.

  Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, "Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace."

  Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, "Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba." Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, "A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba." Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi.

   Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, "Larai bisimillah"  Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, "Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka" Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, "Inna ki yi hakuri me kike so?"

   Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, "Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji."
[7/1, 6:02 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 2

          Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, "Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu'a ita ce mafita." Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: "Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba."

Inna Furai  ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, "Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza."  Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, "Ban da ƙaddara da rashin ɗan'uwana da na yi,  me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama'a ɗan'adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan'uwana bai yi miki ba?"

Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi'u ya ce: "Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne  kike haɗa kaya?"

  Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, "Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba.  Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.

Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.

  Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, "Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?" Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, "Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba."

Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, "Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka."

  Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, "Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi'u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama'a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi."

  Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar  jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, "Laƙadi ja'akum... Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau." A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare.

  Tana fita ita ma Lantan ta sa ƙafa ta fito ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruƙo hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, "Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?" Lantan ta fyace majina a haɓar zaninta ta ce, "Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu Ɗan'iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiƙanka Malam Mudassiru." Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum ɗaya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki ƴan bakinciki bantaɓa sanin bakwa ƙaunar aminiyata ba kuma ƙanwar Mahaifinku ba sai yau."Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki.

Ba su da zaɓi haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin ƙaguwa Auwalu ya ce, "Inna za mu iya tafiya yanzu?"

Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya ɗan fara sosa ƙeya sannan Inna Furai ta ce, "Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taɓa musa wa maganarsa ba, sai yau don ƙasa ta rufe masa ido?" Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, "Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. Sharaɗi fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba."

  Lokaci ɗaya suka ɗauki salati gabaɗaya saboda ta'ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, "Inna kin san me kike faɗa kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruɗe ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai ƙara dawowa ba. Sai dai idan shaiɗan ne yake son razanar..."

A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la'anannan Allah?" Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, "Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama."

Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, "Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini."

  Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, "Lantan taɓa ni na ji." Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, "Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri."  Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.

Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,

"Yahanasu lafiya kuwa?" Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, "Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni." Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, "Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?" Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, "Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona." Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, "Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa." Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata.

  Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.

   Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.

  Washegari.

  Jama'ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko'ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.

   Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, "Ina za ki tafi ki bar ni?" Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, "Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba." Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, "Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba." Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, "Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?" (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa  ta zo ƙarshe.

  Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, "Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka." Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, "Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni."  Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita.

Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan  Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.

  Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.

  Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaɗaya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa'azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.

Inna Fuarai ta karkace ta ce, "Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi." Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, "Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare." Auwalu ya rumgumota yana cewa, "Ba za ki mutu ba Yahanasuna" Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, "Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin.

  Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taɓa kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce ɗakin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma'a da su. A wanke suke a goge fari ƙal da su, sai da ta bubbuɗa su ta je bakin katangar banɗaki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saƙale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake ɗanawa wuta tana cewa, "Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da ɗankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige ɗakin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faɗuwa can bakin ƙofa.
[7/1, 6:03 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 3

    Ƙananan yaran da aka bari a ƙofar ɗakuna ban da kiran sunayen iyayensu babu abin da suke yi, ƴan madaidaitan cikinsu waɗanda suka fara sanin ciwon kansu ne suka samawa kansu mafita suka nemi maɓoya. Sauran marasa wayo sai ihu suke suna buga ƙofar ɗakin da iyayensu suka shiga. Yaya Idi saboda firgita bai san lokacin da ya wuce can ƙarshen gadon Inna Furai ba, mutumin da ko falon Inna Furai baya iya ƙwaƙwaron tsayuwa, a cewarsa yana Yayan miji haka sam bai kamace shi ba. Rabon shi da shiga ɗakin Inna Furai tun wata doguwar rashin lafiya da ta yi sama da shekara goma, lokacin da ya je dubata amma a wannan ranar shi ne har tsakiyar gadonta. Ban da ɗigar da gumi babu abin da gemunsa yake yi saboda tashin hankali. Lantan can ƙarƙashin gado ta shige ban da ƴan idanuwanta babu abin da kake iya hangowa, ta ƙwale kai a jikin ƙarfe gado ya fi sau biyar duk don ganin ta ɓoye kanta ba tare da an hangota ba bare tawagar fatale su kawo mata farmaki.

   Inna Furai zaman ƴan bori ta yi zanin jikinta ya jiƙe sharkaf da fitsari don gani take wannan zuwan da Fatalwar nan ta yi zuwanta ne, don a ganinta saɓawa umarnin fatalwar da tayi na sake shayar da ƴaƴanta ne ya sa, fatalwar nan ta yi dirar mikiya domin ƴan sama jannati su tafi da ita. Badariya tuni ta ƙwaƙume Yaya Idi da ke gefenta, duk yanda Badariyya ta kai ga jin ƙyanƙyamin gemun namiji sai ga gumin gemun Yaya Idi na ɗiga a sai tin fuskarta. Gabaɗaya mutanen cikin ɗakin ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Ita ma Dubu tuni ta bi yarima don kar wani ya yi saurin gano shirinta saboda ko kaɗan bata son ta samu matsala, ta tabbata muddin  ta ci gaba da razana su babu wanda zai ƙara koda nan da kwana biyu ne.

  Bayan wasu ƴan mintuna Yaya Idi ya ɗago sai a lokacin ya lura da wacce take gefensa a maƙale da shi suna haɗa ido ya watsa mata harara, da sauri ya matsa gefe yana cewa, "Subhanallah! Astagafirullahi wa'atubu'ialhi ke matsa gefe matsa-matsa" A razane ita ma ta ja baya tana yamutsa fuska alamar ƙyanƙyami, don ita kanta bata san lokacin da ta ƙwaƙume Yaya Idi ba don ta san kowane ne shi. Ya kalli Dubu da ke can bakin ƙofa da yake ita ce ƙarshen shiga sannan ya ce, "Ke Dubu wai da gaske kike kin ga Fatalwar Mamman?" Dubu ta yi wani fakare sai kawai ji suka yi ta rushe da wani irin kuka har tana wani furjin yawu kamar wata ƙaramar yarinya." Yaya Idi ya yi zuru yana kallonta a zuciyarsa yana fatan kada Allah ya sa ta tabbatar da abin da ta faɗa da farko. A ƙagauce Yaya Idi ya sake cewa kamar zai yi kuka, "Ke Dubu wannan kukan ba ke kaɗai za ki yi shi ba ki sanar da mu musan halin da mu kanmu muke ciki."

Dubu ta tsagaita da kukan sannan ta fara cewa, "Na ga fatalawar Baffa ido da ido don har cewa suka yi za su fara ɗaukan Innarmu da Innar su Sabi'u. Kuma wai sun ci alwashin duk wanda ya haure shekara Arba'in a gidan nan sai sun naɗe masa ƙafafuwa kamar alkaki."

Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Inna Furai na jin ance za a tafi da ita da Yaya Babba hantar cikinta ta sake kaɗawa gumi ta ko'ina sai keto mata yake yi. Don har kusan suman zaune ta yi saboda waɗansu irin taurari ta rinƙa gani suna yi mata gizo a tsakar idonta. Tun daga abin da Dubu ta faɗa babu wani abu da Inna Furai ta sake fahimta a ƙwaƙwalwarta, don sama-sama ta rinƙa jin wani yuuuuuu a zatonta wannan abin da ta fara ji ƴan sama jannatin ne suka fara kawo mata farmaki. Cikin fitar hayyaci Inna Furai ta fara cewa, "Ikon Allah Ikon gaske! Kai Auwalu kana ina ne? Ke Larai don Allah a cikinku wani ya ɗauke ni ko a kafaɗe ya fice da ni tun fatalwa bata tafi da ni. Auwaluna! Auwaluna na ci burin ganin Ɗanka amma da ƙyar idan zan samu wannan damar ka kawo mini Yahanasu idan ya so mu tafi da ita ko da Fatalwar sun tafi da mu na yi mata raino a cen barzahun idan ta haihu." Dubu juyawa ta yi ta rinƙa ɓaɓɓaka dariya ƙasa-ƙasa saboda ta lura tuni Inna Furai ta riga da ta fita hayyacinta, don fitsari ma ta yi ya kai sau uku daga shigarsu ɗakin.

Lantan tun da ta ji labarin naɗe ƙafafuwansu kamar Alkaki, ta sake firgicewa wani buhu da ke gefenta ta fisgo wanda yake ɗauke da dawa kusan kwano biyu, bata bi ta kan dawar ba ta watsar da ita a gefe ta fara tura kanta a ciki. Don yanda Lantan take ji da ace akwai hanyar da za ta fitar da ita daga cikin ƙarƙashin gado ta tuni ta fice ta yi hanyar zariya. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zancen naɗe ƙafafuwansu da ta ji ance Fatalwa za ta yi mayar da su kamar alkaki. A duniya babu abin da ta fi so da ƙauna a jikinta kamar santala-santalan ƙafafuwanta, wannan ya samo asali ne sakamakon kirarin da marigayin mijinta yake yi mata akan Doguwa mai tsawon alheri tsawo rabin kyau ƴar fillo.Wannan kirari ba ƙaramin baƙanta zuciyar Lami kishiyar Lantan yake ba saboda ita gajeriya ce, kuma hatta bayan rasuwar mijinsu idan wani abu ya haɗo Lantan da Lami haka za ta yi ta hura hanci tana yi wa Lami habaici. To kuwa idan aka mayar da ƙafafuwanta kamar Alkaki ai ta shiga-uku don ta tabbata idan aka naɗe mata ƙafafuwa, ta san ko tsahon turmin gidansu ba za ta kai tsayi ba.

Lantan bata gama tunani ba ta riski maganar Dubu cikin kuka tana sake cewa, "Kuma har ce mini ya yi a cikin ƴan uwan sa zai aiko a tsotsewa wani ko wata roman da ke cikin Ƙwaƙwalwarsu. Saboda gonar Mahaifinsu da suka taɓa danne masa."

Lantan na jin haka ta ci gaba da karanto duk wata addu'a da ta san ta taɓa biyata a bakinta. Saboda ta san badaƙalar da suka shuka akan gonar Mahaifinsu. Hatta kalmar larabci indai Lantan ta santa a baki  haka za ka ji tana maimaitata ya fi sau goma. Ta yi kiran sallah da tayar da iƙama ya fi sau biyar, idan ta biya addu'ar shiga banɗaki sai ka ji ta fara, "Labbaikallahumma Labaik" Idan ta dire sai ka ji ta sake cewa, "Hayya'alal salah" haka ta rinƙa yin addu'a don neman kariyar Ubangiji, amma addu'a har da ta shiga abin hawa haka ta rinƙa maimaitawa. Tana gamawa sai ka ji ta sake cewa, "Walaƙadkarramna bani adama..." Bata iya direwa sai ta ƙara kamo wata kalmar hatta sunayen Annabawa da Sahabai waɗanda ta san sunansu haka ta rinƙa biyawa.

   Ana cikin haka suka jiyo muryar Baba Munkaila a bakin ƙofar Inna Furai yana cewa, "Lafiya kuwa mutanen gidan nan tun daga babban zaure nake sallama shiru ga ƙananan yara suna ta kuka." Ya ƙarasa maganar yana bubbuga ƙofar ɗakin, da ƙyar Yaya Idi ya ta so ya fara ƙoƙarin zare sakata.

  A can ɗakin Yaya babba dirama ake yi da ita akan dole sai an barta ta fito wai sai dai Fatalwar ta ɗauketa ita da Dubu don ba za ta iya jure rashin Dubu ba. Hadiza da ke riƙe da kubar ɗakin ta ce, "Inno don Allah ki yi haƙuri ki zauna na san Dubu ba za ta zauna a waje ba, kuma ni fa gani nake sharrin shaiɗan ne amma babu wata fatalwa." Yaya Babba ta sake share ƙwalla ta ce, "Kaico rayuwa ban taɓa sanin haka zuciyarki ta ƙeƙashe ba Dije, wannan wacce irin falsafar rashin imani ce? Kowaccenku na riƙe da Ɗanta amma ni kun hanani nemo Marainiyar Allah. An ya kuwa Dije?" Hadiza babu yanda ba ta yi ba amma fir Yaya Babba ta kafe, don ban da ruwan hawaye babu abin da take yi. Hadiza na buɗe ƙofar Yaya babba ta fice da sauri tana ƙwalawa Dubu kira. Da sauri Dubu ta taho aikuwa caraf Baba Munkaila ya damƙi hannunta bayan ya gama jin labarin abin da aka bashi dangane da fatalwa. Yana fisgota ya zuba mata ranƙwashi a ka yana cewa, "Wallahi sam ban yarda da abin da wannan shaiɗaniyar yarinyar nan ta faɗa, ke a gidan uban wa kika ga fatalwa har ta baki saƙo?" Yaya babba na ganin haka ta ƙarasa wurin ƙafar Baba Munkaila ta yi zaman dirshen sai kawai ta fashe da kuka. Gabaɗaya ido ya dawo kanta, Baba Munkaila ya sassauta murya ya ce, "Inno lafiya kuwa?" Yaya Babba ta ɗago ya dubi Mukaila ta janyo hannunsa ta ce, "Ka dake ni kawai Munkaila na ce ka dakeni ka huce takaici. Kaga sai na tabbatar da falsafar rashin mutumcinka yanda ya kamata."

  Baba Abubakar da shigowarsa kenan ya hango taron jama'a yana zuwa ya ga Mahaifiyarsa ce mutane ke zagaye da su. Har ƙasa ya russuna yana tambayar Mahaifiyarsa. Yaya Babba ta share hawaye ta ce, "Allah ya yi maka albarka Garba! Don Allah ka ga ya mini me na tsare wa Munkaila da Dije? Munkaila dai ya fi jin haushina. Garba ka gaya mini wacce tsiya suke tsinana mini, bayan Allah da ma'aiki waye gatana wa zai tsunduma ni a aljannah?"  Baba Garba ya jinjina kai ya ce, "Inna wai me yake faruwa ne? Me suka yi miki?"

"Tsoronsu kake ji da zan yi magana ka amsa ƙasa-ƙasa. A cikinsu ka gaya mini akwai Malam ko kuma akwai ni. Ban da Allah da Manzonsa wa yake ƙaunata, ya hore mini lafiya da abin da lafiya za ta ci?" Yaya Babba ta yi maganar cikin ƙunan rai. Baba Abubakar ya ce, "Ayi haƙuri Inno"

Yaya Babba ta zuba hannuwa biyu tayi tagumi ta ce, "Garba ni wace ce a wurinku?" Baba Abubakar ya bata amsa, "Ke Mahaifiyarmu ce Inno"

"Idan na tsinewa su Munkaila wa billahi sai ta ka kama su ko ba haka ba?"

"Inno abar maganar tsinuwa don Allah." Baba Abubakar ya faɗa cikin sanyin murya. Yaya babba ta kuma rushewa da kuka sannan ta ci gaba da cewa, "Don Allah mecece tsinuwa da zan tsinewa ƴaƴan cikina. Idan na tsine musu na ɓalɓace duniya da lahira ko ina da wasu ƴaƴan bayan ku?" Baba Abubakar ya yi ƙasa da murya ya ce, "Inna don Allah ki yi haƙuri kin ga duk mutane kallonki ake yi."

Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, "Ka yi mini iyaka da Munkaila ko a hanya ya ganni kar ya nuna ya sanni, balle a lahira ya yi gabas na yi yamma. Haƙƙi ɗaya na san Munkaila yana bina, lokacin da aka yi masa shayi (kaciya) don Allah Garba ka biya shi cinyar kazar da na ci, ko ba za ka biya shi ba Garba?" Baba Abubakar ya rasa abin faɗa sai kawai ya girgiza mata kai. Yaya Babba ta ci gaba da cewa, "Me marainiyar Allah ta yi masa da zai ƙullace ta har ya sheganta mini ita? Don Allah Garba ka tambayar mini shi ta wurin da Dubu ta zama shegiya? Ka tambayi munkaila Ni Indo Kakarta ce shegiya ko matattun iyayenta?"

Baƙin ciki ne ya cika Baba Munkaila domin jikansa ya ba shi abin da Dubu ta faɗa ba gaskiya bane saboda ya san wacece ita, amma gani yake meye laifinsa don yana son hukunta Dubu domin ta faɗi gaskiyar magana. Gani yake idan ya yi haka shi zai kawo musu ƙarshen duk wannan guje-gujen da ake yi. Tun da tun farar safiya ya ji labarin abin da ya faru yake tantama akan Dubu don kowa ya san irin hatsabibancinta.

Wata uwar harara ya watsawa Dubu sannan ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, "Yanzu Inno saboda na hukunta Dubu shi ne ya ɓata miki rai? Tun da haka ne na zame hannuna daga cikin sabgarta shi kenan?"

Yaya babba ta wara hannuwa alamun abin ya mata daɗi ta ce, "Sadaƙallahul azeem! Kana jin me ya ke faɗa ko Garba, dama me Munkaila yake yi wa Dubu? Ka gaya mini waye yake shiga lamuran Dubu bayan Allah da manzonsa idan ba ni ba?" Baba Abubakar  ya sake ƙasa da murya ya ce, "To duk na ji wannan Inno amma don Allah ki taho mu tafi ɗaki."

Yaya Babba ta yi biris da Baba Abubakar tana cewa, "Don Allah ka yi mini iyaka da Dije saboda tsoro nake ku tafi ku bar ni da ita a ɗaki ɗaya, kar a wayi gari ta maƙure ni na mutu har lahira." Cewar Yaya Babba tana satar kallon Hadiza.

Rass gaban Hadiza ya faɗi da jin kalmar Mahaifiyarta, da sauri ta ce, "Inno ni kuma? Ni ce zan kashe ki?"

"Duk gidan nan babu wanda ya ƙullace ni yake jin haushi kamar Dije dubi irin kallon da take yi mini, haushina take ji saboda na ce ta buɗe mini ƙofa na je wurin Dubu. Don Allah Garba ka gaya mini me na yi mata ko zargina take akan mutuwar mahaifinku?" Sam wannan maganar bata yiwa duka ƴaƴan Yaya Babba daɗi da cikin yanayin rashin jin daɗin maganarta ya ce, "Haba Inno me kike yi haka ne kowa fa a wurin nan ke yake kallo saboda Allah me mutane za su ɗauka jiya-jiya Mahaifinmu ya rasu amma kina wannan abubuwan." Ya ƙarasa maganar yana dafa ƙafarta.

"Sakar mini ƙafata Garba." Yaya Babba ta faɗa a hassale. Ba musu ya sakar mata ƙafa. Sai kawai ta miƙawa Hadiza hannu ta ce, "Allah ya jiƙanki  ba don kin mutu ba Dije don Allah taimaka min zan koma ɗaki, ko a baƙar zuciyar Munkaila kina ga zai kaini ɗaki?" Hadiza ta girgiza kai tana murmushi, Yaya babba ta ci gaba da cewa, "Don Allah ki ce Garba ya matsa daga gabana ko na fice na bashi wuri." Gefe Baba Abubakar ya matsa Dije ta samu ta lallaɓata suka shige da Yaya Babba ɗaki. Suna niyyar tafiya daga wurin suka ji ƙarar abu tim! Daga bayansu. Da sauri suka waiga sai gani suka yi Inna Furai ce da ƙaton buhunta tana ja Auwalu shima yana ja wai dole a barta ta fita ta yafewa zaman cikin gidan. Ita ma sai da suka sha fama da ita sosai sannan suka samu ta koma ɗaki. Baba Abubakar ya dubi Dubu yace,

"Dubu ince idan muka je da ke za ki iya nuna mana ta wurin da kika ga fatalwar?" Dubu ta gyaɗa kai suna haɗa ido da Baba Munkaila ya watsa mata harara. Shi kansa Baba Abubakar zuciyarsa raya masa take tabbas akwai wanda yake son tsoratar da mutanen cikin gidan tun da wanda ya mutu ya mutu kenan har abada baya ƙara tashi. Dubu suka tasa a gaba tana gaba suna biye da ita a baya, sai wani ɗari-ɗari take ita Allah dole tsoro take ji.

Zu-gar mutane ne suka yi dafifi don ganin ta wurin da Dubu ta ga Fatalwa da idonta. Ita kuwa hakimar kanta sai ƙara girma yake musamman yanda ta ga mutane kowa ambatarta yake ana jinjina mata bisa ga ƙoƙarinta na tunkarar wurin. Daga can hanyar banɗaki suka hango wasu fararan kaya, daga nan wasu suka fara cin burki, sai kuma hular Marigayi Mai carbi da iska take kaɗa ta sama-sama. Mamaki da ta'ajibi ne ya kama su hatta Baba Munkaila sai da ya zubawa kayan ido, ɗaya  tsagin na zuciyarsa na son aminta da abin da Dubu ta faɗa sakamakon kayan da ya gani. Amma yana tuna wace ce Dubu zai ji ya ƙi aminta da komai.

  Baba Abubakar ne ya yi bismillah ya ɗebo kayan yana ƙare musu kallo zuwa can ya kalli Dubu yana shirin yi mata magana, sai kuwa ta zabura tamkar wacce aka ɗanawa wuta. Can bayan Zulfa'u ta maƙale tana cewa, "Baba Habu wallahi tsoro nake ji." Baba Munkaila ya karɓi kayan yana jujjuyawa sannan ya ce, "Amma gaskiya ana raina wa mutane hankali." Baba Abubakar ya yi gaba yana cewa, "Dole mu san abin yi amma tabbas akwai wata a ƙasa. Da alama wani ne yake son kawo yamutsi amma kowa ya kwantar da hankalinsa komai ya zo ƙarshe." Baba Munkaila ya hau muzurai yana zare idanu ya ce, "Koma wane ne ni da hannuna zan ci ubansa don na san na gida ne yake aikata wannan abubuwan. Amma duk wanda yake da hannu cikin wannan tafiyar sai na kusa tsinka shi gida uku." Ya ƙarasa maganar yana yi wa Dubu kallon idan ma ke ce za mu gauraya da ke.

   Kafin wani lokaci tuni maganar fatalwa ta fara zaga cikin garin Ɗangwauro, har da masu isar da labarin abin da bai faru ba. Kasancewar kowa da abin da yake ji shi yake idarwa.

                ************

"Dubu ki kwantar da hankalinki idan ma don wannan ne kamar an yi an gama a wurina. Ba dai ni na haifi Garba ba?" Yaya babba ta ƙarasa maganar tana kallon Dubu cikin sigar lallashi.

Dubu ta tura baki gaba tana cewa, "To ai ke sai an gama magana da ke lafiya ƙalau sai kawai daga baya ki sake shawara, gaskiya ni dai ko ki sa mu koma birni gidansa ko kuma ki ce su dawo garin nan wallahi sai mun fi cin daɗi tun da anan me muke ci kamar ba ke kika haifeshi ba." Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, "Ba zan koma birni ba domin Malam har wasiyya ya bari akan kar mu kuskura mu bar gidan nan to kin ga saɓawa miji haramin ne amma Garba ko ya ƙi ko ya so dole ya dawo gidan nan da zama."

Baba Munkaila ne ya kawo kai zai shiga ɗakin Mahaifiyarsu amma ya ga mutane sun yi carko-carko a ƙofar ɗaki ya tambaya ko lafiya.

Hadiza ta taɓe baki ta ce, "Inno ce suke shawara da Dubu shi ne ta koro mu waje." Haushi ne ya ƙara kamashi don ya san duk iskancin da Dubu take yi Mahaifiyarsu ce take ɗaure mata. Ɗaga labulen ɗakin ya yi suna haɗa ido da Yaya Babba ta ce, "Kai Munkaila ka tara mini ƴan uwanka yanzun nan ina son magana da ku!" Kallon Dubu ya yi ya ga ta yi ɗai-ɗai  a cinyar Yaya Babba, gudun neman magana ya sa bai tanka ba ya amsa ya fice. Don baya raba ɗayan biyu Dubu ce ta kitsa mata wata maganar.

Ba a ɗauki lokaci ba Iyalan Yaya Babba suka cika a ɗakin kowa da abin da yake ƙissimamawa zuciyarsa. Dubu na ganin haka ta saci jiki ta tafi haɗa kayan aikinta domin da alama tana ganin wankin hula zai iya kaita dare, don ta ga mutanen gidan ba su da alamar tafiya.

"Na san za ku yi mamakin ganin wannan taron amma ba wata doguwar magana bace. Gabaɗayanku so nake idan an yi sadakar bakwai kar wanda ya sa ƙafarsa ya fita daga gidan nan akwai babban taron da za mu yi gabaɗaya gidan nan. Musamman kai Garba tun da kaine babba." Yaya Babba ta yi maganar tana ɓata fuska don kar wani ya nemi kawo mata wargi. Suma ganin haka ya sa babu wanda ya musa mata sai dai cikin ladabi ɗayan bayan ɗaya suka ta shi suka fita kowa yana wani lissafi daban a zuciyarsa.

  Baba Munkaila yana lura da duk wani shige da ficen Dubu sai dai kamar yanda ya sa mata ido ita ma tana ankare da shi. Yi ta yi kamar babu wani shiri da take haɗawa don shi kansa a wannan lokaci ya fara rage zarginsa a kanta.

  Tun da yamma ta kawo kai doshin magriba ƙafafuwa suka fara janyewa daga cikin gidan kowa daga alwalar magriba ya riƙe abarsa don kowa a tsorace yake. Wannan dalilin ya sa zaman cikin gidan ya gunduri Hajiya Nafisa Matar Baba Abubakar da iyalanta. Allah ya sani ita dama ba ma'abociyar son zaman ƙauye ba ce, don ta kusa shekara biyar ba ta kwana a garin ba sai dai taje ta dawo a ranar, haka ma daga ɓangaren ƴaƴanta shi ya sa basu cika wani sakin jiki da mutanen gidan ba.

Bayan Sallar Isha'i.

   Daga cen bayan ɗakin Marigayi suka fara jin kiran sallah da muryar Marigayi mai carbi. Kasaƙe mutane gidan suka yi aka rasa mai zuwa kiran Mazan da ke ƙofar gida don sanar musu da abin da yake faruwa. Don kowa hantar ciki ta kaɗa saboda lokacin dare ma bai gama yi ba don ko tara na dare bata yi ba.

  Tana gama kiran sallar ta fara wasa wuƙa ji kake , "Kuyat! Kuyat" Sai da ta ƙara matsowa hanyar cikin gidan ta fara wani irin kuka mai kamar haniniyar doki. Gidan tsit ya yi kamar an yi ruwa an ɗauke tun da Dubu ta ji haka cikin muryar marigayin Kakanta ta fara cewa, "Da alama yau za mu ɗebi mutanen gidan nan da yawa. Amma duk wanda ya cinye tuwon daren yau ya tsira ba za mu taɓa ko ta fatarsa ba."

Daga can ɗakunan mutanen ɗakin nɓa jin haka suka fara kantamar tuwon da ko minti ashirin ba a yi da kwasarsa ba. Da zafinsa suka rinƙa ci saboda tsira daga kaidin tawagar fatalwa. A ɗakin Inna Furai faɗa ne ya ɓarke tsakanin Lantan da Inna Furai akan suɗin kwano har Lantan ta ji haushi ta kwalawa Inna Furai silba a goshi.

Dubu na daga wurin da take laɓe tana jin hayaniyar mutane sai da ta kintaci lokaci, ta fara wani irin nishi mai ban tsoro tana cewa, "Duk wanda ban ji sautin tusarsa ba shima wallahi babu mai hanamu ɗaukansa a daren nan."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 4

        Wannan karon gabaɗaya turus suka yi da jin abin da aka faɗa, kallon-kallo aka fara yi a tsakanin juna kowa da abin da yake nazari a zuciyarsa. Suna cikin haka suka sake jin an ce, "Bismillahir rahmanirrahim bari mu fara ɗauka daga kan ta bakin ƙofa." Ai Dubu bata rufe baki ba sai ji ta yi alamar guje-guje, Yahanasun Auwalu tun bayan sallar asuba da ta shiga ɗakin Inna Furai ba ta sake fitowa ba kuma ta ci alwashin ko da fitsari za ta ji sai dai ta matse abin ta, idan ta kama ma sai ta saki abin ta a wurin. To ashe tsugunne bata ƙare mata ba tun da har fatalwar za ta iya kawo musu farmakin dare har cikin ɗakuna, tun da ta ji an ce za a fara ɗauka daga na bakin ƙofa.

Nabila ƴar wurin Hajiya Nafisa, budurwa ce don ta yi sha tara a shekaru. Turo baki ta yi tana cewa, "Maganar gaskiya Mommy ni fa na gaji da wannan abubuwan kullin abu ɗaya wacce irin fatalwa ana zaune ƙalau bayan kowa ya san babu wata fatalwa a musulunci." Cike da ƙosawa Hajiya Nafisa ta ce, "Nabila ya za mu yi kin san dai ba mu da ta cewa tun da zuwan nan na dole ne ya kama mu haka Allah ya ƙaddara mana." Yaya Babba da ke gefe fuskarta ban da gumi da maiƙo babu abin da take yi, ta dubi Hajiya Nafisa da kallon sheƙeƙe ta ce, "Ke Nafi! Zuman ku a gidan na shi ne ƙaddara? Wallahi za ki ga ƙaddara kuwa ganin idonki. Wannan gidan da kike gani kin zo kenan zuwa sojan badaskare." Tana gama faɗa ta yi ƙwafa a zafafe.  Dubu daga wurin da take ta jiyo hayaniya na tashi kaɗan-kaɗan ta sake shaƙe murya ta ce, "Ƴan sama jannati basa lamintar kuskure don haka za mu fara bi ta kan dabbobin gidan kafin mu fara taɓa mutanen ciki, ina tawagar Fatale ku fara dirowaaaa." A hankali ta lallaɓa da sauri ta buɗe ɗakin zabbin Baba Munkaila. Hannunta riƙe da muciya ta fara buga ƙyauren langa-langar da ke jikin ƙofar.  Nan da nan zabi suka fitowa a tsorace suka fara tsalle da kuka "Ƙurƙet! Ƙurƙet!"  Da yake da hasken wutar lantarki tuni zabbi suka fara bazama suna kuka, Dubu ta sa muciya ta riƙa make kawunansu ɗaya bayan ɗaya. Da ta bugawa zabo ɗaya sai ka ji ya yi ƙara ya faɗi ƙasa. Wannan kukan Zabbin ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen da ke cikin ɗakunan ya yi ba. Shiru suka yi suka zurawa sarautar Allah ido. Kowa da abin da yake ayyanawa zuciyarsa. Sai dai a wannan ƙadamin Lantan ta ci alwashin matuƙar tana da rabon ganin wayewar gari, babu wanda zai hanata tafiya don tun da ta zo duniya bata taɓa ganin masifa da tashin hankali irin wannan ba.

Zabbin nan gabaɗaya haka suka warwatsu suka shiga sauran sashen da ke cikin gidan. Muhsana ita ce ƴar autar Lantan, ta taho daga can sashen Baba Sule ba ta san abin da yake faruwa ba ta hangi Zabbin Baba Munkaila suna guje-guje wanda ya tabbatar mata da alama akwai abin da yake faruwa. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin gawarwakin Zabbi kusan bakwai a ƙasa jini duk ya ɓata wurin. Sai dai har lokacin bata ga wanda yake aikata wannan abin ba, ɗaya zuciyarta ce take raya mata ko dai da gaske Fatalwar da ake faɗa ce ta fara aikinta, yayin da ta ƙara riƙe hannu Ɗanta Salihu don dama yaron ne ya fito da ita zai yi kashi. Ta bayan ɗakin Marigayi mai carbi ta je wucewa ba ta yi aune ba sai ji ta yi an fisgi hannun Salihu, aikuwa kusan tare suka ƙwalla ƙara daga ita har Salihun da ake ja, jan Salihu ta riƙa yi tana yi tana ihun neman agaji amma ba a daina jansa ba. Dubu na ganin Muhsana ta kusa fin ƙarfinta ta raɗa mata muciyar a baya tana cewa, "Ki taho mu yi rayuwar barzahu da ke. Ko ki bani Ɗanki Salihu na tafi da shi, ko kuma na ɗauke ku gabaɗaga." Muhsana bata gama jin ƙarashen maganar ba ta saki hannun Salihu ta yi cikin gida da gudu tana tafe tana sosa wurin da Dubu ta maka mata muciya. Shi kansa Salihu da ba a yi masa komai ba ya gama tsorata, dama jikinsa babu riga babu wando haka ya zuba a guje da tiƙeƙen cikinsa a daidai lokacin aka ɗauke wuta Salihu ya rasa wurin da zai bi haka ya riƙa gware da bango yana make sauran zabbin da suma ta kansu suke yi.

Ihun da Salihu yake yi ne ya tabbatar musu da lallai Fatalwa ta fara zuwa kan bil'adam, tun da; da farko sun ji kukan zabbi. A wannan lokacin Yaya Babba da ƙaramin tsorata ta yi ba don ko kaɗan Dubu bata faɗo mata a rai ba bare ta ambace ta. Lantan da ke ɗakin Inna Furai ta fara hawaye bibbiyu don saboda firgici ta tuɓe kayan jikinta ta sake saka su ya fi sau bakwai. Lokacin da ta riski muryar Muhsana na ihu, kuka ta riƙa yi wiwi don Mushana ita ce autarta. Da ta daina jin kukan Muhsana sai na Salihu wannan ne ya bata tabbacin tuni Tawagar Fatalen sun gama da Muhsana sun koma kan Salihu. Da ƙyar Salihu ya samu ya isa wurin ɗakuna ya fara lalubawa yana kuka, hannunsa ya ɗora akan ƙofar su Inna Furai yana bugawa yana faɗin, "Innaaaaa! Iyaaaa" Lantan na jin haka ta ɗare saman gadon Inna Furai hannunta riƙe da ɗan kanfen Badariyya tana ta tura kai duk a tunaninta rigarta ce za ta saka. Inna Furai wani farfari ta riƙa yi kamar wacce take kan hanyar suma, sai motsa baki take tana addu'a.

  Zabbin da suka tarwatse wasu daga cikin su hanyar waje suka yi, suna kuka a firgice. Dubu tun da ta ga an ɗauke wuta ta haye katanga ta dira ta bayan gidan. Sai ga ta kamar mumina ta wuce shagon Lamarana ta siyo maganin sauro, da sauran wata hamsin ɗinta. Zuwanta ƙofar gidansu ya yi daidai tashin Baba Munkail kenan yana kaɗa Zabbin da ya ga suna tsalle suna fitowa ɗaya bayan ɗaya.  Mutanen wurin ne suka fara taya shi, Dubu na zuwa ta zabga uwar sallama, ta yi haka ne saboda Baba Munkaila ya ganta don ta sake cire zarginta da yake daga kanta.

Cikin masifa ya fara yi mata magana, "Dallah sakarai matsa kina gani zabbina na fitowa sai wani ya ɓace a cikin duhu." Da sauri ta matsa gefe ta ce, "Baba Munkaila don Allah ara min fitila na kaiwa Inna Maganin sauronta tsoron soro nake." Ci kanki bai ce mata ba har suka samu suka kame zabbin, ban da masifa babu abin da Baba Munkaila yake yi, don a duniya idan kana son ganin ɓacin ransa cikin gaggauwa ka taɓa masa zabbinsa ko kuma wani laulawar keken hawansa. Yana gaba Dubu na biye da shi sai mutum uku da suke riƙe da zabbin nasa. Faɗa yake ta saki yana cin alwashi ga duk wanda ya buɗe masa Zabbi sai ya yi masa rashin mutumci. Suna shiga tsakar gida Baba Munkaila ya hasko gawar wasu zabbi biyu daga bakin ƙofa. Nan take cikinsa ya bada sautin ƙululululu! Jikinsa ne ya ɗau tsuma wani gumi na keto masa ta ko'ina, watsar da na hannunsa ya yi; ya kwasa a guje.

Yadda jaruman Indiya suke kwasar gudu idan sun yi tozali da masoyansu haka Baba Munkaila ya watsar da zabbin hannunsa ya kwasa da gudu har da wata uwar ƙara yana zuwa ya zube a wurin ya suri Gawarwakin zabbin ya rungume yana sauke ajiyar zuciya mai zafi, haɗe da haɗiyar wani irin yawu mai ɗacin gaske.

Kamar mai shirin yin kuka haka Baba Munkaila ya rinƙa shafa matattun zabbin yana cewa, "Don Allah wanene ya yi mini wannan ɗanyen aikin. Wallahi duk wanda na kama yana da hannu a ciki sai na ci ubansa." A daidai lokacin Dubu da sauran mutum ukun da ke riƙe da zabbinsa suka ƙaraso. Dubu ta yi tsaye tana kallon yanda gumi ke ɗiga daga jikin Baba Munkaila. Yana ɗagowa ya maka mata duka yana cewa, "Don Ubanki za ki kamo mini sauran ko su ma sai an kashe mini su." Kamar mai jira haka Dubu ta sheƙa da gudu kamar gaske tana dariya ƙasa-ƙasa. Daga can ɗan nesa Baba Munkaila ya fara hango ƙaramin yaro yana tafe yana jan ƙafar wata ƙatuwar zabuwa, wacce da alama ita ce uwar garken ciki. Salihu yana tafe yana murmushi yana zuwa ganin Baba Munkaila na riƙe da sauran zabbin ya sa ya miƙa masa yana sake yaƙe baki yana cewa, "Baba an ci kaza." Kusan suman zaune Baba Munkaila ya yi, ya ƙurawa Salihu ido ya ganshi tik ko wando babu. Cikinsa ya yi kurcici sai sheƙi yake da maiƙon abinci. Baƙin cikin ne ya kama Baba Munkaila ya dubi Salihu murya a daƙile ya ce, "Kai a ina ka gano wannan?" Salihu ya juya bayansa ya nuna ya sake cewa, "Baba an ci kaza"

A fusace Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, "A gidan uwarka za a ci kaza?" Salihu ba ƙaramin tsorata ya yi ba don haka ya saki zabon hannunsa jikinsa na rawa. Baba Munkaila ya sake ɓata fuska ya ce, "Waye ya kashe mini zabbi ko kaine?" Tsoro da ganin yanda Baba Munkaila ya ɓata fuska ya sa Salihu bai yi wata-wata ba, ya ce, "Ni ne a cen"

Baba Munkaila zuru ya yi yana kallon Salihu kamar wanda ya yi tozali da sabuwar halitta, ya sake haɗiyar yawu mai ɗaci murya a daƙile ya ce, "Wato kai ka buɗe daga keji suka fito ko?" Salihu ya gyaɗa kai wannan karon har da murmushinsa na ƙarfin hali ya ce, "Ni a Umma ne..." Haushi ya sake kama Baba Munkaila ya ji kamar ya shaƙe wuyan Salihu. Kawai sai ya miƙe ya damƙi hannun Salihu ya juya ba walawa ya cewa mutanen da suka rako shi ciki, "Malam Hamza ga kejinsu ku zuba su a ciki." Mugun kallo ya watsawa Dubu don Allah ne ya taimake ta ba ta yi wani laifin ba da ragowar fushinsa a kanta zai sauke.

Yadda Baba Munkaila yake fusgar hannun Salihu ba ƙaramin tausayi da dariya zai baka ba, yana zuwa wurin ɗakunan ya fara kwaɗawa Muhsana kina. Sai dai babu motsin wanda ya ji hasalima ƙofar ɗakunan gabaɓaya a rufe suke. Haushi da ya kama shi ya hau buga ƙofofin ɗakuna yana faɗin,

"Wai lafiya kuwa mutanen gidan nan wannan wanne irin abu kuke yi ne." Wannan bugun ƙofar ba ƙaramin razana Salihu ya yi ba, don haka ya fara tsanyara kuka yana murza idanu tare da wurga tsilla-tsillan ƙafafuwansa. Cike da takaici Baba Munkaila ya tallaƙe ƙeyarsa yana cewa, "Rufe mini baki don ubanka. Shegen yaro mai siffar ƴan ruwa."

Dukan da Baba Munkaila ya yi wa Salihu ba ƙaramin ratsa kansa ya yi ba don haka ya kuma fashewa da kuka. Lantan da ke cikin ɗaki ta kuma zabura tana cewa, "Innamal A'amalubinniyati..." Sai kuma ta hau gado ta sauko, sannan ta sake cewa, "Sadaƙallahul azeem. Kuna ji fatalwar nan har rikiɗa take yi za ta yaudare mu, mu buɗe mata ƙofa." Inna Furai da ta yi ɗai-ɗai a ƙasa ta ɗauko wani rawanin Marigayi  Mai carbi, ta ƙadandane shi tana numfarfashi ta ce, "Ni dai na san idan da zazzagar amana to babu makawa fatalwar nan koda ta shigo ba za ta illatani ba. Wannan rawanin tun na ranar aurenmu ne wannan kaɗai ya isa shaidata..." Bata ƙarasa sambatun ba suka ji bam Baba Munkaila ya ɓallo ƙofar, ya koma ta ɗakin Yaya Babba ita ma ya ɓalle ta. Nan fa suka yo carko-carko masu ihu na yi masu gudu suma suna yi. Tsawar da Baba Munkaila ya buga ce ta saita nutsuwarsu, yana huci ya nuna Salihu da ke rarraba idanuwa ya ce, "Ina uwar yaron nan?" Tsit suka yi aka rasa mai magana sai Lantan da ke zare idanu ta ce, "Ai Muhsana kam tuni Fatalwa ta daɗe da gamawa da ita..." Da sauri ya katse ta da cewar, "Don Allah Inna Lantana ki rabani da zancen fatalwar nan. Ku duba irin ɓarnar da aka yi mini." Ya ƙarasa maganar yana haska musu gawarwakin zabbinsa.

Yaya Babba da fitowarta kenan ta zuba kabbara tana cewa, "Kazalika mun ga tabbaci wallahi ya tabbata fatalwa na bibbiyarmu a gidan nan. Dama fa kafin su aiwatar sai da suka faɗi cewar za su fara ta kan dabbo. Don Allah ku kira mini Garba don idan na ƙara kwana a gidan nan ba Mai Jama'a ne ya haife ni ba."

Ana cikin haka sauran Mazajen gidan da ke zaune a ƙofar gida suka shigo sakamakon Malam Hamza ya sanar da su abin da suka gani. Ganin su Yaya Babba carko-carko a tsaye ya sa su tambayar ba'asi, nan take aka sanar musu Baba Munkaila ya kora musu jawabin zabbinsa. Cikin Baba Auwalu da na Baba Sule kusan lokaci ɗaya ya kaɗa, tuni gumi ya wanke musu fuskoki. Nan fa aka shiga tausar Baba Munkaila akan ɓarnar da aka yi masa sannan magidantan mazan suka ci alwashin ɗaukan mataki a cikin gidan. Baba Abubakar da kansa ya fita ya sanarwa ƴan bijilanti abin da yake faruwa ya basu umarnin kula da gidan tun daga bayan gidan har zuwa cikinsa.

Lantan duk wannan matakin da aka ce za a ɗauka bai yi mata ba, don ta kasa ta tsare akan dole sai ta tafi a daren sai da Baba Abubakar ya lallaɓata sannan ta amince da sharaɗin gari na waye za ta kama gabanta. Hajiya Nafisa na jin haka ita ma ta yi tsalle ta ce washegarin ranar za ta tafi don ba za ta ƙara kwana ba. Gabaɗaya suka ɗunguma zuwa sashen Auwalu da ƙyar can ma aka samu suka buɗe ƙofofi don Muhsana sai da ta suma ya kai sau Uku, da ta farfaɗo idan ta ce ina Salihu? Suna ce mata baya nan take sake zubewa.

Duk plan ɗin da ake shiryawa Dubu ta yi fakare tana sauraronsu, kuma zuciyarta ƙal da ta ji kowa ya ce zai koma inda ya fito.

Sai dai suna haɗa ido da Nabila sai ta bushe da dariyar mugunta tun Nabila bata lura ba har ta fara fahimta. Faɗa suka yi kace-kace har Nabila ta cewa Dubu, "Ballagaza ƴar ƙauye." Buɗar bakin Dubu kuwa ta ce mata, "Ubanki ma ɗan ƙauyen ne kuma kema kin dawo nan har abada." Tsautsayi ya ja Nabila ta kifawa Dubu mari nan take kuwa Yaya babba ta yi tsalle ta dire ta fara faɗa daga ƙarshe har ta ce a kira mata Baba Abubakar.

Ran Mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, don a ganinta hukuncin da Nabila ta ɗauka shi me daidai.

Baba Abubakar cikin ladabi ya je gaban Yaya Babba ya ce, "Inno an aiko kina kirana."

Nuna masa Nabila ta yi tana ɓata fuska ta ce, "Garba don Allah ka gaya mini kana da wani ƙauyen da ya wuce wannan?" Baba Abubakar ya girgiza kai ya ce, "Babu Inno."

"Ka gaya mini ni da Marigayi mahaifinka muna da garin da ya wuce nan?" Yaya babba ta faɗa fuska a gaɗe.

"Babu Inno mai yake faruwa ne?"

"Ƴarka za ta makanta Dubu akan ta ce mata Ubanta ma ɗan ƙauye ne, don Allah meye aibu a nan? To tun wuri ka yi musu tsakani don ba za ta nakasa mini jika ba. Tun zama bai kankama ba har anfara kai ga haka, ina ga in sun kwaso kayansu sun dawo nan gabaɗaya." Nabila ta kalli Yaya Babba a fusace ta ce, "Allah ya sawaƙe wa zai dawo nan da zama..." Tun bata rufe baki ba Mahaifinta ya ɗauke ta da mari don tun kafin su zo yake gargaɗinsu akan taɓa Dubu don ba abu ne mai wuya da zai ɓata ran mahaifiyarsu ba. Marin ba ƙaramin shigar Nabila ya yi ba don haka ta fashe da matsanancin kuka, ita kanta Mommy sai da marin ya taɓa ta dukda ba ita aka yi wa ba.

Yaya Babba ta ɗebi sallati tana tafa hannuwa rai a matuƙar ɓace, ta nuna Baba Abubakar ta ce, "Garba a gabana za ka illata mini jika ina ji ina gani. An ya kana ƙaunar Nabila kuwa? Daga na ce ka yi wa yarinya faɗa shi kenan sai ka kashe ta da mari. Don Allah meye mari ana zaune ƙalau? Wallahi idan ka sake shigowa ɗakin nan Garba sai na watsa maka falsafar rashin mutumci. Don Allah Dije ki fice mini da Garba daga ɗaki tun ban fice na bar masa ba." Yaya Babba ta share ƙwallar idonta ta dubi Baba Abubakar da ke niyyar miƙewa ta ce, "Garba ka fita daga sabgar jikata Nabila wallahi idan ba haka ba sai na saɓa maka." Ya russuna cikin girmamawa ya ce, "A yi haƙuri dai Inno." Biris ta yi ta rabu da shi, ita kuwa Mommy ta cika fam kamar za ta fashe sai harare-harare take, don ma Yaya babba bata lura da ita. Dubu ta raɓe ta gefe tana yi wa Nabila gwalo, ai kuwa karaf akan idanun Yaya Babba.

  Da sauri ta riƙe haɓa da hannu bibbiyu cikin mamaki ta ce, "Ke dai an yi makirar yarinya. An ya Dubu halin Ahmad kika yi kuwa wallahi wannan baƙin halin sai dai idan na Kulu ne..." Tun bata rufe baki ba Dubu ta ce, "Ni dai ki daina zagar mini iyaye tun da ba su yi miki komai eheee." Yaya Babba na jin haka ta rushe da kuka tana ƙwalawa Baba Munkaila kira.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 5

      Da sauri Baba Munkaila ya juyo yana muzurai don har lokacin banda huci babu abin da yake yi. Tun kafin ya ƙaraso Dubu ta riƙe hannun Yaya babba tana bata haƙuri, don duk cikin gidan babu wanda Dubu take tsoro kamarsa. Zuciyar Hajiya Nafisa fes don ko ba komai ta san zai gyarawa Dubu zama, yana ƙarasowa ya ce, "Inno ga ni." Yaya babba ta kalli Dubu da ta yi wuri-wuri sai zare ido take yi saboda gari banza ma Baba Munkaila ba ya raga mata ina ga yau da yake cike da haushin kashe masa zabbinsa.

Yaya babba ta ɗauke kanta daga wurin Dubu tana cewa, "Munkaila don Allah ka raba ni da yarinyar nan Dubu, ni take son yi wa ɗiban albarka. Wai don Allah meye dalilin da ya sa ba za ka tafi da ita sashenka ba..." Tun bata gama magana ba Baba Munkaila ya zuba mata ranƙwashi a ka. Ai kuwa ta daka uban tsalle ta faɗa uwar ɗaki. Ganin haka ya sa Yaya babba ta sallame shi amma sam ba haka Hajiya Nafisa ta so ba.

Cikin Dare.

   Tun dare bai gama tsalawa ba ƴan bijilanti suka yi wa gidan Marigayi mai carbi dirar mikiya, hannuwansu ɗauke da gorori sai fitilun da suke haskawa masu ɗan karen haske. Ban da haske-haske babu abin da suke yi, da sun ji motso ko na dabbobin gidan ne za ka ga sun haske sun nufi wurin da gudu. A wannan ranar ma Dubu da wuri ta yi kwanciyarta don ta samu damar gabatar da aikinta idan ta farka ciki dare. Sai dai wannan karon tsoro ne mamaye a zuciyarta saboda irin gororin da ta gani a hannuwa su Duna da Kuraye. Tana son suma ta nuna musu iyakarsu amma tana shakkar ta inda za ta ɓullowa lamarin saboda sun zagaye ko'ina ga fitilun da suke haske-haseke da su.

Dabara ce ta faɗo mata don har sai da ta murmusa a fili saboda mugunta. Ta shi ta yi a hankali cikin sanɗa ta ɗauko butar Yaya babba sai da ta zo daidai kan Barira wacce take kwance da Ƴarta ta tsiyayawa yarinyar a jikinta , idan ka ga yanda ta yi sharkaf sai ka rantse da Allah fitsari ta yi. Ɗaga rigarta ta yi ta zaro guntun likkafanin da ta ɓoye sai ta ɗaura a ƙafar Baraka ƴar wurin barira. A hankali ta fara jan ƙafar yarinyar har sai da ta kaita ƙofar ɗaki, ta koma ta riƙa jan ƴaƴan mutane tana kaisu bakin ƙofa sai da ta gama sai kawai ta haɗa ƙafafuwa su ɗai-ɗai ta riƙa ɗaurewa da likkafani. Sai da ta kai kusan yara biyar bakin ƙofa sannan ta janyo tsintsiyar kwakwa ta tsinka ta riƙa bi tana kartawa iyayen da yaran, da sauri ta bi gefe ta wurin da yaran suke kwance a bakin ƙofa ita ma ta yi luff ta tura ƙafarta ciki tasu. A hargitse mutanen ɗakin suka tashi carko-carko suka fara wawurar fitila, Barira na haska fitilarta a ka hango yaran suna firƙai-firƙai suna koke-koke. Kowacce da sauri ta je ta rarumi Ɗanta ai suna ganin Likkafani a ƙafar ƴaƴan kowa ya fara shan jinin jikinsa.

Maraƙisiyya ta dubi Barira ta ce, "Don Allah Barira me idona yake gane mini kamar likkafani." Barira dama bakinta ƙunshe yake da magana don dai tana tsoron furtawa a samu matsala, ai kuwa tana jin haka ta yi farat ta ce, "Lashakka fihi wallahi likkafani ne don Allah ku taimaka mana fatalwar nan za ta ja mana yara." Jin wannan maganar ta Barira da sauran hayaniyar mutanen ɗakin ya sa Ƴan bijilantin suka tattaru a ƙofar ɗakin Yaya babba suna tambayar ba'asi. Dubu na ganin haka ta zari buta tana matse-matsen ƙarya wai fitsari take ji, da sauri Yaya Babba ta yi farat ta ce, "Dubu ki raba ni da wannan ƙaddararran fitsarin da za ki yi yanzu, so kike ki fita fatalwar nan ta yi gaba da ke?" Dubu ya sake zabura tana buga ƙafa ta ce, "Wallahi fitsarin ya matse ni."

Barira ta wurga mata fo ɗin Sa'ima ɗayar ƴar tata ta ce, "Maza hau fo ki yi amma babu in da za ki." Wata uwar harara Dubu ta watsa mata ta ce, "Allah ya sawaƙe a gabanku da su Duna zan yi fitsarin ni dai wani daga cikinku ya raka ni." Haushi ya ƙule Yaya babba ta zabga mata carbinta da bacci ya kwashe ta yana hannunta ta ce, "Wallahi idan kin ga fita ta ko ƙofar ɗakine ba Mai jama'a ya haife ni ba." Dubu ta dubi Kuraye ta ga yanda yake ta Muzurai yana hange-hange shi a dole ga wanda yake fagen fama. A zuciyarta ta ce, "Wallahi kuma sai kun kwashi rabonku dan ubanku." Ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka ta ce, "Inna don Allah ki ce Duna ya sa ɗaya daga cikin yaransa ya raka ni." Duna na jin haka kansa ya ƙara fasuwa don a duniya babu abin da Duna yake so yake ƙauna sama da a fasa masa kai yana fagen aiki. Don idan ya saka uniform ɗin su na Ƴan bijilanti har ji yake ya fi wani Major general ɗin na Sojoji. Don haka cike da izza ya fara buɗa kafaɗa ya ce, "Babu damuwa  muje zan raka ki. Ba fatalwa ba ko Aljan ne idona idonsa sai na ɗaye masa fata daga ƙafa har ƙeya."

Dubu na gaba ya yi yana haske mata fitila suka fita daga cikin ɗakin, sauran yaransa kuma suna tsaye a bakin ƙofar sai dai gabaɗaya yanzu sun kasa taɓa likkafanin da suka gani yashe a gefe wanda ake ce musu fatalwar ce ta ɗaure ƙafafuwan yaran da shi.

  Sai da suka yi ta fi me ɗan nisa da yake banɗakin na da nisa da wurin ɗakuna kamar yanda al'adar ginin ƙauye yake. Suna ratsewa ta bayan ɗakin Marigayi Dubu ta zabga ihu tana yin gefe da sauri haɗe da faɗin, "Wayyo Allah hannuna." Durƙushewa ta yi a ƙasa tana murza hannu haɗe da yamutsa fuska. Duna ba ƙaramin tsorata ya yi ba don idan idonsa ba gizo yake yi masa ba gani ya yi kamar wurgar da Dubu aka yi gefe. Gyaran murya ya yi yana kallon hagu da damansa a ɗan tsorace, amma sai ya basar don kar Dubu ta fahimci tsoron da yake ciki ya ce, "Ke Dubu lafiya, me ya samu hannun naki?" Dubu da ke satar kallonsa ta gefe ta sake shafa hannu ta ce, "Wani abu ne mai kaifi kamar farata na ji yana niyyar fisgata daga baya sai ji na yi an hakaɗa ni."

Wata irin karta cikin Duna ya yi nan take gumi ya fara neman game jikinsa amma sai ya ɗaga gorarsa yana ƴan haske-haske ya ce, "Yana daga wurin ina." Kusurwar ɗakin Marigayi mai carbi ta nuna ta ce, "Daga can ne." Duna ya coge daga wurin da yake ya ce, "Wuce mu je ki nuna min to."

Dubu tsabar mugunta ji ta yi dariya na neman suɓuce mata don haka ta miƙe sai kuma ta fara tafiya a dudduƙe tana riƙe ciki alamar fitsari ya matseta. Ganin haka ya sa Duna ya ce,

"Fitsari ko? Wuce muje idan mun dawo ma duba koma meye." Shima da biyu ya faɗi haka saboda a lokacin da za a kuma yin wani ƙwaƙƙwaran motsi mai ƙarfi yana iya fita da gudu. Suna zuwa ta shiga banɗaki ta yi fitsari ta fito don kafin ta fito tuni Duna ya ƙagu saboda gani yake kamar wani abu zai kama shi. Suna tafe har suka bar wurin banɗakin suna yin gaba Dubu ta buga tsalle tana cewa, "Duna kanka ga shi nan zai warci kanka." A guje Duna ya zuba yana ƙwalla ƙara haɗe da dafe kansa, don fitilar hannunsa sai da ta yi tsalle uku sannan ta tarwatse a ƙasa, batiran ciki suka yi gabas, kan fitalar ya yi yamma. Gangar jikin fitilar ta yi arewa gorar hanunsa ta yi Kudu. Dubu na ganin haka ta rufa masa baya sai dai tun a tsakar gida suka raba hanya don tuni Duna ya dafe katanga ya dire yayin da Dubu ta yi cikin ɗakin Yaya Babba a guje, Yaran Duna na ganin haka suma suka zuba a guje kowa ya kama gabansa. Su Barira da sauran mutane ɗakin Yaya babba suka hau gwara kan ƙananan yara aka rinƙa ƙwallo da su kamar yanda ake gara ƙwallo a filin wasa. Cikin ɗakin ban da kukan yara da ihun manya babu abin da yake ta shi a ciki.

Daga ɗakinsu Inna Furai suma tashi suka yi don tun lokacin da suka ji ihunsu Barira, gabaɗaya suka watssake. Lantan ce ta fara miƙewa a zabure mai bin bayanta Inna Furai sai kuma ragowar mutanen ɗakin kowa ya yi tsuru-tsuru. Jin maganar ƴan bijilanti ne ya sauƙaƙa musu damuwar da suke ciki. Sai dai ihu da gudun Duna ya yi ya fi komai kaɗa musu ciki don, a wannan lokacin sun gama sadaƙƙarwa da indai Fatalwar ta fafake su babu mai tsira daga hukuncinta. Lantan hawaye ne ke zuba a kan dakalin fuskarta ga wani irin kaɗawar ciki da take fama da shi. Cikin kuka ta dubi Inna Furai ta ce, "Furaira sai da na gaya muku ku bar ni na tafi amma aka hanani tafiya ni da zuri'ata, yanzu don Allah idan tsautsayi ya ritsa da ni fa? Maganar gaskiya idan na mutu ta wannan hanyar ranar gobe ƙiyama sai an yi mana hisabi da Garba don shi ne sila." Ta ƙarasa maganar tana son jin ta bakin Inna Furai amma sai gani ta yi ta zura mata ido tana kallo, Lantan dafa mata hannu ta ce, "Furaira ko bakya ji na ne?" A wannan karon ma gani ta yi Inna Furai ta sake zura mata ido tana kallo ko ƙiftawa bata yi ba. Lantan na jijjiga Inna Furai sai gani ta yi baya luuu!

Lantan ta zuba kabbara haɗe da cewa, "Innalillahi yau me nake gani haka jama'a ku taimaka mana wallahi sun fara ta kan Furaira." Nan fa suka ƙara ruɗewa sai Mardiyya ce ta yi ƙarfin halin yayyafa mata ruwa don ta fi zargin Inna Furai suma ta yi. Inna Furai na farfaɗowa suka fara jero mata sannu sai ji suka yi tana amsawa da,

"Ashhadu'anlla'ilaha'illallahu, wa'anna Muhammadarrasulillahi."

Lantan ta yi sauri ta ce, "Furaira me kike faɗa ne?"

Inna Furai da bata cikin hayyacinta ta ce, "Wa saumu ramadana. Amma Hajji kam sau ɗaya na taɓa ziyarta." Lantan rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da matsanancin kuka tana yi tana fatar majina ta ce, "Tun da Uwata Mai carbin Malam ta haife ni ban taɓa ganin ƙadaddararrun ranaku kamar waɗannan ba kai jama'a yanzu Furaira daga suma sai hauka." Inna Furai bata san me ake yi ba don haka suka ƙarasa ganin daren har zuwa asuba Inna Furai na yi musu sumbatu.

  Washegari.

  Tun asuba da mazan gidan suka fito aka sanar da su abin da yake faruwa, don tun da suka wayi gari da ganin gororin ƴan bijilanti da fitilar Duna sai kuma takalmin ɗaya daga cikinsu, suka tabbatar da babu lafiya. Da aka sanar da su abin da yake faruwa wasu daga cikin mazan zuciyarsu ta fara aminta fa zancen fatalwar, saboda dama da Auwalu da Baba Sule tuni suka aminta da abin da aka sanar da su. Ba shiri aka ɗauki Inna  Furai aka wuce da ita asibiti, saboda jikinta wani irin zafi da ya yi ga sumbatu ta take yi ba kai ba fasali.

Kaso casa'in da tara na mutanen da suka halarci gidan mutuwar a wayewar garin duk suka ɗaɗe kowa ya kama gabansa. Lantan dama ko sallama ba ta yi musu ba tana idar da sallar asuba ta fice ko jakar kayanta bata ɗauka. Ta so ta yi wa Autalliyarta magana ta ɗauko Salihu su tafi amma gani take ko ya ta ƙara ƴan sakanni komai zai iya faruwa. Wannan lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Dubu, don gabaɗaya gidan abin da ya rage daga ƴaƴa sai jikokin gidan. Wasu daga cikinsu har sun yi niyyar tafiya aka ce su bari a ga yanda jikin Inna Furai zai yi. Yaya Babba ta sake jaddadawa ƴaƴanta tana son zama da su idan komai ya daidaita akwai maganar da za su tattauna mai muhimmanci.

Wannan zaman da aka ce za su yi ba ƙaramim ɓata ran Hajiya Nafisa da Hajiya Fauziya ya yi ba. Ita kuwa Hajiya Rahama ko a jikinta damuwarta ɗaya fargabar da suke ciki ta rashin kwanciyar hankali.

Asalin Zuri'ar Mai Carbi.

   Asalinsu mutanen garin Kano ne cikin ƙaramin ƙauyen Ɗangwaro dake jihar Kano. Mai carbi Su biyar ne a wurin Mahaifi da Mahaifiyarsu. Maza uku mata biyu amma acikinsu saura Mutum Uku rayayyun. Yaya Idi, Malam Munzali sai Lantan wacce dama ita ce ƴar autarsu. Sunan Yaya Babba Aisha wacce aka fi yi wa laƙabi da Indo. Ƴar uwar Marigayi Mai carbi ce ta fannin Mahaifinsa ƴar maza zar suke, an yi musu auren zumunci suka zauna anan cikin garin Ɗangwauro.

Inna Furaira ita ce matarsa ta biyu ita ma ƴar uwarsa ce ta ɓangaren Mahaifiya, ita ma auren zumunci aka yi musu sakamakon Mahaifiyar Mai carbi ta nuna itama dole ya auri ƴar ƙaninta tun da ya auro ƴar ƙanwar Mahaifinsa. Wannan dalilin ya sa aka sake yi masa aure bayan yin aurensa da shekara biyu a lokacin Yaya Babba tana goyon Baba Abubakar.

Ƴaƴan Yaya babba Shida Maza biyar Mace ɗaya. Akwai: Baba Abubakar, Baba Munkaila, Baba Sule, Baba Shehu, Baba Aminu, Baba Adamu sai Hadiza. Inna Furai tana da ƴaƴa biyar akwai: Larai, Baba Sabi'u, Baba Musa, Baba Sha'aibu sai Baba Auwalu.

Gabaɗaya waɗannan ƴaƴayen kowanne yana da tashi zuri'ar, daga cikin waɗanda ba sa cikin gidan gandun, akwai Baba Abubakar Mazaunin unguwar Na'ibawa, kuma lakcara (Lectural) ne kwalejin Sa'adatu rimi. Sai Baba Adamu.

Baba Abubakar yana da mace ɗaya Hajiya Nafisa da yara Huɗu: Aseem, Nabila, Husna da Humaira. Aseem da Humaira sunan Mai carbi da Yaya babba suka ci amma ana kiran Humaira da Ummi. Baba Adamu yana zaune a unguwar Gyaɗi-gyaɗi likitane yana aiki a asibitin Aminu Kano. Yana da mata biyu Hajiya Rahama ita ce Uwar gida tana da ƴaƴa biyu Fahad da Fatima sai Hajiya Fauziyya mai ƴaƴa uku Halifa mai sunan Marigayi Mai carbi, Zainab sai Hafsa. Sai Hadiza da Larai da suke aure a wasu gidajen.

Tsayawa zayyano wannan ahalin Marugayi mai carbi ba ƙaramin ɓata lokacin mai karatu bane.

Dawowa Labari.

Kimanin sha biyun rana da ƴan mintuna, zaune yake a cikin motarsa yana ƴan danne-dannensa. Ya kai kimanin mintuna ashirin  da faka motar amma yana ciki bai fito ba. Ɗaiɗaikun yara ne suka fara zagaye motar suna kallo wasu daga cikinsu har da masu shafawa. Tsirarin ƴan mata sa'annin Dubu har da masu kallon fuskarsu a jikin mudubin motar, ganin suna niyyar yi masa ɓarna ya sa ya zuge galashin motar. Wani sihirtaccen ƙamshi ne ya fito daga cikin motar nai sanyin ƙamshi. Ƙamshinsa ne ya ankarar da su akwai mutumin da ke cikin motar. Kallon su ya fara yi kowa ya shiga taitayinsa sakamakon ganin fuskarsa ko ɗigon murmushi babu. Mugun kallon da ya wurga musu ne ya sa kowacce daga cikinsu ta kama kanta, sum sum sum suka wuce. Gajiya ya fara yi da zaman motar sannu a hankali ya zuro ƙafarsa waje tare da fitowa ya jingina da jikin motar yana ƴan danne-danne a wayarsa. Kakin sojan ba ƙaramin ƙarɓarsa ya yi ba, ya yi kyau matuƙa ga wani kwarjini da yake da shi.

Kasancear mutanen ƙofar gidan sun watse sakamakon ruɗanin da yake faruwa wasu daga ciki kuma sun tafi asibiti wurin Inna Furai.

Lambar mahaifiyarsa ya kira sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗauka. Kamar zai yi kuka ya fara yi mata magana: "Momma don Allah ki zo ki shigo da ni banga su Daddy ba kuma na san gidan cike yake da mutane..." Bai ƙarasa magana ba Baba Munkaila ya ƙarasa wurinsa yana washe baki ya ce, "Wa nake gani kamar Soja? Soja mazan fama saukar yaushe." Zame wayar ya yi yana sosa kai ya ce, "Yanzu na ƙaraso Baba."

"Bismillah mu je ciki mana" Baba Munkaila ya nuna masa hanya. Sai da ya kulle motar sannan suka ƙarasa cikin gida.

Dubu tun a hanya su Kaltume suka tare ta da zancen baƙon da suka yi. Hura hanci ta yi kanta na ƙara girma sannan ta ce, "Wani dogo mai mota baƙa? Yau ma da kayan sojoji yazo ko?" Har rige-rigen bata amsa suke sannan ta tallaɓi ƙwaryar tsakin da ta karɓo ta fara buɗa kafaɗa tana cewa, "Ai shi ya sa nake gaya muku duk shegen da ya kawo raini wallahi haɗa shi da Yaya Aseem zan yi ya ci ubansa. " Tana gama maganar ta yi gaba. Su kuwa kowa ya yi zuru-zuru don basa manta ranar da suka taɓa ganinsa da bindiga.

Dubu cike da ɗoki ta shiga gidan don ko ba komai so take ta riƙa ƙare masa kallo tana ayyana wai shi ma ɗan uwanta ne a matsayinsa na soja. Ita ba shi yake birgeta ba illa kakinsa na soja da sautari idan zai zo garin da su yake zuwa.

Kamar wacce aka wurga tana shiga gidan ta yi ciki da Nabila ai kuwa suka fara faɗa, juyawar da Dubu za ta yi a zafafe ta sheƙawa Aseem garin tsakin da ta karɓo daga injin niƙa. Sai ga Aseem da ke cikin unifom ɗin sojoji har da hankicin ɗin goge-goge ya fito furu-furu kamar wanda ya yi wanka da toka. Gashin kansa har wani tsinin farin garin masara ya yi.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 6
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Duk wannan abin da ya faru sam Dubu bata lura ba, masifa na cin ta bata san da ta sheƙa wa Aseem garin masara a jiki ba, sai ma uban tsalle da ta buga ta cukumi wuyan Nabila tana kai duka tana cewa: "Wallahi ba za ki daki banza, kwarankwasa dubu sai na koya miki hankali, hegiya tsigi-tsila da ƙafa kamar ta tsinken tsintsiya" Ganin ɗankwalin da ke kanta na niyyar kawo mata cikas ya sa ta fisge shi wurga shi ta baya sai kuwa ya sauka a kan fuskar Aseem, ban da tsami da bashi babu abin da yake tashi a cikinsa. Sai ga kitson kanta ya fito duk ya tuje hatta da tsagar kitson ta haɗe sai furu-furun amosani a saman kan.

Warin ɗankwalin ne ya doki fuskar Aseem har ya shaƙa da ƙofofin hancinsa  ya sa shi farkowa daga suman tsayen da ya yi na wucin gadi.  Aseem tun da ya zo duniya ba a taɓa yi masa abin da ya fusata shi lokaci ɗaya kamar abin da Dubu ta yi masa, dom shi abin daga haushi ma sai ya koma ba shi mamaki. Bakinciki da ganin yadda mutane suka zura masa ido ne ya ɓata masa rai har ya gagara sanin abin da zai aiwatar don ya wanke masa zuciya. Amma tabbas sai ya koya mata hankali don ya lura har lokacin Yaya babba ba ta ɗora ta a hanyar arziƙi ba.

Duk yanda Dubu  ta so nunawa Nabila ƙarshen iyawarta abin ya ci tura don a girme Nabila ta girme ta da kusan shekara huɗu. Gudun kar a kunyatata cikin jama'a ya sa Dubu ta tattara ƙarfinta ta fara wani fisge-fisge kamar mai aljanu tana kai duka ta ko'ina, ai kuwa ta ɗaga ƙafa bisa taautsayi ta harbawa Aseem da ke saƙa da warwara akan irin abin da ya dace ya yi mata. A hassale ya ƙarasa wurinta cikin zafin nama ya fisgi hannunta. Cikin tsiwa da rashin sanin wa ya riƙe ta Dubu ta ce, "Wallahi duk wanda ya riƙe ni sai na yi masa jini da majina dalla ku sake ni wallahi ba za ta daki banza ba."  Ai kuwa ya sauke mata mari a fuska, kafin wancen marin ya gama ratsa fuskarta ya sake kifa mata wani marin har sa da ta ga wasu irin taurari na gilma mata. A gigice Dubu ta buga tsalle cikin fitar hayyaci ta ce, "Innalillahi wayyo Baba Munkaila zai kashe ni wayyo! Inno fuskata."

Sauke hannun Aseem ya yi daidai da fitowar Yaya Babba za ta zagaya banɗaki. Da sauri ta saki butar hannunta ta fashe da kuka ta ƙarasa wurinsu, tana shirin riƙe hannun Dubu; Aseem ya sake fisgar Dubu ya nufi hanyar fita da ita. Duk irin kiran da Yaya Babba take yi masa ko waiwayenta bai yi ba bare ta saka ran zai tanka mata.

Duk yanda zuciyar Dubu take a bushe wannan karon sai da hanjin cikin ya kaɗa, tsoro ya mamaye ta musamman ta lura da irin ɓarin makauniyar da ta yi masa da garin masara. Suna zuwa soron ƙarshe ta yi ta maza ta fara ƙoƙarin fisge hannunta tana faɗin:

"Wai ina za ka kaini? Ka sakar mini hannu malam." Idanunsa sun kaɗa jawur saboda ɓacin rai don haka tambayar Dubu ba ƙaramin baƙanta masa rai ta ƙara yi ba. Bai tanka mata ba ya sake fusgarta da ƙarfin tsiya ya buɗe mota ya wurga ta sannan ya buɗe mazaunin direba ya zauna.

   Ganin ya tuƙa mota da ya fice da gudun tsiya ya ƙara hargitsa hanjin ciki Dubu, don wannan karon har ta fara bubbuga gilashin motar tana ihu. Can gefen titi ya gangar ya faka motar sai dai uffan bai ce ba. Sai da ya share minti biyar a haka yana jin kukan da Dubu take yi da ɗan ƙarfinta, ya zaro ƴar ƙaramar bindiga ya juya yana ce mata.

"Idan baki rufe mini baki ba zan harbe ki na wurgar da banza a wurin nan." Wata ajiyar zuciya da Dubu ta sauke idan ka ji za ka yi tsammanin numfashinta na ƙarshe ne zai fita. Bata san lokacin da ta haɗiye kukanta ba, ban da raba idanu babu abin da take yi, haɗe da jin wata irin da-na-sanin zuwanta duniya. Saboda ta san da ba'a haifo ta ba babu wata ƙaddara da za ta haɗo ta shi har ya nemi kashe ta da bindiga murus ya wurgar a gefen hanya. Don tun da take bata taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai dai ko idan tana daga moto ta hangota a hannun Sojoji ko ƴan sanda. Amma yau har ita ake yi wa iƙirarin harbewa da ita da rana tsaka. Tana son tambayarsa inda zai kaita amma tsoro ya hanata, tana cikin tunani ta ji ya sake fisgar motar da wani irin matsanancin gudu, ai kuwa ta ƙwalla uwar ƙara tare ta ƙanƙame jikin kujera.

A wannan yanayin suka ƙarasa gidan Mahaifinsa da ke unguwar Na'ibawa. Yana zuwa ya ciro mukulli ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fisgi hannun Dubu, ai kuwa tana ganin zai shiga gidan da ita ta riƙe ƙofar gate ɗin gidan da sauri tana cewa.

"Wallahi ni ba ƴar iska ba ce da za ka kawo ni gidan nan." Maganarta  ba ƙaramin dariya ta so bashi amma ya sake tamke fuska ya ce, "Ni ko ɗan iska ne an gaya miki zan yi iskanci da kucaka irinki?" Yana gama maganar ya sake fisgar hannunta aikuwa ta rungume wani ƙarfe tana cewa, "Kwarankwatsa dubu ba zan shiga ba, dama Inna ta ce ƴan iska ne suke bin maza." Tsugunnawa ya yi cikin ɓacin rai zai yi mata magana, ita kuwa Dubu tuni ta shagala da ƙarewa fuskarsa kallo don tun bayan fitowarsu ta lura da abin da yake jikinsa. Ai sai tsoro ya sake kamata saboda bata taɓa zaton haka garin masarar ya yi masara furfurar da bai shirya ba. Ta maza ya yi ya tsugunna a gabanta don wani tsami ne yake bugar hancinsa, saboda tun da aka yi rasuwa Dubu bata ƙara saka ruwa a jikinta ba. Dama wankanma sai Yaya babba ta yi da gaske take yi to rurumar jama'a ya sa ta basar ta ci gaba da harkokinta. Zaro bindigar aljihunsa ya yi ya ɗora mata akan goshinta nan take kuwa ƙirjin Dubu ya fara bugawa da ƙarfi, da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta shiga Dubu ta soma hawaye tana cewa, "Don Allah ka yi haƙuri idan saboda na zuba maka garin masara ne. Wallahi ban kana kusa ba."

Idan ka ji yanda Dubu take magana a ladabce za ka rantse da Allah mutuniyar kirki ce. Iya nadama Dubu ta shige ta don ta gama tsorata gabaɗaya, amma duk da haka bata jin za ta bi Aseem cikin gidan saboda ba za ta taɓa manta Baraka da ta yi ciki ba aka riƙa tsangwamarta ƙarshe sai sayar da gidansu Mahaifinta ya yi suka bar garin. Ita kuwa idan ta yi ciki ai ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda zai yarda a sayar da gidan Mai carbi.

"Idan kika bari na ƙirga uku ba ki tashi ba zan baki mamaki." Maganar Aseem ta farkar da ita daga dogon tunanin da ta tafi. Cikin hawaye Dubu ta ce, "Don Allah me za ka yi mini a ciki."

Banza ya yi mata yana buga bakin bindigar a ƙasa a hankali cikin sigar, idan baki tashi ba kin san sauran. Dubu bata yi ƙasa a gwiwa ba ta sake tambayarsa. Bai ɗago ya kalle ta ba ya ce, "Idan kin shiga kya gani."

"Wallahi ko me ka ce zan yi amma ni ba ƴar iska bace." Dubu ta faɗa lokacin da gumi da hawaye ya gama mamaye ilahirin fuskarta zuwa wuyanta.

"Ni ɗan iska ne." Ya bata amsa yana miƙewa a fusace ya fisgi hannun Dubu tana ihu tana fisge-fisge ya wuce da ita ciki. Yana shiga ya datse ƙofar ya wurgar da ita gefe sannan ya faɗa wani ɗaki da ke ɓarin hagu. Dukda gidan ba baƙon Dubu ba ne amma a wannan ranar gabaɗaya bata da nutsuwa. Bai jima da shiga ba ta ga ya fito da wani abu a hannunsa na dama, ɗayan hannun hagun kuma wata ƴar ƙaramar wuƙa ce, ai kuwa ta zabura kamar wacce aka ɗanawa wuta za ta gudu. Fuska a murtuke ya fisgi hannunta ya wuce da ita cikin banɗaki. A wannan karon Dubu duka ta fara kai masa tana cewa.

  "Jama'a ku taimaka min zai yanka ni. Kuma ka rabu da ni na ce maka ni ba ƴar iska bace. Wallah idan ka kashe ni na rataya a wuyanka duk zunuban su Inna Furai dana ɗauka kai za a ɗorawa." Suna shiga ya sa hannu ya bige bakinta har sai da ya fashe ai kuwa Dubu ta fashe da wani marayan kuka bai bi ta kanta ba ya sa kilifar aski ya ɗora mata akan gaban goshinta. A zabure ta matsa baya ta ce, "Aski za ka yi..." Idanun da ya zuba mata ne ya sa ta haɗiye maganar ba tare da ta ƙarasa faɗa ba. Ta ci gaba da hawayen baƙinciki da nadama.

"Idan kika sake yi mini magana sai na yanke harshenki da wuƙar nan." Dubu na ji na gani haka  Aseem ya sauke mata sumar kanta ban da hawaye babu abin da take yi. Kafin wani lokaci sai ga kan Dubu ya fito ral da shi babu gashi. yana gamawa ya nuna ta wuƙa hannunsa ya ce:

"Wannan da kika gani somin taɓi ne amma matuƙar kika sake shiga hannuna sai na yi miki zanen gobirawa da wuƙar nan a fuskarki." Ganin wuƙar na sheƙi ba ƙaramin razana Dubu ta yi ba, kuma a yanda ta ga babu ɗigon tausayi a fuskarsa ta san zai iya aikatawa don haka ta hau gyaɗa kai hawaye na zuba. Hannunta ya fisga zuwa falo ya sata tuƙin mashin. Dubu tun tana ganin kamar da wasa yake har ta tabbatar da yau sai ya kusa halakata a cikin gidan. Tana ganin ya ciro belt ta shiga taitayinta. Kuka take wiwi saboda yanda ƙafafuwanta suka ƙage, gashi ko nan da cen Aseem ya ƙi matsawa bare ta samu ta zauna ta huta. Tana zama kuma yake lafta mata belt ba shiri za ta sake miƙewa ta tashi tana soshe-soshe.

Sai da ya ga Dubu ta yi lugub sannan ya miƙe ya faɗa banɗaki ya yi wanka.

A wurin Dubu ta zube tana sauke numfashi da ƙyar, ta jera masa Allah ya isa ya fi a ƙirga. Kamshin da ya game hancinta ne ya ankarar da ita dawowar da Aseem ya yi. Ya yi kyau sosai cikin ƙananan kaya, haushinsa ne ya sake mamaye zuciyar Dubu don bata taɓa yadda da faɗar da ake yi akan sojoji mugaye ba ne sai a wannan lokacin. Kan kujera ya zauna sannan ya kirata, da sauri ta ƙarasa wurin ƙafarsa ta zauna. Danne-danne ya fara yi har sai da Dubu ta gaji da zaman sanna ya kalle ta ya ce, "Har yanzu kina nan da rashin kunyarki ko? Inno ta ɓata ki kina shuka tsiyar da kika ga dama. Wallahi daga yau na sake ji ko ganin kin aikata wani abin na rashin ɗa'a gaba hannu da ƙafafuwanki zan yanyanke miki, wannan bakin naki sai na datse shi na ga ta ƙaryar iskanci." Kamar ƙosashen ƙadangare haka Dubu ta riƙa gyaɗa kai tana hawaye. Yana gama maganar ya fisgi hannunta suka fice daga cikin gidan.

Yaya babba na ganin irin marin da Aseem ya yi wa Duba ta zuba salati haɗe da dafa ƙirji, don har jin saukar marin sai da ta ji wani iri a jikinta. Tana ganin fitarsa ai kuwa ta zauna daɓar a wurin ta fashe da wani irin kuka. Hajiya Nafisa ci kanki ba ta ce mata ba, sai ma jin zuciyarta da ta yi ta mata fes saboda ta san tun da ta tabo Aseem ba za ta ji da daɗi ba. Saboda ko su Nabila baya musu ta daɗi bare Dubu da kowa ya shaida fitinarta. Yaya Babba wayarta ta zaro ta miƙawa Hadiza tana faɗin.

"Maza kira mini Garba idan shi ya ɗaure wa wannan fitsararren yaron yake shuka rashin matumci, har ina kiransa yana ji na sai ya mini bayani. Wallahi ba Soja ba yau ko Barek ɗin ce da kansa sai an yi mini iyaka da shi." Hadiza jiki a sanyaye kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ta karɓi wayar ta fara lalubo lambar, amma a ƙasan zuciyarta tana ayyanawa irin rikicikin da za a kwasa a cikin gidan.

Baba Abubakar suna hanyar dawowa gida daga asibitin da Inna Furai take kwance har an bata sallama, da yake dama likitocin sun ce damuwa da fargaba ne ya jefa ta a halin da take ciki. Bai yi aune ba ya ji kiran waya. Hadiza na jin an ɗauki wayar ta miƙawa Yaya babba, shi kansa Baba Abubakar tun da ya ga kiran mahaifiyarsu ya ayyana dole akwai abin da yake faruwa. Ɗaukan wayar ya yi da sallama jiki babu ƙwari, Yaya babba ko amsa sallamar sa ba tayi ba ta ce, "Garba! Garba!! Garba!!!" Gabansa na faɗuwa ya amsa sannan Yaya Babba ta ci gaba da cewa, "Sau nawa na kira ka?" Ya amsa  mata.

"Sau uku Inno"

"Wallahi tun ban kwashe wa ɗanka falsafar albarka ba ka zo gidan nan yanzu-yanzu" Kansa ɗaurewa ya yi don shi ya manta ma da sun yi magana da Aseem akan zai zo gaisuwa saboda haka ya cewa Yaya babba.

"Inno wa kenan?"

Yaya Babba ta fashe da kuka tana cewa, "Karka zo ka bari idan ya kashe mini jika shi kenan."tana gama maganar ta katse kiran. Da sauri Baba Abubakar ya danna wayar Aseem sai dai ya ji ta akashe don lokacin tuni ya kashe ta saboda ya san dama tabbas za a neme shi.

Wayar Hajiya Nafisa ya kira tana ɗauka ya shiga jero mata tambayoyi, tana jin haka ta saci kallon Yaya babba da ta cika fam sannan ta bashi amsa da, "Ka san dai yarinyar nan Dubu ba kunya gare ta ba, daga zuwan Aseem ta sheƙa masa garin masara. Dama kuma ta cikumi Nabila tun da ta rainata kamar takalmin ƙafarta. Sauran maganar dai sai ka zo." Yana tafe a mota amma gani yake kamar tafiyar bata sauri don ya san lamari ya gama kwaɓewa gabaɗaya amma gyarawa sai Allah.

Yana zuwa ya samu Yaya babba a zaune ban da hawaye babu abin da take yi, a gefenta ya tsugunna ya ce, "Ga ni Inno."

"Garba ka raba ni da wancen mai busasshiyar zuciyar. Wallahi ni an cuce ni da aka tura mini jika aikin soja, dama tun tuni na ce bana son wannan aikin saboda cire musu imani ake yi amma aka ƙi yanzu ga irinta nan. Yaro ya koma kamar basamude haka ya riƙa kifawa yarinyar mari babu tausayi barr imani. Wallahi idan ya kashe mini jika ba zan yarda ba shari'a sai ta kaimu har kotun ƙoli." Sai ta kuma rushe wa da kuka tana ci gaba da cewa, "Saboda Allah me Dubu ta tsare masa da zai riƙa zabga mata mari kamar Allah ya aiko shi. Kana ganin wannan shirgegiyar matar ta min tsaye a ka, ko ta tsawatar masa wa ya sani ba ko ita ta saka shi don na lura ba ƙaunar Dubulliyata take ba. Kaico yanzu yarinyar ko a wane hali take oho." Yaya Babba ta sake rushewa da kukan da ya fi na farko taɓa zuciya.Nan take aka yi wa Baba Abubakar bayanin abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Da ƙyar ya samu ya lallaɓi Yaya babba ta rage faɗan sai dai bakinta ya kasa yin shiru.

Bayan wani lokaci suna nan zaune Aseem da Dubu suka shiga cikin gidan, fuskar Dubu duk ta yi zurur-zuru tana tafe tana gwale ƙafafuwa. Gabaɗaya mutanen wurin binta suka yi da kallo, Baba Abubakar rai a matuƙar ɓace ya tari Aseem da kyakkywan mari. Dubu kuwa na ganin haka ta sake ɗangalewa ta rushe da kuka ta faɗa kan Yaya Babba.

Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, "Dubu me nake gani kamar aski akanki." Dubu ta rushe da kuka ta ce, "Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne." Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, "Dubu je ki can mu gani." Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha.

Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, "Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera." Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, "Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba."

Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.

Baba Abubkar ya kalli Aseem da kallon tuhuma rai a ɓace, Aseem ya sunkuyar da kai ƙasa saboda ba ƙaramin takaici kakar tashi ta bashi ba. Da wata irin murya Baba Abubakar ya ce, "Abin da Inno ta faɗa haka ne?" 

Aseem ya furzar da iska mai huci ya ce, "Daddy don Allah ka bar biyewa maganar tsohuwar nan ka san dai wasu maganganun nata ba su..." Bai ƙarasa ba Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, "Ka iya bakinka Aseem duk yanda Mahaifiyarmu take furta lafazi Mahaifiyarmu ce."

Yaya Babba ta wara hannuwa ta ce, "Kuma na fi wannan gajeriyar uwar tashi mai kama da gajeren turmi, na gama maka komai tun da na haifo uban da ya haifeka. Atoh gara ka yi bayani wallahi babu inda zani in wahalar da kaina wurin neman maganin gargajiya. Alƙur'an dama sai da Idi wanzan ya gaya mini ɓat haka za a nemi komai a rasa. Wa ya sani ma ko aljanunsa ne za su ɗauke su cinye su barka a shafe.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 7
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

    Waɗannan kalamai na Yaya Babba ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Hajiya Nafisa suka yi ba, ciki a kaɗe hankali a tashe ta dubi Yaya babba da babu abin da take yi ban da huci ta ce, "Inno ba mu fahimce ki ba. Shi Aseem ɗin za a mayar kamar bayan silba?"

"Ke Nafisa ki fita daga idona, dama ban faɗa don ku fahimce ni ba ehe. Hadiza meye laifina don na nemawa marainiyar jikata maganin tsari?" Hadiza ta girgiza tana faɗin, "Babu laifi Inno!" Yaya babba ta ci gaba da cewa:

"Allah ya jiƙan Idi ɗan wanzam ya gafarta masa shi ya bani laƙani na yi wa yarinyar nan Dubu, akan duk wanda ya farketa to shi da sake zama namiji har abada kenan." Hajiya Nafisa ji ta yi ƙafafuwanta sun yi sanyi har tsayuwar na neman gagararta. Don haka ta jingina ta bango tana bin Aseem da wani irin marayan kallo.

Kafin wani lokaci gabaɗaya iyalan gidan sun hallara a ɗakin Yaya babba dama kuma gidan babu kowa sai iya su ƴan gidan, don haka suka hallara kowa zuciyarsa babu daɗi. Yaya babba ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara cewa, "Na san dai kun san dalilin tattara ku da na yi a wurin nan. A zahirin gaskiya Soja ya keta mini rigar mutumci, saboda Allah wane mugun abin yarinyar nan ta yi wa yaron nan da zai aikata mata wannan mugun halin..." Kuka ya ci ƙarfin Yaya babba saboda zuciyarta ɗaya ta ɗauka Aseem wani abu ya yi wa Dubu da ta tafiyarta ta sauya.

Baba Adamu ya yi sallama sannan ya fara fa cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri. Amma kafin a yanke wani hukunci ya kamata a ji ta bakin yaron nan bana jin Aseem zai aikata abin da ake magana akai..." Yaya Babba ta yi farat ta katse Baba Adamu da cewar, "Ado ƙarya na yi kenan? Ku tashi ku fice daga gabana idan ba so kuke na yaye falsafar albarkar da ke kanku ba." Baba Adamu ya yi ƙasa da murya ya ce, "Inno don Allah ki yi haƙuri ba haka nake nufi amma duk yanda kika ce haka za a yi."

"Ke Dubu me soja ya yi miki bayan ya tafi da ke." Dubu da har lokacin da sauran tsoron Aseem a zuciyarta ta saci kallonsa aikuwa suna haɗa ido ya watsa mata mugun kallon. Sai a kan idon Yaya babba ta ga irin kallon da Aseem ya yi wa Dubu, ai kuwa wani irin gumi ne ya fara yayyafowa Dubu ta fara inda-inda. Yaya babba ta fara salati tana tafa hannuwa ta kalli Aseem ta ce, "Ittaƙillah Soja ka ji tsoron rabbissamawati, idan ka zare mata ido a nan duniya a cikin kabari za ka zare wa Mala'iku ido ne. An ya Soja haka ka koma ban sani ba?" Ta mayar da kallonta wurin Dubu ta ce, "Za ki yi wa mutane bayani ko sai na sa Munkaila ya zane miki jiki ciki da bai." Dubu ta muskuta gefe ta fara cewa, "Da ya kaini mota bindiga ya ciro wai zai harbe ni ya wurgar da gawata a gefen hanya." Da sauri Yaya Babba ta dafe ƙirji ta ce, "Kun ji ko? Na gaya muku tuni ya riga da gama da ita." Hajiya Nafisa saboda ɓacin rai ji ta yi kamar ta shaƙo Dubu da Yaya Babba ta shaƙe su. Dubu ta ci gaba da cewa, "Muna zuwa gidan ya yi mini aski kuma wai da har billen gobirawa zai yi mini. Daga nan ya sani tuƙin babur shi ne muka taho gida." Yaya babba jikinta ne ya fara sanyi ta ce, "Daga haka bai yi miki komai ba?" Dubu ta ce, "Eh"

A ɗan ƙufule Yaya babba ta ce, "To da kika ce ɗan iska ne?"

Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Eh mana ba ke kika ce mini duk mace mai bin namiji, ita da shi duka ƴan iska bane?" Wata gwauruwar ajiyar zuciya Hajiya Nafisa ta sauke, Yaya babba cikin jin haushi ta ce, "Amma Allah wadaran halinki Dubu da za ki iskanta mini jika, ina ji ina gani a gaban iyayensa. Kedai an yi makira yanzu ba sai ki sa Garba ya ce ba na son Ɗansa ba. Ni dai kin cuceni za ki haddasa gaba a tsakanina da ƴaƴana. Tashi ki bani wuri makira in Allah ya yarda ba zan ga ɗan iska a kan jikana ba. Don Allah ku gaya mini abin da Soja ya tsare wa Dubu da za ta yi masa mugun fata haka?" Kowa ya yi shiru a ɗakin bai tanka mata ba. Yaya babba ta dubi Aseem da fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin ra ta ce, "Soja ka gafarce ni wallahi wannan makirar ce ta ingiza ni, ni dama sai da zuciyata ta raya mini babu abin da za ka yi wa Dubu." Ci kanki Aseem bai ce mata ba, sai kuma ta fara matsar ƙwalla ta ce,

"Garba kana gani Soja ya ƙullace ni har ya ɗau fushi da ni. A gidan duniya idan ban yi wa jikana magana ba wa zan yi wa? Kana gani hakkin Soja zai bar ni kwanciyar kabari?" Baba Abubakar ya ce, "Inno bai ƙullace ki ba ina jin bai jiki ba ne." Ya faɗi haka ne don kar wutar rikicin Yaya babba ta ƙara tashi. Yaya babba ta saki murmushi tana goge hawaye ta ce, "Soja!" Ya ɗago ya dube ta har lokacin fuska babu walwala ya ce, "Na'am" ta ci gaba da cewa, " Allah dai ya yi maka albarka. Wallahi ka biyani da ka askewa yarinyar nan kai." Da sauri duk suka ɗago suna kallonta don ba su taɓa zaton haka daga bakinta ba.

Ta janyo Dubu tana sulle hijabin da ta ɗaura ta rufe kan da shi ta ce, "Wari dai akanta yanda ka san an buɗe shadda, idan Dubu ta buɗe kai a kusa da kai alƙur'an ko yawu ba za ka iya haɗiya ba. Kwanaki haka na saka mata fiya-fiya saboda kwarkwata amma yarinyar nan duk ta watsar a banza. Don Allah ka gaya mini wane saurayi ne zai ɗauki Dubu tana fama da tsamin kai dana hammata?" Hajiya Rahama ta yi murmushi ta ce, "Inno ai har yanzu Dubu yarinya ce tana ƙara zama budurwa duk za a nemi wannan ƙazantar a rasa." Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Ke Rahama rabani da cewa Dubu yarinya. Yarinyar da tun bara ta fara jini, ki gaya mini ta zama budurwa ko bata zama ba? Ga Ma'awiyya ƙawarta nan tun kwanaki aka yi mata aure wai sai ga ciki, nace kai waɗannan ƴaƴa an yi jarababbu yanda kika san a bakin ƙofa suke cin karo da shi. Yarinyar nan haka ta riƙa kuka da zan kaita ɗakin miji da yake ƙud-da-ƙud muke da kakarta, ina ta zuba ido na ji an ce yarinya tana gudun miji tana dawowa gida, kamar yanda muka riƙa yi muna amare ba sai muka ji shiru ba. Hali ne dai a ƙoƙon rai Dubu ba za ta daina wannan halin ba, ban ƙi ba idan ta haɗu da miji ɗan gayu kamar Soja." Ai kuwa Aseem na jin haka ya ɓata fuska bai gama tsinkewa da lamarin Yaya Babba ba sai ji ya yi ta ce, "Ai shi ma wannan shirun da yake yi ba banza ba wallahi, aure yake so don dai bai gaya muku bane. Ya yi gadon Kakansa Malam, don haka ya bani labari shi ma yana matashi Allah ya jiƙan Malam babba shi ya fahimci aure yake so, ba a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure. Shi ma Soja ana haɗa shi da ƴar budurwa kamar Dubu shiru za ku ji sai dai ku ji ciki." Aseem a daƙile ya miƙe zai fita saboda takaici. Yaya babba ta bushe da dariya ta ce, "Kun ga abin da na gaya muku wai ya ji kunya na tona asirin zuciyarsa." Baba Adamu ya yi murmushi ya ce, "Yanzu Inno magana ta wuce kenan kowa zai iya tafiya?"

Take ta murtuke fuska ta ce, "Sam ban sallame ku ba wallahi akwai muhimmiyar maganar da nake son yi da ku ko Dubu?" Ta faɗa tana kallon Dubu da ke cika tana batsewa.

Dubu ta gyaɗa kai don fushi take da Yaya babba saboda irin bankaɗar da Yaya babba ta yi mata a gaban mutane, Yaya babba ta gyara zama sannan ta fara cewa.

"Garba wata shawara na yanke don Allah ya sani an daɗe ana shiga haƙƙina." Gabaɗaya suka kalleta suna mamakin jin kalamanta sai dai ba wanda ya tanka suna jiran jin ci gaban sauran maganar.

"Tun Malam yana raye nake son ganin kan iyalaina a haɗe ba wannan ya yi gabas, waccen kudu wani arewa ba."

Hadiza ta jinjina kai sannan ta ce, "Maganarki hake ne Inno amma ai kanmu a haɗe yake don gabaɗayanmu babu mai bijirewa maganar na gaba da shi." Yaya Babba ta washe baki ta ce, "Ai shi ya sa nake son na ƙara haɗa kanku idan na waiga na ga wannan inna juya na ga wannan ko ba haka ba Dubu?" Dubu ta yi murmushi don ta san muddin Yaya babba ta zartar da hukunci to ba fa ba shakka suma sun zama ƴan gayu irin yanda ƴaƴan Baba Adamu da Baba Abubakar suke rayuwa.

"To na zauna mun yi shawara ni da Dubu kuma ta bani shawara mai kyau akan haka." Wannan kalamai na Yaya babba ya yi daidai da shigowar Aseem zai ɗauki mukullin motarsa. Yaya babba ta yi farat ta dakatar da shi da cewar, "Kai Soja tsaya ayi da kai ka ji alherin da zai same ku don wallahi ba ƙaramin gata zan yi muku ba. To ina dalili in kwanta inmutu zuri'a a tarwatse, a'a sam haka ba za ta faru ba dama abin da na riƙa nusar da kakanka kenan ya ƙi gane wa." Aseem bai so zama ba don ya san ban da rikici babu abin da za ta yi musu a wurin. Amma gudun tashin hargitsinta ya sa ya koma ya zauna ba tare da ya tofa uffan ba.

"Yauwa magana muka yi ni da Dubu kuma wannan shawara da ta bani na yi na'am da ita. Na yanke hukunci kai Garba da ɗan uwanka Ado za ku dawo gidan nan da zaman. Kowa ya kwaso iyalansa ya kawo su ɓangarensa. Yo ina dalili ace da mahallinku a gidan gado kowa da ɓangarensa sai dai ace wai idan an kawo mana ziyara a sauka a ciki. A'a sam ba da ni za a yi haka ba Dubu ta ce sai mum fi cin daɗi kuma waye baya san daɗi a  rayuwarsa Garba." Ta ƙarasa maganar tana tambayar Baba Abubakar da ya yi suman zaune. Kasancewar ya tafi wani tunani can bai ma san irin tambayar da Mahaifiyar ta shi take yi masa ba.

Hajiya Nafisa da ta cika fam har wani ɗaci take ji a zuciyarta ta ce, "Inno yanzu shawarar Dubu za a ɗauka? Dubu har wata mutum ce da za a saurari shawara daga bakinta. Maganar gaskiya wannan ci baya ne ace shekara sama da ashirin da bakwai muna zaune a cikin birni rana tsaka a ce mu dawo ƙau..." A hanzarce Baba Abubakar ya ce: "Nafisa! Bana son jin bakinki!"

"A'a ka barta Garba idan bata tsefe ni ba ai ba za ta nuna mini ta isa ba. Don Allah ka gaya mini lokacin da ka auro Nafisa a ina ka aurota da ya wuce ƙauye. Ka tuna lokacin da kuka je ƙauyensu ɗaurin aure Labaran ƙanina cewa ya yi ruwan garinsu kamar turɓaya haka yake. Nan dai gidan gado ne ko ana so ko ba'a so dole mutum ya dawo." Rai a matuƙar ɓace Aseem ya ɗago yana kallon Yaya babba, da Dubu da ke gefe. Furzar da iska ya yi ya sunkuyar da kai yana danne-danne da waya, sai dai ba zai ce ga takamaimai abin da yake latsawa ba. Baba Adamu ya russuna ya ce, "Inno a duba lamarin dai saboda yanayin aikinmu ga makarantar yara. Idan sha'awar zama kike kusa da mu ni ko Yaya Abubakar wani sai ya ɗauke ki, koma can da zama."

"Haram giya a gidan liman! Ba da ni ba. Ba zan taɓa bijirewa umarnin Mahaifinku ba, na gama magana idan za ku dawo nan kowa ya gyara wurinsa ya dawo, idan ba za ku dawo ba shi kenan" Tana gama maganar ta rushe da matsanancin kuka.

Zuciyar Baba Munkaila fes don ya san ko ba komai ya san idan suka dawo cikin gidan za su iya ɗauke masa cefanen gidansa. Baba Abubakar yanayinsa sam babu walwala ya dubi Mahaifiyarsa ya ce:

"Inno wannan kawai kike buƙata?" Da sauri Hajiya Nafisa ta hangame baki. Hajiya Fauziya ma ta cika fam tana watsawa Yaya babba harara ƙasa-ƙasa.

Yaya babba ta share hawaye ta ce, "Garba idan kuka yi mini wannan duniya da lahira kun biya ni haƙƙin mahaifiya. Ni dai Allah ne gatana kuma da shi na dogara, ko na dogara da ɗaya daga cikinku?" Baba Munkaila ya ce, "Inno mu kuma fa?"

"Munkaila a gidan duniya ka gaya mini wane abu ka taɓa yi mini." Baba Munkaila zai yi magana, Baba Abubakar ya katse shi da cewar, "Shi kenan zamu dawo Inno amma ki ɗan bamu lokaci tun da kin ga tashin namu babu shiri dole akwai abubuwan da za mu gudanar."

"Allah dai ya yi muku albarka Garba, ku yi komai a nutse wallahi. Me ake da gaggawa aikin  shaiɗan. Me ye haɗinmu da shaiɗan muna masoya Mazon Allah (S.A.W). Allah ya yi mana tsari da shaiɗan, ku bi komai a sannu ko nan da sati biyu ne." Cikin haɗin baki suka ce, "Sati biyu Inno?"

"Ko ya yi yawa?"

Baba Adamu ya ce, "Inno Sati biyu ai ya yi kaɗan ina laifin nan da wata guda kinsan ko a gun aiki sai mun ɗauki uzuri." Ya gaya mata haka ne don ya san yanda take bawa aikinsu muhimmanci. Sai da ta yi jim sannan ta ce.

"Eh ka fi ni gaskiya Ado maza ku je ku yi komai a nutse kar wurin aikin su ji haushi su sallame ku ko?" Hajiya Nafisa kamar za ta yi kuka ta ce, "Yanzu Alhaji shi kenan ka amince nan ɗin za mu dawo?" Aseem ya sa hannunsa ya damƙi hannun mahaifiyarsa don ba ya son ace ita ta fara ɓullo  da wata maganar. Fisgewa ta yi ta ci gaba da cewa, "Maganar gaskiya ba a yi mana adalci ba, sai da aka ga ƴaƴanmu sun zama ƴanmata za a ce mu dawo ƙauye wallahi da  sake..." Cikin tsawa Baba Abubakar ya ce:

"Nafisa ya isa haka! Tashi ku fice an sallame ku." Rai a ɓace gabaɗaya matan nasu suka fice daga ɗakin. Baba Abubakar ya russuna ya ce, "Na barki lafiya Inno." Yana fita Baba Adamu da tsirarun ƴan uwansu suka bi bayansa. Ɗakin ya rage daga Baba Munkaila, Aseem, Dubu, Yaya babba sai Hadiza.

Jiki a sanyaye Yaya babba ta kalli Baba Munkaila ta ce, "Munkaila an ya yaran nan ba haushina suka ji ba kuwa? Na ga kamar a fusace suka fita. Don Allah meye laifina don na nemi haɗa kan zuri'ata?" Baba Munkaila ya washe baki ya ce, "Babu Inno kawai dai haka kika gani amma babu abin da suka ji, ya za a yi su ji haushinki." Yaya babba ta yi murmushi cikin jin daɗi.

Hadiza da ke gefe ta ce, "Gaskiya Inna bai kamata ace kowacce shawara Dubu ta gaya miki ki ɗauka ki yi amfani da ita ba. Mu fa mune ƴaƴanki mu ya kamata ki kira mu ji shirinki amma nawa Dubu take da za ta baki shawara." Yaya babba ta yi shiru kamar mai nazari sannan ta ce, "Kuma maganarki fa haka take don kin manta shawarar da Dubu ta bani akan sayar da ƙaton ragona ta ce na siyo ƴan tsaki, me ake yi da kiwon kaji idan ba asara ba? A rana ɗaya sai a fitar mini da mushen biyar suka lalace a banza bai fi ƙwara goma muka mora ba cikin Sittin. Kai amma Dubu an yi shakiyyiyar yarinyar, da ta ga kaza ta fara rufa sai dai na ji ta wasa wuƙa ta yanka, ni an ya ba da biyu ma Dubu ta riƙa yanka kajin nan ana soyawa ba?" Hadiza ta taɓe baki ta ce, "Ai koma meye Inno kun fi kusa. Amma kiwon kaji ana samu da shi wacce kika ɗora akai ce dai sai a hankali. Yanzu mu koma maganar su Yaya Adamu maganar gaskiya Inno ba za su ji daɗin zaman gidan nan ba, tun da sun saba da zaman cikin gari kina gani tun a gabanki me Nafisa take faɗa. Kina ganin zamansu a kusa da ke babu wata matsala?" Yaya Babba ta saci kallon Aseem sannan ta ce, "Ni fa Nafisa ta birgeni, sabo fa aka ce miki Hadiza. Sabo turken wawa, kuma ko ke ce haka za ki faɗa. Gaskiya ki daina cin naman mutane a ɗakina karki haramta mini mala'ikun rahama shigowa ɗakina ina zaune ƙalau. Yanzu ga Soja a zaune idan ya ji kina aibata mahaifiyarsa ba sai ya ɗauki gaba da ke."

Aseem bai tanka musu ba Hadiza ta ce, "Inno gaskiya fa na faɗa ko a gaban Nafisa zan faɗa ba wai Aseem ba. Ina guje miki abin da za a zo ana yin babu daɗi Amma tun da haka kike so shi kenan Allah ya dawo da su lafiya." Hadiza na gamaƙ maganar ta tashi ta fice, Baba Munkaila ya rufa mata baya.

Aka bar Yaya babba da riƙe haɓa, Aseem na shirin ta shi ta ce masa, "Soja  don Allah ka bar ni na kwashewa yaran nan albarka, kana ganin abin da duk suka yi mini wai haɗe mini kai za su yi su ware ni daga cikinsu. Cikin halin ko'inkula Aseem ya ɗaga kafaɗa ya ce: "Ki kwashe musu mana, idan kin ga dama ki tsine musu ƴaƴana ko naki. Wallahi akwai abubawan da dama da idan muka dawo zan saita muku zama ke da sheɗaniyar jikar taki mutum ya kawo mini wargi na sa bakin bindiga na harbe shi." Yana gama maganar ya fice a fusace. Da sauri Yaya babba ta dafe ƙirji a firgice da jin maganar da Aseem ya faɗa.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 8
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

     Aseem haka ya tafi ya bar Yaya babba hangame da baki, ta yi ƙasa da murya ta ce, "Dubu kin ji abin da Soja ya ce mini kuwa?" Dubu ta bushe da dariyar ƙeta don duk wanda ya ga yanda Yaya babba ta tsure sai ya fahimcin irin fargabar da ta shiga. Dubu ta ja hijabinta ta rufe kanta ta ce, "Ai wallahi Inno tsaf zai harbe ki don ba imani gare shi ba. Ni fa wallahi ina jin ma da ƙyar idan kafiran nan ba su fara koya masa kafirci ba." Da sauri Yaya Babba ta dafa cinyar Dubu ta ce, "Ke Dubu raba ni da jin wannan maganar, Mai sunan Malam ne zai amshi addinin kafirai?" Dubu ta ɗauke kai gefe ta ce, "Yoo musulmin ƙwarai za a haɗa shi da Allah da manzonsa ya ƙi ji ne?"

"A'a! Amma ki ji tsoron Allah Dubu kar ki sa na tuhumi Garba ya sake ɗaukan gaba da ni." Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Ai dama ke ba a magana da ke sai kin kwashe kin gaya musu, haka kika gama ci mini mutumci a gabansu kina kirana da ƙazama." Yaya babba ta janyo Dubu cinyarta ta ce, "Ina sane na gaya musu haka idan ba haka ba wallahi Soja gaba zai ɗauka da ni amma ki bar ni da su idan suka dawo gidan nan duk za mu saita musu zama." Dubu na jin haka ta bushe da dariya don har ta gama tamawa yanda za ta yi wasan kura da Nabila don da alama ta lura ita ce hoton Hajiya Nafisa da duk wasu halayenta.

Inna Furai tun da suka dawo daga asibiti take ta bacci ba ita ta farka ba sai bayan magriba, tana farkawa ta hangi Larai a gefenta. Da murnarta ta tarbe ta da sannu sai dai ta lura da yanda Mahaifiyar tata take ƙarewa ɗakin kallo, matsawa kusa da ita ta yi ta ce, "Sannu Inna ya jikin?" Inna Furai ta yunƙura za ta tashi, Larai ta taimaika mata tashi sannan ta ce, "Larai ina su Lantan suke?" Larai ta yi murmushi ta ce, "Inna su Lantan ai sun wuce tun safe yanzu dai bari ki yi alwala ki yi sallah sai ki ciki abinci, ko sai kin fara cin abincin?" Inna Furai ta girgiza kai tana faɗin, "Wane mutum sallah ai ita ce gaba da komai, bare yanzu da Fatale suke kawo mana farmaki. Amma ya maganar tawagar fatwar da ƴan sama jannati?" Larai ta ce, "Inna don Allah ki bar maganar nan wannan fa duk ya wuce komai ya daidaita yanzu bari na kawo miki ruwa ki yi alwala." Tun daga lokacin Inna furai ta ɗan saki jikinta ta fara harkokinta.

Kafin wani lokaci tuni maganar dawowar su Baba Abubakar ta karaɗe cikin gidan, wasu daga cikin facalolin ban da murna babu abin da suke yi don dama ba ƙaramin haushi suke ji ba, a duk lokacin da suka ga su Hajiya Rahama sun zo garin fes kowacce ta ƴaƴanta cikin gayu. Wasu daga ciki kuma suna jin haushi don gani suke matuƙar matansu Baba Abubakar suka dawo gidan sun koma bola a wurin Yaya babba, don a haka ma ya suka iya da tsiyar da Dubu take shuka musu amma basu da abin faɗa? Wasu kuma murna ɗaya suke ta dawowar tasu don suma su dangwali abin arziƙi saboda ko banza za su ci gaba da cin mai kyau saɓanin da, da sai dai su ga an direwa Yaya babba kayan alatu na more rayuwa sai dai idan ƴaƴansu sun je ta zaunar da su ta ba su, su ci su yi ƙat su suna daga gefe suna lasar baki.

Kamar haɗin baka duka matan Baba Abubakar da Baba Adamu suka haɗa kai kowacce ta kwashi ƴaƴanta suka yi tafiyarsu. Shi kansa Aseem yana fita ya shiga motarsa ya yi gaba, Hajiya Nafisa ta tasa ƴaƴanta suka wuce bakin titi suka tari abin hawa suka tafi don saboda ɓacin rai ko ta kan Maigidanta bata bi ba. Hajiya Rahama da Hajiya Fauziyya ma tafiya suka yi, a hanya babu mai tankawa kowa saboda takaici har suka ƙarasa gida.

Suna zuwa gida kowacce ta yi sashenta da iyalanta saboda ko da cen ma dama ba wani cikakken zaman lafiya suke yi ba. A ranar ma abin da ya sa wani abu bai haɗo su ba saboda ba daɗi ya sa su tafiyar ba kowacce zuciyarta cunkushe take da baƙin ciki.

Gidan Baba Abubakar.

Hajiya Nafisa na zuwa gida ta ɗau waya ta kira ƙawarta Hajiya Ikilima, bata jima da shiga ba aka ɗauka da sallam. Ko ƙwaƙƙwarar gaisuwa ba su yi ba Hajiya Nafisa ta fara da cewa, "Ƙawata don Allah kina ina? Ina son ganinki cikin gaggawa!" Daga can ɓangaren ta bata amsa, "Lafiya kuwa Ƙawas ko tsohuwar ita ma ta sheƙa ne?"

Hajiya Nafisa ta yi murmushin takaici ta ce, "Wallahi da za ta sheƙa da na fi kowa murna a rayuwar duniyar nan. Kai ni tun da nake na taɓa ganin ƙaddararriyar tsohuwa kamarta kuwa, yanzu kina ina kizo na dawo gida don Allah maganar gaggawa ce ina son ganinki." Hajiya Ikilima ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Gani nan zuwa yanzu kuwa amma ince dai mijinki baya nan ko? Don kinsan gani yake kamar ni nake zuga ki shi ya sa ma bana son zuwa idan yana nan." A ƙagauce Hajiya Nafisa ta ce, "Ba fa ya nan ya can ƙauyensu ni dai sai kin ƙaraso." Daga haka suka yi sallama, Hajiya Nafisa ta fara sintiri a cikin ɗaki.

Tana nan tsaye ta ji sallamar Aseem, tun bai tufe baki ba ta fita falon idanu a ƙanƙance ta fara magana: "Aseem yanzu saboda Allah wannan tsohuwar ta yi mana adalci kenan? Saboda Allah a ce duk abin da waccen ƴar iskar yarinyar, mai zubin sheɗanun ta gaya mata da shi za ta yi amfani. Wacce rayuwar za mu tsinta a zaman ƙauye? Tun da ba ta ce mu koma ba sai da ta ga yaranmu sun zama ƴanmata wato yanda waccen za ta zauna a ƙauye tana baƙincikin su Nabila su sami miji a birni. Da sake wallahi, Allah sai dai Mahaifinka ya zama ko zaman ƙauyen ko kuma mu raba gari."

Dama ya san za a rina don haka ya shiga sashen mahaifiyar tashi don ya samu ya taushe ta. Amma maganarta ta ƙarshe ta fi firgita hanjin cikinsa, saboda tun da yake bai taɓa jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Mahaifiyarsa ba. Shi kansa sheda ne duk irin ɗabi'un Mahaifiyarsa na rashin haƙuri amma mace ce mai kyawawan ɗabi'u. Matsalarta ɗaya rashin haƙuri da kawar da kai sai kuma son kanta da saurin ɗaukar zuga, amma bayan wanna baya jin tana da wasu halaye marasa kyau.

Cikin sigar lallashi ya kalli mahaifiyarsa ya ce, "Don Allah mommy zauna mu yi magana." Bata musa ba ta zauna a kan kujera tana kallonsa. Aseem ya ci gaba da cewa, "Mommy don Allah ki kwantar da hankalinki wannan fa ba abin tashin hankali bane. Kamata ya yi a ajiye maganar nan agefe har zuwan bayan sadakar bakwai, amma Mommy kun taho gida ke da su Nabila da Aunty kina ganin Daddy zai ji daɗi?"

"Dama ban aikata haka don jin daɗinsa ba, Aseem idan kana da wata maganar bayan wannan ka yi amma magana ɗaya za a gaya mini na saurara cewar mun fasa komawa ƙauye. Ina nan wallahi mahaifinku zai dawo ya same ni." Tashin hankali wanda ba a sa masa rana. Miƙewa Aseem ya yi ya ce, "Allah ya huci zuciyarki Mommy amma hakan sam bai dace ba yanzu idan Iya ce (Mahaifiyar Hajiya Nafisa) ta ɓata miki rai na san ba za ki yi haka ba, kin ga Daddy shi ma gani zai yi don ba mahaifiyarki ba..."

"Fita ka bani wuri" Hajiya Nafisa ta faɗa tana nunawa Aseem ƙofa azafafe. Sum sum sum ya miƙe zai fita ta ci gaba da faɗa, "Ai wallahi dama na sani wannan zaman daɓaron da tsohuwar nan take zuwa duk lokacin dana haihu ba banza ba, ta gama asirce mini ƴaƴa fa magane-maganen da take basu tun jarirantaka. Ban da lalacewa kai ba me shigar mana ba ne sai inda ƙarfinka ya ƙare, a'a kai gudun ɓacin ran mahaifinka kake yi." Aseem ya fice daga falon ya bar Mhaifiyarsa tana da sababi.

Gidan Baba Adamu.

Hajiya Rahama ita kaɗai ta ƙule a ɗaki tana nazari, lokaci ɗaya ta ji kamar ba su kyauta da abin da suka yi ba domin suma idan mahaifansu ne dole su yi musu biyayya. Tashi ta yi jiki a sanyaye ta nufi sashen Kishiyarta Hajiya Fauziya, a falo ta same ta tana waya, tana ganin Hajiya Rahama ta ce, "Ok, ba damuwa za mu yi waya an jima." Hajiya Rahama ta kalli Hajiya Fauziya ta ce, "Mamin yara na zo mu yi magan." Kujera ta nuna mata fuska ba walwala ta ce, "Zauna ina jin ki."

"Gani nake kamar ba mu kyatawa Alhaji ba, saboda Mahaifiyarsa tamkar mahaifiyarmu ce idan ta mu mahaifiyar ce muma babu yanda muka iya dole mu yi mata biyayya. Kina gani ko sadakar uku ba a yi mun taho gani nake gaskiya akwai..." Tun bata ƙarasa ba Hajiya Fauziyya ta katse ta da cewar,

"Don Allah idan wannan ne ya kawo ki kwashi tsummokaran ƙafafuwanki ki ƙara gaba, bana son kutungwila da shegen iyayi kamar ta macen kyankyaso. Kin san da haka kika ɗebo ƙafa kika taho ai sai ki tashi ki koma ba sai kin zo min ba." Hajiya Rahama ta miƙe tana cewa, "Ni na kawo kaina duk abin da kika faɗa, nina ja wa kaina."

"Oho fice ki bani wuri tun da ban gayyatoki ba, kinibabbiya kawai." Hajiya Fauziyya ta faɗa tana huci kamar wacce ta yi tseren gudu."

Hajiya Rahama na komawa sashenta ta samu ana kiran wayarta, tana dubawa ta ga lambar maigidansu har sai da hanjin cikinta ya kaɗa, da ƙyar ta yi ta maza ta ɗauki wayar da sallam. Bai amsa mata ya fara da cewa, "Rahama ina yi miki kallon mai hankali ashe ba haka ba ne. Kun nuna mini Mahaifiyata bata isa da ku ba, kun kama hanya kun taho ba tare da izinina ba. Na gode kun nuna min ni kaina ba wata tsiya bace a wurinku." Jiki a sanyaye Hajiya Rahama ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Alhaji wallahi nima na yi nadama amma yanzu zan taho insha..."

"Duk wacce ta sake ta fito daga gidan nan wallahi-wallahi a bakin aurenta. Tun da kun riga da kun yanke hukunci shi kenan, rasuwa dai Mahaifina ne ya rasu bana buƙatarku kuma komawa Ɗangwauro kamar mun koma mun gama, duk wacce ta ga za ta koma bismilla wacce ta ga ba za ta iya ba za ta iya komawa gidansu. Ita ma waccen zan kira na shaida mata." Yana gama maganar ya katse bai jira cewarta ba. Lokaci ɗaya ta ji duniya ta yi mata zafi don ita kanta ta san abin da suka yi ba su kyauta ba.

Gidan Baba Abubakar.

  Hajiya Ikilima ce zaune cikin mamaki ta dubi Hajiya Nafisa ta ce, "Wai wannan maganar da kike gaya mini da gaske ne ko kuma zolayata kike yi?" Haushi ya fara kamata da jin kalaman aminiyar tata ta ce, "Ƙawas kin san bama irin wannan wasan da ke. Serious ki bani shawara Allah dana koma Ɗangwauro gara aure ɗna ya mutu da bawan Allahn nan." Cikin zuciyar Hajiya Ikilima ƙyal saboda farinciki don ta jima tana hangen kanta a gidan wannan baƙin bafulantin mai cike da kwarjini, amma ina ƙawarta ta yi mata shamaki. Ta dube ta da fuskar tausayi ta ce, "Gaskiya dole ki ɗau mataki kika koma ƙauye wallahi kin faɗo, yanzu abin yi ki shirya na raka ki Ƙauyen tudun-wada akwai wani Malami yana taimako wallahi, zai taimaka miki sosai ke ko kashe tsohuwar nan kike son yi murus za a gama da ita." Hajiya Nafisa ta zaro ido waje tana faɗin, "Kin san fa ni bana haɗa hanya da ƴan tsibbu shawarwarin da kika saba bani dai su za ki bani. A kashe ta, ta rataya a wuyana. Ba za a yi haka ba kedai..." Bata ƙarasa maganar ba Aseem ya shiga falon don sarai ya ji abin da suke tattaunawa, sai ya wuce kan daininga da kofin shayi a hannu yana danne-dannen waya. Hajiya Ikilima ta saci kallonsa cikin ƙasa da murya ta ce, "Ko dai ya ji mu?" Hajiya Nafisa ita ma kallonsa ta yi sai ta ƙanƙance murya ta ce, "An ya kuwa amma bari ki ga." Hajiya Nafisa ta kalli Aseem ta ce, "Aseem jeka ɗakina ka ɗauko kuɗi akan mudubi ka tsallaka titi ka siyowa mamanka fura." Babu yanda ya iya haka ya tashi ya tafi kamar zai yi kuka don ya so jin ƙarashen hirar tasu. Dama ya jima yana zargin wannan matar da zuga mahaifiyarsu ashe kuwa ita ɗin ce take zuga ta.

Yana fita Hajiya Ikilima ta ci gaba da ɗora Hajiya Nafisa akan shawarar banza. Sai dai abin da kullin yake ɓata mata rai duk yanda take son ɗora Aminiyar tata akan biye-biyen malamai taƙi bada kai bori ya hau, kuma da haka take son cimma ƙudurinta akanta amma bahaushe ya ce a juri zuwa rafi watan tulu zai fashe.

Bayan Sadakar Bakwai.

   Dubu ce tafe za ta tafi makarantar Islamiyyar Malam Jafaru, tana tafe da ƴar maƙalaliyar jakarta ta buhu tana rera waƙar Bureka (Breaker) ta Jaruma, idan ka ji yanda take rairawa sai ka rantse ita ta biyawa mawaƙin waƙar. Ɗan'iya da ke tafe da Mahaifiyarsa ya ƙwala mata kira. "Dubu!"

Dubu ta juya hagu da dama sai a can daga nesa ta hango Ɗan'iya ai kuwa ta yashe baki, tana ɗaga masa hannu. Ɗan'iya sai da ya ga sun ɗan yi nisa da Dubu sannan ya ce, "Dubu mai kan Silba mun san komai ashe ƙwaryar molo aka yi miki." Lawandi da taron abokansa da ke bakin bishiyar dalbejiya me za su yi idan ba dariya ba. Ma'azu har da tuntsirawa kamar zai faɗi ƙasa. Wannan abu ba ƙaramin ɓata ran Dubu ya yi ba, ta tattakura ta ɗaga murya da cewa, "Eh na ji ɗin Ɗan gidan Balaraɓe kwarton dare" Da sauri su Lawandi suka riƙe baki kasancewar dama ana ta raɗe-raɗin wannan zargin da ake wa Balarabe ashe har kunnen yara ya fara bazuwa.

Hansatu mahaifiyar Ɗan'iya ta nufo wurin Dubu a fusace tana zuwa ta ce, "Iskancin na ki yau akan mijina ya sauka? Dan uwarki za ki ƙara cewa mijina kwarto?" Bata rufe baki ba sai da ta zabgawa Dubu mari sannan ta ɗora da cewa, "Wallahi ba Balarabe ba ko Bala na sake ji a bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Na lura iskancinki ƙara yawa yake saboda baki da mafaɗi..." Dubu ta fisge hijabinta tana cewa, "Allah ya isa kuma wallahi bashi kika ɗauka. Na faɗa waye bai san Balaraɓe kwarto bane har ɗakin Baba Auwalu sai da ya taɓa leƙawa lokacin da Yahanasu tana amarya. Banza kina gida kina tare da ɗan iska..." Kukan kura Hansatu ta yi ta fisgo Dubu ta fara jibga kamar Allah ya aikota. Jin Hansatu na niyyar hallakata ya sa ta fara kiciniyar ramawa, ai kuwa Hansatu ta cukwikwiye Dubu a cikin hijabi ta riƙa dukanta ta ko'ina sai da ƙyar su Lawandi suka ƙwaci Dubu. Suna fisgarta sai ga hijabinta a hannun Hansatu nan fa kan Dubu ya fito ral da shi yana ƙyalli don ranar Yaya Babba ta sharɓane mata shi da man kaɗanya. Nan Ɗan'iya ya fara tafi yana cewa, "Yeeh Dubu mai kan Silba (Silver)" Ai kuwa kafin wani lokaci tuni yara suka taru ana kallo, dukda tsoron da suke yi wa Dubu amma ruruma ta ɗauke hankalinsu suka fara sowa da tafi suna cewa, "Yeeh Dubu mai kan silba."

Idanun Dubu ne suka kaɗa jawur saboda baƙin ciki, sai dai har lokacin idanun Dubu a bushe suke babu ko ɗison hawaye don gudun kar a ga hawayenta yara su rainata. Cikin takaici ta kalli Hansatu ta ce, "Kwarankwatsa dubu bashi kika ɗauka kuma da ni kike zan cen." Ta juya ta kalli sauran yaran da suke tsokanarta ta ce, "Ku kuma za mu gauraya da ku kowanne shege sai na sa an harbe Uwarsa." Tana gama maganar ta suri jakarta da ke cen gefe ta fisgi hijabinta ta ɗora aka ta yi tafiyarta. Sai dai kusan rabin yaran jikinsu ya yi sanyi don suna tuno Yayan Dubu soja ne hantar cikinsu ta kaɗa har da masu bin ta suna bata haƙura amma babu wanda ta waiga, bare ya sa ran za ta amsa masa.

Dubu tun daga soron gidansu ta fara barke baki tana ihun kuka, amma ci kanki babu wanda ya tanka mata saboda sanin hali irin nata. Matan kawunan nata suna gani ta wuce cikin gida. Tana zuwa sashen su Yaya babba Inna Furai ta tare ta da tambaya, "To ƴar nema wa kika tsokano wanda ya fi ƙarfinki?" Dubu ta goge majina da hijabin hannunta sannan ta kuma yage baki tana ihu har sai da Yaya babba ta fito tana tambayarta.

"Inno wallahi daga yau ba zan ƙara fita waje ba. Ki dubi irin cin mutumcin da Hansatu ta yi mini ita da Ɗan'iya yau kashe ni ne kawai ba ta yi ba. Yara suka taru suna ce mini mai kan silba. Ni dai wallahi Allah ya isa da  askin nan da azzalumin nan ya yi mini." Dubu ta faɗa tana sake fashewa da kukan baƙinciki, don abin ba ƙaramin ciwo ya yi mata ba. Yaya Babba ta karɓe zan cen da cewar:

"Wallahi faɗi ki ƙara Dubu Allah ya iskan ki, don Allah me kika tsarewa Soja da zai sauke miki gashi ana zaune ƙalau? Hassada dai ka rasa wa za ka yi wa sai jininka. Na rantse da Allah ko uwarsa Nafisa ba za ta gwada miki gashi ba. Kanta da har gobe kamar hamtar ɗan isa ga uban sanƙo da almajiran ƙeya. Wallahi ni bansan abin da Garba ya gani a jikin gajeriyar matar nan ba ya aura, mace sai faɗin ran tsiya tana baje hanci kamar tattasai ya ji sanyi wuri." Dubu ban da tuntsira dariya babu abin da take yi har da hawaye saboda ƙeta don tuni ta goge hawayen idonta saboda ko ba komai Yaya babba ta biya ta, da ba'ar da ta yi wa mahaifiyar Aseem.

Inna Furai da ke gefe ta sa dariya ta ce, "Yaya ai ba za ki ga baje hanci ba sai ta shiga gaban mota yanda kika san funkaso." Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Yaya Babba ta ce, "Furaira wai dama ranar da muka fita da Garba tana gaba kina ankare da ita?" Inna Furai ta ce, "Ina gani mana wai har ca take ka saya mana wani abin mana a danja wai ita mai miji." Ai kuwa dubu me za ta yi idan ba dariya.

Yaya babba ta saki dariya ta ce, "Furaira alƙur'an ni kuma fuskar Nafisa ta ƙi ɓace mini lokacin da muka karɓi haihuwarta ta wannan yaron soja kin tuna lokacin har cewa take wai Inno zo na goyaki. Na ce mata ke Nafisa rabani da zancen goyon nan, rabona da goyo tun shekaru tsububu sai yau da kike nakuɗa za ki goya ni, na turmushe ki Garba ya ɗau gaba da ni." Inna Furai dariya har da hawaye sannan ta ce, "Yoo kafin ki zo har cewa take Inna karɓi cikin, na ce Nafisa lamari ya lalace ina Uwar Garba na karɓi cikin Garba ai ba kanta sai cewa ta yi har Garban na bar miki gabaɗaya." Dubu ta kife a wurin ban da dariya babu abin da take yi.
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 9
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

     Sallamar Baba Munkaila ne ya dawo da Dubu cikin hayyacinta, ba shiri ta shiga nutsuwarta ta fara kumbure-kumbure don ta san babu makawa zai samu labarin abin da ya faru tsakaninta da Hansatu. A daidai kan Dubu ya tsaya fuska babu walwala ya ce, "Ke!" Kamar bata ji shi ba ta yi biris, sai da ya sake buga mata tsawa sannan ta amsa. Cikin faɗa ya ci gaba da cewa, "Dubu ki kiyaye ni fa, kullin iskancinki da iya shegenki ƙara gaba yake ko? Ƴar ƙanƙanuwarki da ke har kin isa tarar matar aure ki ce za ki yi dambe da ita. Wallahi a hir ɗinki idan kika shiga hannuna na lahira sai ya fiki jin daɗi." Dubu dama kamar me jira yana dire zancensa ta fashe da kuka tana faɗin, "Dama na san komai ni za a ɗorawa alhalin ita ce bata da gaskiya." Rankwashi ya sakar mata a tsakiyar ka aikuwa ba ƙaramin shigarta ya yi ba, a zabure ta yi gefe ai kuwa Yaya babba dama ta fara cika ta dubi Baba Munkaila cikin faɗa ta ce, "Munkaila nakasa marainiyar Allah za ka yi? Ka duba irin ƙusar da ka sakar mata a tsakiyar ka sai ka huda mata kai, ka cuceni ka cuci Ado. Ko da ya kasance likita ba sai an sayi magunguna da alluran da za a yi mata aiki ba. Gaskiya bana so ka fita rayuwar yarinyar nan shi ya sa ga tana kamar ruwan aski kullin bata kumari." Baba Munkaila bai tankawa Yaya Babba ya dubi Dubu ya ce, "Tashi ki ɗau hijabinki ki wuce makaranta. " Tun bai rufe baki ba Dubu ta suri kayanta ta fita waje tana kurma uban ihu.

Inna Furai ta ja tsaki ta dubi Baba Munkaila ta ce, "Munkaila wai me ya sa ko yaushe burinka ka zazzagewa yarinyar nan albarkar da ke kanta? Yanzu da ka kaɗa ta waje idan ta shiga gari wa ya shiga uku idan ba mu ba." Yaya babba ta cafe zancen da cewa, "Wallahi idan na rasa Dubu hukuma ce za ta raba ni da Munkaila dama na daɗe ina zargin ba ƙaunarta kake ba." Baba Munkaila ya yi murmushi sannan ya ce, "Inno yanzu so kuke a zurawa Dubu ido ta taso babu nutsuwa da rashin ilimi? Kuna ganin Fatima yarinyar nan kowa sha'awarta yake, saboda ilimin addininta. Mu kuwa wa yake sha'awar Dubu? Ku shaida ne a rana sai a kawo muku ƙara ta yi sau goma. Amma Inna furai ai bai kamata mu zura mata ido haka har girmanta ba."

Yaya babba ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "Munkaila ka yi tunani, kuma wallahi ina jin hannu aka sawa Dubu dole na sake nema mata maganin baki don wallahi baki ba ɗan'uwa ba ne." Baba Munkaila na ganin ya yi wa Tsofaffin iyayen nasa dabara ya tashi ya fice daga gidan.

Dubu na fita ta goge hawayenta ta maƙale jakarta ta ɗauki hanyar islamiyya, sai dai tana saƙa da warwarar abin da za ta yi wa Hansatu don ta fanshewa abin da ta yi mata. Kamar daga sama tana shan kwanar hanyar da za ta sadata da makarantarsu sai ga Ɗan'iya ya fito da tallar wake da shinkafa a kansa, hannunsa na riƙe da bokitin ragadada. Yana ganinta ya yi baya da sauri a tsorace don ya san mai ƙwatarsa a hannun Dubu sai Allah, don haka bai yi wata-wata ba tun Dubu bata tanka masa ba ya fara cewa, "Dubu don Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Kamar wani abu bai haɗasu ba, haka Dubu ta basar da Ɗan'iya ta ce, "Da aka yi me?"

Ɗan'iya ya washe baki ya ce, "Faɗanki da Innarmu mana." Dubu ta zurawa bokitin ragadadar hannunsa ido, take ta ji yawunta ya tsinke, ta kai hannu za ta taɓa ya janye da sauri. Dubu ta riƙe ƙugu tana jinjina kai sannan ta ce, "Ɗan'iya wallahi ko ka bani bokitin nan ko kuma in haɗa gabaɗaya da Shinkafa da waken da shi bokitin ragadadar in kifar da su don wallahi wannan rigimar mun fara ta kenan ni da ku."

Tun ba ta rufe baki ba Ɗan'iya ya soma hawaye ya ce, "Don Allah ki mun rai wallahi Innarmu duka za ta yi min." Dubu ta yi dariyar mugunta ta ce, "Idan ka koma gida in ta tambayeka ka ce ta zo gudanmu ta karɓi kuɗinta." Ɗan'iya ya fara ja da baya Dubu na tsaye ta ce, "Tsaya-tsaya Ɗan'iya gaya mini duka kayan naka na nawa-nawa ne?" Ɗan'iya a tunaninsa rangwame Dubu za ta yi masa idan ta ji tsadar abinci ya taƙarƙare da ƙarfinsa ya ce, "Shinkafa da wake na Dubu biyu ne Ragadadar dubu ɗaya ce." Dubu ta yamutsa fuska ta ce, "To Allah ya yi belinka saboda wallahi da babu kayan nan sai na jiƙa maka jikinka, amma yanzu dole za ka bani bokitin ragadadar nan wallahi, ko in haɗa da kai da su duka na damalmale ku a cikin ƙasa." Ɗan'iya ya yi shiru yana nazari don ya san ciniki ko hamsin ne babu a ciki, Innarsu cin ubansa take bare bokitin Ragadada gabaɗaya. Ragadadar da sai sun yi da gaske suke samu Mahaifiyarsu ta ke basu yanka ɗaiɗai yau ita ce zai ɗauka ɗungurungun ya bada bokitinta.

Dubu na ganin haka ta buga tsalle tana ƙoƙarin janyo robar shinkafar, Ɗan'iya na ganin haka ya miƙa mata da sauri don kar ya yi biyu babu. Wani wawan kuka ya saki lokaci ɗaya ya juya zai koma gida Dubu ta sha gabansa ta ce, "Maza wuce wallahi ba za ka koma gida yanzu ba sai ka sayar da abincin nan salan ka min mugunta tun ban gama cinyewa ba ka sa azo gidanmu. Munafiki yana zare idanu kamar shege a rabon gado." Ta ƙarasa maganar tana ɗake masa ƙeya. Babu yanda ya iya haka ya nufi titi yana share hawayen fargaba da tashin hankali.

Dubu sai da ta saita Ɗan'iya ya bi titi sannan ta bi wani layi bata tsaya ko'ina ba sai cikin wani sabon gini da ba a ƙarasa ba. Zama ta yi dirshan ta kwashi ragadada tana ci tana siɗar romo, kafin wani lokaci tuni ta cinye shi tas, saboda ba ƙaramin daɗi ya yi ba, ya ji farin magi zaƙwai ga ɗan yaji-yaji. Tana gama ci ta sa gefen hijabinta ta goge baki. Ta ɗauki bokitin ta cika shi da yaji ta ɓoye a cikin hijabi ta fice daga cikin kangon.

Dubu bata tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan Hansatu, Hansatu na  tsaye a kan ƴarta Mairo da take ta zuba ragadada a ƙananan robobi, ta hango Dubu tsaye a ƙofar gida. Suna haɗa ido Dubu ta ƙarasa ciki kamar mutuniyar kirki ta ce, "A bani ragadada." Tana maganar tana sakin wani irin murmushi. Hansatu ta hangame baki tana yi wa Dubu kallon mamakin wato rashin kunyar Dubu ta bunƙasa haka. Balabare da ke bakin bishiya yana sharɓar ragadada ya yi zaraf ya ce, "Dubulliya ta nawa za a baki?" A fusace Hansatu ta ce, "Ta nawa za ki siya?" Ba musu Dubu ta miƙa naira ashirin nan fa Balarabe ya fara leƙenta yana kashe mata ido ɗaya. Dubu ta ɗauke kai kamar bata gan shi ba. A fakaice Dubu ta sunkuya tana gyara takalminta ta cikin hijabi ta dire mata bokitin ragadada, ta bayan ƙatuwar tukunyar ragadadar. Ta matsa can gefen bishiyar da Balarabe yake zaune. Hansatu mace ce mai matuƙar son kuɗi don duk abin da zai haɗa ku da ita muddin ka zo siyan abu wurinta bata zuciya. Tana da tsumulmula saboda ko ita bata iya zagewa ta ci ragadada idan ba mijinta Balabare da Allah ya jarrabeta da mutuwar sansa ba. Duk abin da Balarabe ya tambaya ba ta iya hana shi. Don haka a ƙa'ida kullin ta sauke tukunyar ragadada kwanonsa daban yake, kuma ko kara ya ajiye ba za ta iya tsallakawa ba.

Hansatu na ɗauko leda ta shiga wurgawa Dubu harara sanna ta fara zuba mata, za ta ƙulle ledar Balarabe ya ce, "Ke Hansatu ƙara mata ta hamsin." Ai kuwa kamar ya watsa mata ruwan zafi ta ɗago a zafafe ta ce, "A kan wane dalili za ka siya mata bayan ɗazun nan yarinyar nan ta gama ci mini mutumci..." Nan fa Hansatu ta zayyanewa Balarabe yanda suka yi, kamar ta rufe bakinsa shiru kake ji sai dai sam ba haka ya so ba, Dubu na karɓar ragadadarta ta nufi hanya za ta fita sai ga Ɗan'iya ya shiga gidan yana kwala ihu.

Da kallon mamaki ya bi Dubu har ta fice, Hansatu don sauri zaninta har faɗuwa yake. Ta fara jefo masa tambaya a hargitse, "Ɗan'iya ina bokitin ragadadar?" Tun bata rufe baki ba ya hau nuna ƙofa ya ce, "Dubu ce ta karɓe mini." Ai kuwa kamar wanda ya ɗanawa wuta haka Hansatu ta zabura tana cewa, "Buhun uban can, kai buɗe baki ka yi mini magana yanda zan fahimta." Dubu na jin haka ta fara zuba sauri bata tsaya ko'ina ba sai islamiyya.

Ɗan'iya ya zayyanewa Mahaifiyarsa abin da ya faru. Hansatu na jin ƙarashen labarin ta shuri takalma garin ɗaukan takalmi ƙafarta, ta shuri bokitin Ɗan'iya da ke cike da yashi. Hansatu ta nuna Bokitin tana faɗin, "Ɗan'iya ba wannan ba ne bakitin da ka fita da shi?" Nan take mamaki ya cika su. Hansatu ta suri bokitin ragadadar da ke cike da yashi, ko ta kan Balarabe bata bi ba ta wuce gidansu Dubu tana kumafar baki.

Lokacin da Yaya babba ta gama jin jawabinta, kallon sheƙeƙe ta yi wa Hansatu sannan ta ce, "Hansatu kura ko mayya kika mayar mini da Dubu da za ta iya cinye bokitin ragadada guda? Allah na tuba me ye ragadada abin da duk yaɗi da jijiya ne, me ye Dubu bata ci a gidan nan?" Takaici ya kama Hansatu ta yi ƙwafa sannan ta ce, "Dama ai sake ta samu shi ya sa take shuka tsiyar da take so, to wallahi daga kaina ba za ta sake yi wa wani haka ba." Tana gama masifar ta fice, Inna furai ta bita har soro tana mayar mata da martani.

"Aniyarki ta faɗa kanki, azzulama mai baƙin baki. Bayan zazzagar iya shegen da kika yi mata shi ne bai ishe ki ba za ki biyota har gida kenan." Sai da ta ga ficewar Hansatu ta juya ta samu Yaya tana faɗin, "Yaya an ya maganar yarinyar nan bata kan hanya, na san halin Dubu sarai za ta iya tare yaron nan ta karɓe bokitin ragadadar fa." Yaya babba ta yi ƙwafa cike da takaici ta ce, "Ai kuwa wallahi da na ɗebe mata falsafar albarka alƙur'an da babu ni babu ita."

Hansatu kai tsaye wurin mai unguwa ta wuce bayan ta kwashi gaisuwa ta zayyane masa abin da yake faruwa, ba shiri ya aika da kiran gaggawa gidan Marigayi mai carbi. Zuwan dogarawan ya yi daidai da zuwan Baba Abubakar shi da Aseem, wannan sammaci ba ƙaramin ɓata ran Baba Abubakar ya yi ba. Ya ci alwashin idan kuwa haka ta tabbata Dubu ce ta cinye ragadadar, tabbas ba ƙaramin hukunci zai ɗauka akanta ba don duk abin da Yaya babba za ta faɗa sai dai ya toshe kunnuwansa. Shi da Aseem suka wuce wurin mai unguwa ba tare da sun shiga cikin gidan ba. Suna zuwa aka aika kiran Dubu, tare da Dogarawan suka taho tana zuwa ta yi turus! Jiki a sanyaye ta zauna ta hangi Aseem na wurga mata harara sai Ɗan'iya da idanunsa suka yi wuri-wuri, saboda kukan da ya sha. Hansatu lokaci-lokaci take kallon Dubu tana ƙwafa cike da jin haushi.

   Shiru wurin ya ɗauka Mai gari ya ƙurawa Dubu ido yana son gano gaskiyar lamari, don ya san sarai Dubu za ta yi abin da ya fi haka, bayan an gabatar da abin da ya tara su a wurin, Mai unguwa ya kalli Ɗan'iya ya ce, "Ɗan'iya ko za ka gaya mana yanda abin da ya kasance." Ɗan'iya ya fyace majina sannan ya zayyane duk abin da ya faru tsakaninsa da Dubu. Tun bai rufe baki ba Dubu ta yi caraf ta fara magana, "Alƙur'an ƙarya yake yi mini haka kawai zai yi mini sharri saboda ba ƙaunata ake..." Da sauri Baba Abubakar ya katse ta yana yi mata daƙuwa Hansatu ta tura ɗankwali gaba tana faɗin, "Allah ya taimakeka ka yi mini tsakani da Dubu wallahi muddin ta sake shiga gonata sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Ƙwaranƙwatsa kuma sai an biya ni kuɗin ragadadata." Mai unguwa zai yi magana Aseem ya zaro dubu biyar ya miƙawa Hansatu yana faɗin, "Shi kenan magana ta wuce." Dubu na gefe da ta ga maƙudan kuɗin da aka bawa Hansatu ta yi zaraf ta ce, "Wallahi ragadadarta bata kai da kuɗin nan bayan kafin na karɓi bokitin Ɗan'iya ya ce mini ta dubu ɗaya ce." Ta ƙarasa maganar za ta warci kuɗin da sauri Hansatu ta maƙe su tana cewa, "Ai irin wannan asara kullin ma Allah ya kawo ta." Baba Garba saboda ɓacin rai sallama ya yi wa Mai gari ya tafi ya tafi, shi kuwa Aseem hannun Dubu ya fisga suna tafe yana haɗa hannunsa da nashi yana murzawa. Ban da wash! Babu abin da take yi saboda yanda hannunta yake yi mata raɗaɗi.

Suna shiga cikin gidan suka wuce sashen su Yaya babba har lokacin hannun Aseem na riƙe da Dubu. Tun da Yaya babba ta hango su take sakin murmushi, don shi kansa Aseem har sai da ya saki murmushi saboda yanda ya ga kakar ta shi cikin farinciki. Tun kafin su zauna ta sake washe baki tana faɗin, "Allah ƙadiran alamanyasha'u. Ikon Allah! Allah mai sanin abin da yake cikin zuciya." Gabaɗaya ba su kawo komai a ransu ba sai ɗan murmushi da suka yi. Bayan sun gaisa cikin ɓacin rai Baba Abubakar ya fara yi wa Dubu faɗa, kasancewar mutum ne ba mai zafi ba ya sa bai cika faɗa ba, amma Dubu ba ƙaramin tsora ta yi ba. Saboda dama mai haƙuri bai iya faɗa ba. Yana gamawa Yaya babba ta dasa nata faɗan.

"Maganar gaskiya Dubu kin wulaƙanta ni ki rasa me za ki karɓarwa yaro sai ragadada?" Inna Furai ce ta shiga ɗakin tana girgiza kai ta ce, "Don Allah Garba ka ji wata muguwar ɗabi'a, ka gaya mana meye Dubu bata ci a gidan nan?" Yaya babba ta yi ƙwafa ta ce, "Gane mini hanya Furaira neman maganar fa. Garba ka rabani da Dubu tun takaicinta bai kashe ni ba, ba zan iya ba gaskiya ba za ta ƙara kwanar mini a ɗaki ba. Ina dalili ta kashe ni ta cuci iyalaina, ko da dai kun girama shi fa Maraici ba daɗi gare shi. Don Allah Garba idan babu ni ba kun zama marayu gaba da baya ba? Na gaji gaskiya, ka sa Dubu a gaba ka tafi da ita na bar maka ita halak malak."

Baba Abubakar ba ƙaramin daɗi ya ji ba, don dama ya jima yana san ɗaukan Dubu Yaya babba ce take hanawa. Ya gyara zama ya ce, "Dama Inno na daɗe ina yi miki maganar amma yanzu tun da kin amince zan tafi da ita." Madadin Yaya babba ta yi magana sai ta yi jim sannan ta ce, "Ni fa Garba ba raba ni da Dubu ne bana so ka yi ba, gaskiya a riƙa zalintar marainiyar Allah ne bana so. Wannan matar taka ba ƙaunar Dubu take ba, sai ta zo ta yi ta gallazawa marainiyar Allah, ina nan ban san halin da ake ciki ba. Kai kuma mutuwar sonta kake ballantana ka tsawatar mata. Gidan Ado kuma Fauziyya sai jaraba mace sai masifa ko ƴaƴan cikinta ba ƙaunarsu take ba bare kuma Dubu, raba ni da bawa Ado Dubu ana zaune ƙalau. Ita kuma waccan mai tausayin ƙasar komai nata ba kuzari ina dalili inkai Dubu ta riƙa barinta da yunwa? Ni inbawa Rahama Dubu ta kashe ta da yunwa Allah ya tsare ni. Don Allah Garba wacce riba suke ci wai Rahama basa karyawa sai goman safe, mu da anan ƙarfe goma an fara haramar na rana. A'a gara Dubu ta yi zamanta a nan ina ganinta ina jin daɗi." Baba Abubakar ya girgiza kai don dama sai da ya ayyana haka amma ya ci alwashin ko da dabara sai ya karɓi Dubu muddin ya dawo gidan da zama, don barinta a haka har girmanta akwai gagarumar matsala.

Yaya Babba ta kalli Inna Furai ta ce, "Furaira ki gaya masa mana ai kyayi mini kara dai ko?" Inna Furai ta washe baki ta ce, "Garba wani abin alkhairi muka hango kuma mun san da kai da kaya duk mallakar wuya ne. Mun yanke shawara ni da Yaya ya kamata a ci gaba da yaɗa zumunci." Gaban Baba Abubakar sai da ya faɗi don ya san wataƙila wani abin za su ɓallo masa.

Inna Furai ta karɓe zan cen da cewa, "Ka san dai bikin su Salisu da  su Zulfa bayan babbar sallar nan ne kuma dududu bikin saura wata guda ina jin." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai ina jin lokacinma mun dawo nan." Inna Furai ta yi dariya ta ce, "Ai za ku sha hidima tun da auren ƴaƴa shida ba wasa ba." Baba Abubakar ya yi murmushi don shi kansa idan ya tuna bikin har daɗi yake ji ace cikin gidansu za su aurar da ƴaƴa shida maza da mata kuma duk auren gida abin akwai farinciki.

Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, "Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu." Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, "Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?"

Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, "Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan'uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu."
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

FREE PAGE 10
    https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼👆🏼 subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

   Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a jikinta. Dubu na maƙure a gefe sai raba idanu take don ita kanta ba ta san da wannan shawarar da Yaya babba ita da Inna Furai suka yanke ba. A madadin fushi sai ma wani murmushi da Aseem ya ke yi, wanda kana gani za ka tabbatar da murmushin mamaki ne da tsantsar baƙin ciki. Yaya babba da bata kawo komai a ranta ba ta ci gaba da cewa, "Allah ya sani dama wannan ne dalilin da ya sa na aika kiranka kai da Soja, don kune maganar ta shafa ba su Munkaila ba. Waye ya haifa maka Soja bayan kai da uwarsa Nafisa?" Yaya babba ta tambayi Baba Abubakar. Shiru ya yi yana murmushinsu na manya, sannan ya ɗago da kai ya ce,

"Inno na ji daɗin wannan maganar ta ki, kuma ni zan fi kowa farinciki da wannan haɗin domin abin da ya yi Dubu shi ya yi Aseem. Amma wani hanzari ba gudu ba..." Da sauri Yaya babba ta katse zancensa da cewar:

"Don Allah Garba ka faɗi alheri ko ka yi shiru. Wannan fa abin farinciki ne, kuma me ye aibun Dubu yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa. Ƙwaranƙwatsa dubu babu abin da Soja zai nunawa Dubu, kyau ya fita ko tsafta? Yarinyar da sai ta yi wanka sau uku a rana ko ba haka ba Furaira?" Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Ina dalili tun ba a ji ta bakin yara ba Garba za ka kawo mana hanzari, wannan kamar zazzage albarkar da ke cikin auren za ka yi. Gaskiya karka ɓata auren yara tun ba a je ko'ina ba, yoo Allah na tuba wane hanzari gare ka da ya wuce ka sa albarka?"

Baba Abubakar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inna ni fa baku fahimce ni ba. Ina nufin su yaran a fara ji ta bakinsu don kar ayi abu ba da son ransu ba. Amma idan kuna faɗin haka sai in ga kamar kuna nuna Dubu da Aseem ba ɗaya ba ne a wurina." Yaya babba ta washe baki ta ce, "Shi dai Soja na san ai ba zai ƙi ƴar uwarsa ba, ita kuwa Dubu kar ku ji ta, na san ta yanda zan shawo kanta." Aseem saboda takaici miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, Yaya babba na ganin haka ta saki dariyar farinciki tana faɗin,

"Ai na gaya muku wannan shiru-shirun da yake yi wallahi aure yake so, ja'iri ga shi nan kunya ta kama shi ya fita yana sunne kai, yoo waye zai samu Dubu bai yi farinciki na? Alƙur'an ana auren ku basu wata tara sai dai ku ji haihuwa, Soja wai mu zai yi wa hikima bai san na daɗe da gano lagwansa ba." Baba Abubakar ya yi shiru yana nazari domin ya san ba ƙaramin ruwa Yaya babba ta kunto masa ba, saboda ko makaho ya shafa fuskar Aseem ya san yana cikin yanayi marar daɗi. Saɓanin Dubu da ba za ka tantance ainihin halin da take ciki ba, na farinciki ne ko baƙinciki ba.

Yaya babba cikin murmushi ta kalli Baba Abubakar ta ce, "Yanzu dai Garba ka je ka shaidawa Nafisa halin da ake ciki don a fita haƙƙinta na mahaifiya, kar ta ji magana daga sama don ma bata da fushi ba kamar Fauziya Matar Ado ba, kai gaskiya Garba duk cikin ƴan uwanka akwai wanda ya yi dacen mace irinka kuwa? Allah ya sani Nafisa macen arziƙi ce idan na zageta sai dai na yi mata ƙazafi. Suma ƴan uwanka zan shaida musu abin da yake faruwa don kar su ji maganar aure bagatatan, na san Sule da baƙar zuciya sai ya ɗau fushi da ni ba gaira babu dalili. Yo ko auren na yi musu ban sanar musu ka ga laifina Garba? Kai ne dai uban soja halak malak, wani ne ya haifa mini kai? Ni ina na iya gaba halin ƴan wuta, ina masoyiyar Annabi (S.A.W) me zai haɗa ni da wuta ana zaune ƙalau? A'a rabani da wannan falsafar zan sanar da su da kaina, kar shaiɗan ya ɗebe ni idan suka ɗau gaba da ni na biye musu, ana zaune ƙalau na tsine musu su ɓalɓace." Baba Abubakar ya zaro kuɗi a aljihu ya dire musu a gabansu ya yunƙura jiki ba ƙwari ya ce, "To shi kenan Inno Ni bari na wuce." Cikin haɗin baki Yaya babba da Inna Furai suka fara faɗin, "Ka gaida gida Allah ya yi albarka."

Yana fita Dubu ta ɓata fuska ta ce, "Wai ke Inno ce miki na yi ina son shi bayan mugu ne, baki ga irin wuyar da ya bani ba rannan." Yaya Babba ta rungumo Dubu cikin lallashi ta ce, "Ke yi shirunki, kin san me ya sa na yi wannan haɗin?" Dubu zuciyarta ɗaya ta girgiza, Yaya babba ta ci gaba da cewa: "Allah ya sani Dubu idan ba mutuwa ba zan iya rabuwa da ke ba. Idan kika auri Soja a cikin gidan nan za ku zauna, ga wuri nan a gyara masa ku yi zamanku. Amma idan bare kika aura kin san dole ki fice daga gidan nan. Na san irin rayuwar da za ki yi a can gidan? Sam! Ba zan laminta ba a rabani da Marainiyar Allah ina ji ina gani." Daɗi ne ya kama Dubu lokaci ɗaya ta washe baki cikin farinciki. Lokaci ɗaya kuma sai ta ɓata fuska ta ce,

"Inno idan ya harbe ni da bindiga fa? Wallahi ba shi da tausayi tsaf kashe ni zai yi." Inna Furai ta hau jinjina kai sannan ta ce, "Wallahi har kotun ƙoli sai mun je a kan shari'ar nan. Ke bar zancen bindiga tsaf za ki saye zuciyar shi, tun da da me na birnin za su fiki?" Dubu ta ci gaba da washe baki tana jin nishaɗi ita a dole za ta auri Soja kuma ɗan gayu.

A ranar Yaya babba da Inna furai suka gama isar wa da Mutanen gidan, hukuncin da suka yanke har suke ɗorawa da cewar, yara tuni sun haɗa kawunansu don Aseem tsabar kunya tun da ya fito bai dawo ba. Ita kuma Dubu ban da murmushi babu abin da take yi, nan fa ƙananan maganganu suka fara tashi a cikin gidan kowa da abin da yake tsakura yana isarwa.

Lokacin da Baba Abubakar ya fita a cikin mota ya samu Aseem, yana zaune ya haɗa kai da sitiyari. Har Mahaifinsa ya shiga bai sani ba ya zurfafa cikin tunani. Da kallon tausayi ya dubi ɗan nasa ya ce,

"Aseem!" Jiki a sanyaye idanu jawuri ya ɗago ya kalli Mahaifinsa, murya a shaƙe ya ce, "Na'am Daddy."

"Dukda ban shiga zuciyarka ba amma san wannan hukuncin ba lallai ya yi maka daɗi ba." Kamar mai jira ya shagwaɓe murya yana faɗin, "Yanzu shi kenan Daddy duk abin da su Inno suka faɗa, komai ta ce sai dai ku hau ku zauna? Gaskiya ni kam babu yanda za a yi na auri waccen yarinyar. Yarinyar da kowa ya san bata da nutsuwa, don Allah Daddy ya za a yi ma na auri wata Dubu? Never wallahi." Ya ƙarasa maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Baba Abubakar ya yi murmushinsu na manya ya ce, "Rashin nutsuwarta ba komai ba ne idan har kana sonta, kai namiji ne za ka iya nusar da ita akan abin da ya dace." Cikin hanzari ya furta, "Ni ba na ma sonta, Allah ya sani ta nemi wani ta haɗa ta shi amma ba ni ba."

A karo na biyu Baba Abubakar ya sake kiran sunansa, "Aseem." A marairaice ya ɗago ya amsa sannan Mahaifinsa ya ci gaba da cewa, "Inno fa mahaifiyata ce kana ganin zan iya kaucewa umarninta, idan har ina neman albarka duniya da lahira? Su fa iyaye biyayya ake musu akan duk abin da suka buƙata matsawar bai saɓawa mahallici ba, ko da kuwa baka ƙaunar abin sai ka ga wata rana abin ya zame maka alkairi." Murya a raunane Aseem ya ce, "Daddy nima ban taɓa saɓa umarninka ba, amma maganar gaskiya idan aka tilasta ni na auri Dubu sai dai na barta a gidan nan, na yi tafiya ta."

"Da ka wulaƙanta ƴar ɗan'uwa bayan ka aureta; ai gara ka ce mini ban isa na saka ko na hanaka ba.  Zan yi ƙoƙarin ganin na shawo kan Inno idan ta amince shi kenan, idan bata amince ba, ka yi haƙuri ka amshi ƙadaddararka hannu bibbiyu, ka san kowanne bawa baya kaucewa ƙaddararsa, ta yiwu alkairin na gaba kai da kanka za ka ji daɗin haka. Saboda sautari muna ƙin abin da shi ne alkairi a tattare da mu sai daga baya mu fahimci haka." Shiru ne ya ratsa Aseem ya kasa furta komai, zuciyarsa ban da zafi babu abin da take yi masa. Jiki a sanyaye ya tuƙa mota suka wuce gida, kowa na saka da warwara a cikin zuciyarsa.

Tun shigar su cikin gidan Hajiya Nafisa ta fahimci gabaɗaya babu mai cikakkiyar walwala a tattare da su, har ta fi damuwa da damuwar Aseem saboda Baba Abubakar ba wani zaman daɗi suke yi ba, duk akan maganar komawarsu Ɗangwauro. Aseem na shiga ɗaki ta bi bayansa, a ɗaki ta same shi yana kaiwa da kawowa haɗe da kaiwa bango naushi. A ɗan tsorace ta fara watsa masa tambayoyi:

"Lafiya Asem? Wani abin ne ya faru da ku daga kai har Daddynku na ga baku da walwala?" Murya a can ƙasa ya ce, "Mommy babu komai, kawai wurin aiki ne suka kira ni akan wani issue ɗin." Kallon tsaf ta yi masa tana son gano gaskiyar abin da ya faɗa sannan ta ce, "An ya ba wani abin ne yake faruwa a Ɗangwaro ba?"

Da sauri ya kalle ta sai kuma ya ɗauke kai gefe saboda ambatar sunan garin, ba ƙaramin dawo masa da ɓacin rai ya yi ba, ya zauna a gefen katifarsa ya dafe kansa da hannu bibbiyu ya ce, "A'a Mommy." Taɓe baki ta yi ta ce, "Idan ma wani abin kuke ɓoyewa indai Hajiya babba ta kafe kai da fata na san ko ba daɗe ko ba jima zai fito fili." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin.

Aseem ya ƙi sanar da Mahaifiyarsa ne saboda ya san Daddynsu ba zai taɓa sanar mata a wannan ranar ba, duba da yanayin zaman da suke a wannan lokacin. Uwa-uba kuma ya san idan ya gaya mata kamar ya ƙara hura wutar tashin hankali a tsakanin iyayen nasu ne. Lokaci ɗaya tsanar Dubu ta mamaye zuciyarsa don duk ita ce silar komai, dukda hali irin na mahaifiyarsa tun da ya taso bai taɓa jin suna sa'insa ita da Mahaifinsa ba. Amma lokaci ɗaya ta tarwatsa farincikinsu ga auren iyayensu, da yake tangal-tangal tun da har lokacin Hajiya Nafisa na kan bakarta da ta koma ƙauyen nan, gara ya sallameta ta kwashi ƴaƴanta, ta riƙe a wurinta ko sa samu irin mijin da take buri da fatan su samu. Kamar yanda ta gama yi wa Aseem tanadin ƴar ƙawarta, saboda komai ta fi so su yi cikin bajinta da harkar girma.

A daren ranar ya haɗa kayansa tsaf a cikin jaka, washegari da sassafe ya wuce Lagos da yake acen yake aikinsa. Wannan ya ƙara tabbatarwa da Hajiya Nafisa tabbas akwai wata a ƙasa, amma zafin zuciya irin nata ya sa ba za ta iya tambayar mahaifinsa don jin abin da yake faruwa ba. Kuma ta lura shi kansa har lokacin baya cikin walwala, ga yawan waya da ta ga yana yi da ƴan'uwansa. Ga shi ba wata kyakkyawar alaƙa gare ta da facalolinta ba, bare ta kira ɗaya daga ciki don ta ji halin da ake ciki ba.

   BAYAN SATI BIYU

  Duk wani daɗin baki da dabara irin ta tsofaffi Yaya babba ta yi wa Dubu, kuma tuni ta ji ta aminta da Aseem a matsayin mijin aure. Don ba ƙaramin ƙawatawa Yaya babba ta riƙa yi mata ba, tana nuna mata irin rayuwar jin daɗin da za ta yi matuƙar da auri Aseem, hatta wanki ta daina sai dai ya ɗauko mai yi mata. Kan Dubu ba ƙaramin girma ya ƙara ba don ji ta yi duk faɗin garinsu babu wacce ta yi dacen mijin aure sama da ita.

Tuni maganar auren Aseem da Dubu ta karaɗe cikin ƙauyen Ɗangwauro, mutane da yawa mamakin wannan haɗin suke yi ganin Aseem cikakken ɗan gayu amma ya ƙare a auren Dubu. Cikin dangi sai tsegungumi ake da wannan maganar, lokacin da labarin auren Aseem da Dubu ya isa kunnen Hafsa ƴar wurin Hajiya Fauziyya, zama ta yi dirshen tana kuka don duk duniya babu wanda take so da ƙauna sama da Aseem, amma rana tsaka a ce wai Dubu ita ce za ta aure shi. Tun daga ranar ta bar walwala bata da aiki sai zaman ɗaki, ga shi an yi tambayar duniya ta ƙi faɗa, sai dai ta ce bata jin daɗi.

A wannan lokacin saura kwana uku tariyarsu a Ɗangwaro, sun gyara sashensu da sauran ɓangarorin gidan, gidan ya fito kamar a birni. Har fasalin ƙofar gida suka sauya suka rushe gaban gidan, suka saka ƙaton gate wanda mota za ta iya shiga har harabar wurin da suka zagaye da ya zama wurin parking space. Haka bikin su Dubu a lokacin saura sati biyu cif, su Yaya babba har an fara gyaran Amare. Aseem da Dubu a gefen sashen su Yaya babba aka gyara musu, gini ne mai ɗaki uku sai kitchen da banɗaki. Sai Salisu da Zulfa suna maƙota da su Dubu,  Bilalu da Murja suna maƙotaka da Baba Auwalu sai kuma Bashari da Maryama a suke maƙotaka da su Baba Adamu. Duk gyaran da ake wa amaren Yaya babba da Inna Furai sune jigo da ragamar komai.

Sai dai duk wannan budurin da ake yi mai gayya mai aiki, Mahaifiyar Aseem bata san wainar da ake toyawa ba har sai ana gobe tariyarsu, a lokacin da suke tsaka da hatsaniya ita da mijinta. Suma ganin Manyan akwatuna ta yi a ɗakinsa kishi ya rufe mata ido don a tsammaninta idan sun koma Ɗangwaro aure zai ƙara. Bayan ya gama sauraronta ya saki murmushin ƙeta don ya san muddin ya sanar da ita abin da yake faruwa ba lallai ta samu damar runtsawa a ranar ba. Saboda yana da tabbacin Aseem bai sanar mata da abin da yake faruwa ba, saboda har lokacin shi ma ɗaukan maganar yake kamar almara. Kafin lokacin akwai lokacin da Baba Abubakar ya kira a kan maganar kayan lefe, amma babu wata tsayayyiyar amsa da Aseem ya bashi. Hakan ne ya sa ya bugi ƙirji ya yi masa komai, saboda idan ya biye ta tashi ya san babu abin da Aseem zai yi.

Shi kuwa Aseem har kullin sai ya yi yunƙurun sanar wa mahaifiyarsa halin da ake ciki, amma fargabar tashin hankalin da za a shiga sai ta hana shi, don haka ya danne a bari Mahaifinsa ya sanar mata da kansa. Kuma dama sun riga da sun yi maganar shi da Mahaifinsa ya ce masa kada ya gaya mata har sai shi ya tunkareta ya gaya mata.

Bakinsa ɗauke da murmushi ya ce, 'Kanyan ɗanki Aseem ne za a kai masa na aure, yanzu haka saura sati biyu bikin dama ko baki tambaya ba yau na yi niyyar sanar da ke." Ku san suman tsaye ta yi jikinta har rawa yake ta ce, "Idan ma wasa kake min don Allah ka fito ka gaya mini gaskiya, idan aure za ka ƙara ba sai ka ɓillo min ta wannan sigar ba." Bai tanka mata ba ya buɗe durowar kayansa ya zaro katin ɗaurin aure ya miƙa mata. Hannu na rawa ya karɓa ta fara karantawa da yake ɗaurin auren mutane da yawa ne, sai ba za ido take don ta ga sunan Aseem da sunan  Amaryar da za a aura mata ba tare da ta santa ba.

Ƙauyen Ɗangwauro.

"Inno kullin haka kike faɗa amma fa har yau ko kirana a wayarki bai taɓa yi ba, kina ganin su Zulfa kullin cikin waya suke." Dubu ta faɗa tana kwaɓe fuska. Yaya babba ta washe baki ta ce, "Kin san Soja da kunya, tun yana yaro duk cikinku babu mai kunyarsa. Allah na tuba wacce kunya gare ku rannan ina jin Zulfa tana waya akan gadona, munafukar yarinyar ta ɗauka bacci nake har cewa take ko Lobin-lobin ko I Lobiyu. Wai har da cewa tana kewarsa. Don Allah Dubu ki ji mini falsafar rashin kunya ta dubi gardi kamar Salisu ta ce, tana kewarsa wannan bata cancanci istigifari ba?" Dubu ta bushe da dariya ta ce, "Yasin Inno kaɗan ma kika ji." Inno ta dafe ƙirji a tsorace sannan ta ce:

"Au tana faɗin abin da ya fi haka? Amma dai Zulfa an yi ƴar banzar yarinya, ta yi ta sunne kai ƙasa kamar mumina ashe shakiyya ce." Dubu ta ɗauko wayar Yaya babba ta ce don Allah Inno ki kira min shi."

Yaya babba ta ƙanƙance ido tana kallon wayar ta ce, "Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba, duba ki kira shi." Cike da ɗoki Dubu ta fara dubo lambar Aseem sai da, A ɗin kawai ta riƙe amma takamaimai sunan Aseem ba ta san shi ba. Sai da ta kira mutane biyu waɗanda sunansu ya fara daga A, na farko ta kira Baba Adamu da aka sawa Yaya babba sunansa da Ado sai lambar Auwalu. Sai a na uku ta samu ta yi nasarar kiran Aseem.

Cikin wata irin sanyayyiyar murya ta ji ya ɗauka da cewa, "Salamu alaikum." Lumshe ido ta yi ƙirjinta na bugawa ta yi ta maza ta ce, "Wa'alaikas salam."

Jin ba muryar Yaya babba bace ya sa ya furta, "Wace?"

"Me lob ni ce na kira ka, Dubu ce i lobiyu." Dubu ta faɗa cike da ɗoki don ta saba jin waɗannan kalaman a bakin su Zulfa idan suna waya da samarinsu, suna cewa My love da i love you.
[7/1, 10:17 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 11

   Aseem kusan sandarewa ya yi da jin kalaman Dubu, don ya fahimci inda maganar tata ta dosa dukda bata faɗa yanda ake furtawa ba. Babban abin da ya fi ba shi mamaki yana yi mata kallon ƙaramar yarinya sakarai marar wayo, ashe shi take yi wa kallon haka? Tun da har ta san ta kira saurayi ta ce masa My Love, ba tare da kunya ko jin nauyi ba. Jin ya yi shiru ya sa Dubu ta saci kallon Yaya babba ta sake cewa:

"Me lob wallahi ina ta kewarka kuma na yi musun ɗinka." Yaya babba na jin haka ta saki murmushin farinciki, don bata ɗauka Dubu za ta iya nutsuwa lokaci ɗaya ta yi waya da saurayi a haka ba.

Aseem bai gama tunani ba Dubu ta sake jefa shi cikin kogin mamaki, da jin kalaman da idan za a sa mata wuƙa bata san takamaimai abin da suke nufi ba. Dubu ba ta damu da jin shirun da ya yi ba ta ci gaba da jawabi.

"Me lob dama kiran da na yi maka don mu gaisa ne, na san kaima ka yi kewata; kuma ban ji ka ce komai ba..." Tun bata ƙarasa ba ya buga mata tsawar da ta katse ragowar kalamanta da cewar: "Ke! Kina hauka ne?" A tsora ce Dubu ta zame wayar daga kunne, ganin haka ya sa Yaya babba ta kalleta tana faɗin, "Dubu lafiyarki kike razana kamar wacce aka ɗanawa wuta?" Wayar Dubu ta miƙa mata tana faɗin, "Riƙe ki ji abin da yake faɗa Inno." Da sauri Yaya babba ta karɓi wayar ta sa a kunne tana faɗin, "Sojaaa." Aseem na jin haka ƙit ya kashe wayar yana huci. Maganganun Dubu sun jima suna yi masa yawo a rai, yana mamakin har yaushe ta ga makwancinsa da za ta kira shi a waya tana ce masa My love.

Yaya babba ta yi zuru tana nazari sannan ta ce, "Dubu me kika yi wa Soja da zafi haka da zai hau yi miki barazana?" Dubu ta kwaɓe  fuska ta ce, "Inno kina ji dai a gabanki na yi wayar." Wayar ta sake miƙawa Dubu ta ce, "Maza lalubo mini lambar Garba, alƙur'an idan shi yake zuge shi a kanki zan ji dalili. Saboda Allah me ya sa Garba ya cika hassada? Dama tun rannan na lura da hassadar da yake yi wa Soja akan aurenki. A'a ba halina ya gada ba bare kuma mahaifinsa, Allah ya sani wannan ɗabi'ar ƴan wuta ce idan kuma Garba ya ɗore a haka na shiga falsafar tashin hankali a ce jinina na da ɗabi'ar ƴan wuta ina na kama." Dubu ta gama dube-dubenta ta miƙawa Yaya Babba wayar ta ce, "Kin san dai ba iya nemo lambarsa na yi ba Inno kawai ki kira Baba Munkaila, ki sa ya kira shi" Suna cikin haka Salisu ya shiga shi da abokinsa Musbahu, da sauri Yaya babba ta miƙa masa waya ta ce, "Maza kira mini Garba." Da ido ya tsare Dubu da kallon tuhuma, don ya san ita take juya Yaya babba kamar waina, ya ce, "Me za ki ce masa Inno."

"Me ye ma ba zan ce masa ba Ɗan nan? Ka kira mini shi idan ba za ka kira ba, wuce ka kira mini ubanka ko Munkaila in sa su kira shi." Gudun magana irin na Yaya babba ya sa ya karɓa ya kira mata Baba Abubakar, sai dai an yi rashin sa'a wayar a kashe take.

Musbahu abokin Salisu cikin ladabi ya gaishe da Yaya babba ta washe baki ta ce, "Lafiya ƙalau Musbahu ya Uwale?" Ya amsa mata cikin girmamawa, Yaya babba ta ɗora da cewa:

"Ina ma Soja ya samu abokan ƙwarai irin ka Musbahu, don Allah da bai more ba? Don Allah waye ba ya san farantawa, ka duba yarinyar nan Dubu daga  kiran Soja zai fara sauke mata falsafar rashin mutumci, ana zaune ƙalau don Allah wannan halin mutumci ne?" Musbahu ya yi murmushi ya ce, "Gaskiya bai kyauta ba Inno, amma ki yi haƙuri."

"Don Allah rabani da haƙurin nan Musbahu! Kai Salisu ba ina ji rannan Zulfa na ce masa tana kewarka ba. Musbahau don Allah ka ji wata lalata irin ta ƴaƴan zamani. Lokacin da aka ɗaura auren uwar Zulfa, ni kaina da nake uwar miji sai da ta kwana a ɗakina, kwananta biyu tana gudun miji za ta yi na uku na ce, a'a ta rabani da wannan falsafar kar Munkaila ya ɗau gaba da ni ana zaune ƙalau. Munkaila kunya Kulu kunya yooo gadon wa tayo a cikinsu na rashin kunya? Don Allah gane mini hanya Musbahu." Salisu ya karɓe zancen da cewa, "To ke tsohuwa ina ruwanki da sa ido ne?"

Kafin Yaya babba ta yi magana Baba Munkaila ya shiga ɗakin da sallama, Yaya babba na ganinsa ta saki dariya ta ce: "Ɗan halaka kaƙi ambato!" Baba Munkaila ya yi murmushin jin daɗi don ya ɗauka labarin wata bajintar ta shi Yaya babba take bayarwa, da ta ganshi ta faɗi haka.

Yaya babba sai da ta ga Baba Munkaila ya zaune a gefe kusa da ita, ta ɗaga faifai ta miƙa masa kwaɗon rama ta ci gaba da cewa, "Kun ganshi nan a daren angwancinsa ma kasa shiga ɗakin amarya ya yi, kunya dai a cikin Munkaila har da ta siyarwa. Ashe biyu ce ta haɗu shi kunya Kulu kunya, yoo bayan kwana biyu ba sai amarya ta hau guje-guje ba."

Kunyar duniya ta kama Baba Munkaila da ke zaune a ɗaki ɗaya, da Ɗansa Salisu kuma saurin babbar ƴar sa Zulfa da ake shirin ɗaura musu aure. Hakan ce ta faru a ɓangaren Salisu ba ƙaramin kunya ya ji ba, daga shi har Musbahu aka rasa mai bakin magana. Dubu na gefe sai sunne kai take tana dariya ƙasa-ƙasa, musamman da ta lura da yadda Baba Munkaila ya yi fiƙi-fiƙi da idanu, ba abin ya tashi ba yaran ɗakin su fahimci abin da ya tashe shi daga ɗakin. Yaya babba kuwa ko a jikinta ta ci gaba da cewa:

"Kai Allah dai ya sawaƙe kuma bayan kwana biyu fa sai ganin ciki muka yi, na yi dariya na ce Allah mai iko ashe dai rabon a kusa yake. Yoo ashe kunyar duk ta banza ce ban sani ba sai ranar da Kulu take naƙuda." Salisu ya yi karaf ya ce, "To mu dai ba tambayarki muka yi ba." Saboda kunya Baba Munkaila kasa ɗaukan lomar hannunsa ya kai baki ya yi.

Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Salisu ka fita a idona tun da ba kai nake gayawa ba, Musbahu ko ka ji na ambaci sunansa?" Musbahu ya ce, "A'a Inno." Dubu da ke gefe ta ce, "Inno idan baya son jin labarin ai mu muna so." Baba Munkaila ya zuba mata uwar harara, Ita kuwa Yaya babba kamar wacce aka ƙarawa ƙaimi ta ce, "Allah dai ya yi miki albarka Dubu. Kin ga Munkaila ban taɓa sanin ya iya waƙar salawatu ba alƙur'an sai ranar da Kulu take naƙudu. Ranar mun ga abu iri-iri ni da Furaira, daga fara biya mata suratul Khaifi sai ya zarce da salawaitu. Ni kuwa na hau istigifari don ina gudun fushin Ubangiji an haɗa ayarsa da waƙa. Ban tsinke da lamarin Munkaila ba sai da na ga yana kuka wai ta mayar masa cikin jikinsa. Ni kuwa na ce raba kanka da haihuwa Munkaila idan cikin ya dawo jikinka, daga nan har ƙofar dawanau sai an ji ihunka. Yo wa ya gaya masa haihuwa ta maza ce wannan jarumtar sai mata..." Baba Munkaila a hanzarce ya miƙe zai fita daga ɗakin, saboda tun da yake bai taɓa jin kunya irin ta ranar ba, bisa tsautsayi ya yi tuntube jallabiyyar jikinsa ta taɗe shi ji kake kiriiiiif ya zube a ƙasa.

   Dubu kuwa ta kwashe da wata irin dariyar ƙeta, don dama ta jima tana dannewa bata samu ta yi dariyar ba sai ta wannan dalilin. Salisu na ganin sirikinsa ya faɗi ya fara faɗin, "Subhanallah Sannu Baffa." Duk suka yi carko-carko Salisu na son zuwa ya taimakawa Baba Munkaila yana fargabar faɗansa, Musbahu da yake gimtse dariyarsa ya kalli Salisu yana yi masa inkiya da ya  je ya taimaka masa. Yaya babba ta riƙe haɓa tana faɗin,

"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. An ya Munkaila baka taɓa yi wa mutanen wurin nan fitsari a tsakiyar kai ba kuwa? Idan ban manta ba wannan ce faɗuwarka ta biyar tun daga haihuwarka. Ta ƙarshen da ka yi kafin wannan idan na tuna tun baka fi shekara goma ba lokacin an yi muku shayi kai da su Ado, ka warto cinyar kaza a hannunsa ya biyo ka ya murɗe ya karɓe; to gashi yanzu ma an kwatanta." Dubu dariya take har da hawaye dukda ta san wannan dariya da take yi tamkar bashin duka ta ɗauka da hannunta. Salisu ya ƙarasa wurin yana dafa Baba Munkaila ya ce, "Sannu Baffa ko na taimaka maka." Da sauri Baba Munkaila ya fisge hannunsa ya ce, "Sake ni bana so." Da hanzari ya miƙe yana ɗingisa ƙafa ya fita daga ɗakin.

Yaya babba ta jinjina kai ta ce, "Allah ya fissheka alheri Salisu don wallahi Munkaila ya ɗau fushi da kai, yo meye za ka ce za ka taimaka masa gazawa ya yi?" Salisu a ɗan fusace ya ce, "Don Allah Inno ki yi mana shiru, ta ya za a yi na fusata shi bayan ke kika ɓata komai kin zauna kina zancen angwancinsa a gabana; wai har da waƙar salawaitu, ba dole ki sashi ya tashi ya fice ba." Yaya babba ta hamgame baki ta ce, "Don Allah Musbahu me ye laifina a nan don na baku labarin angwancin Munkaila, ba Uba yake a wurinku ba?" Musbahu ya yi murmushi ya ce, "Inno Salisu fa sirinkinsa ne auren Zulfa zai yi kin ga ai hakan da kika faɗa bai kamata ba a gabansa." A sanyaye Yaya babba ta kalli Salisu ta ce, "Salisu kana ganih Munkaila bai yi fushi ba?"

"Ai idan da abin da ya fi fushi ya ɗauka da ke duk ɗaya makafi sun yi dare." Salisu ya yi maganar a ƙule. Yaya babba ta russunar da kai ta ce, "Allah ya sani ban iya gaba ba halin ƴan wuta ne, ni kuwa me zai haɗa ni da wuta a na zaune ƙalau? A'a raba ni da Munkaila ya je ya yi ta gabarsa ko a lahira karma ya nuna ya sanni, bare mu ƙulla alaƙa. Musbahu ku shaida ko a lahira za ku tsaya mini shaidu a gaban Allah."

Da sauri Salisu ya ce, "Ai ko a gidan duniya ba zan tsaya miki shaida ba Inno bare a lahira, kema ki yi ta kanki a wannan ranar da har kike neman wani ya yi miki shaida tsakanin ki da Baffa." Yaya babba ta yi ƙwafa a fusace ta ce, "An ya kana ƙaunata Salisu kuwa?" Salisu ya wara mata hannu ya ce, "Ba tabbas!" A tsorace Yaya babba ta ce, "Alƙur'an bari su Sule su zo sai sun yi mini iyaka da kai, ko a lahira karka nuna ka taɓa sanina." Salisu ya miƙe shi da Musbahu sannan ya ce, "Inno a ina ma zan ganki muna can sahun ƴan aljanna." Yana gama maganar suka fita, ai kuwa Yaya babba ta fashe da kuka tana ƙwalawa Baba Sule kira da sauran ƴaƴanta kira.

Gidan Baba Abubakar.

  Hajiya Nafisa ba ta san lokacin da ta lailayo wani ashar ta maka ba, a tsananin fusace ta ce, "Ƴar gidan uban waye da za ka bata ɗana ba tare da shawara ba? Nawa Mahaifinta ya baka da za ka yi abu cikin ƙanƙanin lokaci? Wacece wannan Haliman? Wane muƙami ubanta yake da shi a ƙasarnan?" Ta jero masa tambayoyi wannan na bin wannan kamar tsohuwar ƴar jarida, saboda yanda idonta ya rufe ko sunan Mahaifin Dubu da inkiyarsu ta ƊANGWAURO  ba ta yi ba. Murmushin tura haushi ya yi ya ce, "Hala baki lura da bayanan da ke jikin katin ba? Me kike ci na baka na zuba Nafisa? Ai duk gaggawar Unguwar zoma ta bari a haihu. Ki wara ido da kyau ki sake karanta bayanin da ke cikin katin.

Kamar sabuwar makauniya haka ta fara ware idanu tana bi daki-daki, kamar wacce kunama ta ɗanawa harbi lokaci ɗaya ta zabura jikinta har rawa yake. Idonta ya sake ƙanƙancewa, fuskarta murtuk saboda ɓacin rai. Ja da baya ta fara yi tana nuna shi bakinta na rawa ta ce, "Wai kana nufin Dubu za a ɗaura masa? Wallahi ba zai yuwu ba. Na rantse da Allah idan nina haifi Aseem ba zai auri wannan jakar yarinyar mahaukaciya ba." Murmushin takaici ya yi a karo na biyu fuskarsa ba walwala saboda ɗacin maganganunta, tabbas shi kansa ya san Dubu na da wasu ɗabi'u, da dole tana buƙatar gyara amma kalaman sun yi zafi akanta, duba da irin riƙon da Yaya babba ta yi mata. Kuma duk lalacewarta ƴan ɗan'uwansa ce, ta ya za bari a ci zarafinta a gabansa? Tana shirin sake yin magana ya katse ta da cewa, "Hawainiyarki ta kiyayi ramata Nafisa, karki ƙara furta kalma mara daɗi akan yarinyar nan idan ba haka ba kuma ranki zai yi mummunan ɓaci. Aseem ɗana ne kuma ina da ikon aura masa duk yarinyar da na yi niyya, Alhamdullah biyyyyar da nake wa Mahaifiyata ba ta tashi a banza ba, domin Aseem bai watsa mini ƙasa a ido ba. Tabbas wannan abin ɗaga hannu ne na godewa Ubangiji, saboda ba kowanne matashi mai ji da ƙuruciya za a yi wa wannan auren ba, kuma ya amince." Sakin baki ta yi tana kallonsa, dukda gwiwoyinta sun fara sanyin da jin kalamansa, hakan bata sa ta bada ƙofar da Baba Abuabakar zai ga lagwanta ba, murya a daƙile ta ce, "Shi da kansa Aseem ya amince da wannan maganar? Tabbas biri ya yi kama da mutum! Amma za mu gauraya da shi wallahi sai dai ya zaɓa ko ni ko auren waccen ballagazar." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin fuuuu kamar guguwar da take tsaka da tashi a tsakiyar sahara. Yana ganin fitarta ta ɗau waya ya kira Aseem tare da sanar masa da ya zauna cikin shiri, don a kowanne lokaci mahaifiyarsa za ta iya kiransa a waya akan wannan maganar.

Lokacin da Aseem ya katse kiran da ya yi wa Dubu, dogon tsaki ya yi yana furzar da iska mai zafi. Nasir da ke gefe ya zura masa ido bayan wani lokaci ya ce, "Aseem!" Bai ɗago ya kalle shi ba sai ma girgiza ƙafarsa da yake yi, don ayyanawa yake yau da yana kusa da Dubu mai hana shi shaƙeta a gidan sai Allah. Nasir bai damu ba ya ci gaba da cewa, "Tun bayan dawowarka na lura kana cikin damuwa, na yi tsammanin ni da kai mun zama ɗaya ashe ba haka ba ne. Ko makaho ya shafa ka ya san kana cikin damuwa, wai mene ne yake damunka?" Aseem ya ɗago da jajayan idanunsa ya ce, "Nasir ba ni kara ɗaya na busa."

Da sauri Nasir ya yi baya haɗe da zaro ido waje, kamar wanda ya yi arangama da kumurcin maciji. Ya fara gyaɗa kai kamar kosasshen ƙadanfare sannan ya ce, "Lallai gumi ta yi gumi arniya da ambaton Allah. Aseem kai da kake hanani busawa yau kai ne kake neman kara ɗaya? Abokina bana fatan ka fara wannan harkar muma da muke busa sigarin Allah ya ye mana, meye labari."

"Aure za a yi mini."

Aseem ya faɗa murya na rawa kamar zai yi kuka. Nasir ya riƙe baki tare da bushewa da dariya ya ce, "Shegen kaya ka ce kakarka ta yanke saƙa, ɗan iska sanyin bana sai dai ka ji a bakinmu."

Aseem ya sake tamke fuska ya ce, "Nasir don Allah fita ka bani wuri." Nasir ya yi murmushi ya ce, "Tuba na ke abokina ya ake ciki?" Nan take Aseem ya zayyana masa duk abin da yake faruwa, kasancewar Nasir abokin Aseem ne tun kafin su shiga aikin Soja, kusan kowa ya san cikin ɗan'uwansa game da harkokin yau da kullin. Lokaci ɗaya Nasir ya buga tsalle ya ce, "Shi ne kake wani marairaicewa kamar mace, kai fa ba wayis ba ne. Wallahi irin ƴan shilolin nan sun fi saurin ɗaukan darasi sai ma ka yi..." Aseem ya katse shi da cewar, "Kai dama duk in da iskanci ya zo ya sameka shi kenan zai shafawa ransa salama." Suna tsaka da magana Daddy ya kira shi ya sanar da shi maganar Mommy, ba a ɗauki lokaci ba Mommy ta kira shi, tashi ya yi tsam daga ɗakin zai fita, ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ka ga Ango ya kusa shan mai, a miƙa min gaisuwa idan an gama yayyafawa fure ruwa mai sanyi." Aseem bai bi ta kansa ba ya fice daga ɗakin.

   Kamar kazar da aka tsamo daga kogi haka Aseem ya dawo cikin ɗakin a sanyaye, kan katifa ya haye ya kwanta yana jin maganganun mahaifiyarsa na sake dawowa masa sababbi fil a cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa abokinsa Nasir ya fita ya bar shi domin ya fahimci abokin nasa na cikin wani yanayi.

Bahaushe ya ce, "Sanin hali ya fi sanin kama." Tun bayan da kace-nace ya faru tsakanin Baba Abubakar da Hajiya Nafisa, washegari ya kwashi su Nabila a mota ko su bai sanar da su inda zai kaisu ba, sai da suka je ƙofar gidan Baba Adamu sannan ya kalle su fuska a tamke ya ce, "Ku shiga gidan Baffanku za su wuce da ku Ɗangwauro, duk wacce ta saɓa umarnina zan gauraya da ita." Duk abin da yake faruwa Mommy ta sanar da su, don haka sun san duk halin da ake ciki. Sun san waye mahaifinsu domin mutum ne mai matuƙar haƙuri, amma idan ransa ya ɓaci kallon fuskarsa kaɗai zai sa ka shiga taitayinka. Ko kaɗan ba sa son komawa Ɗangwauro, amma babu fuskar da za su yi wa mahaifinsu musun maganar. Sai da ya ga shigar su da jimawa sannan ya tada mota ya bar ƙofar gidan, saboda tuni sun gama magana da ɗan'uwansa akan zuwan na su Nabila. Baba Abubakar da biyu ya yi wa Hajiya Nafisa haka, saboda ya san yanda take da matsanancin son yara ba za ta taɓa jurar ya rabata da su ba. Shi kansa yana son matarsa saboda wani hargitsi bai cika haɗa shi da ita ba, hasalima tun da suka yi aure ba su taɓa wani gagarumin tashin hankali kamar wannan ba. Ya santa sarai idan ya ce zai biyota ta lallami ba za ta taɓa komawa ba, amma idan ya biyo mata ta wannan sigar za ta fi ɗaukan abin da muhimmanci kuma za ta aminci cikin ruwan sanyi.

Tun a ranar ta kira Aminiyarta Hajiya Ikilima ta sanar da ita duk abin da yake faruwa, sam abin bai ɗaga mata hankali ba sai ma mamaki da tayi lokacin da ta ji Aseem ya amince da maganar auren. Abin da ya sa bata damu don bata da ƴa mace, saboda a koyaushe ta kalli Aseem rayawa take da tana da ƴa mace, da ko sama za ta faɗo sai ta yi duk yanda za ta yi Aseem ya aure ta. Rufaida ƴar yayarta ta so haɗata da shi, amma da ta ga Rufaida ta samu wanda ya fi Aseem kuɗi shi kenan ta watsar da maganar Aseem.
[7/2, 3:24 PM] Ameera Adam🌚: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 12

  Duk wata huɗuba mara amfani Hajiya Ikilima sai da ta ɗora Hajiya Nafisa a kai kala-kala, sai dai suna saƙa ta gaba ta baya na warwarewa domin a lokacin da suke tsaka da maganar tuni Baba Abubakar ya kwashi su Nabila ya fice da su daga gidan. Kuma ko da ya dawo bai bi ta kanta ba bare ma ta sa ran zai sanar da ita wurin da suke. Ganin bata ga wulgawar ɗaya daga cikinsu ba ya sa ta kira wayar Nabila tana kira bugu ɗaya ta ɗauka, baki na rawa  Nabila ta ce:

"Mommy tun ɗazu nake yi miki filis kwal mi (Please call me) amma na ji ki shiru, ni kuma wayata babu kuɗi." Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Wallahi ban lura ba ina kuka shiga ne." Nan take Nabila ta sanar mata da abin da ya faru, Mommy ban da surfa bala'i babu abin da take yi. Suna gama wayar ta nufi sashen Baba Abubakar fuuuu tana tafe tana surfa faɗa kamar za ta ari baki.  Ko sallama bata yi ba ta doka ƙofar ɗakin tana faɗin, "Daddyn yara wai yaushe ka zama haka ban sani ba? Waye ya haifamin su Nabila da za ka kwashe mini su ka kaisu gidan su Fauziyya, na lura zaman lafiya ne baka so amma wallahi a wannan karon zan nuna maka ɓacin raina." Sai da ta kammala ya juya ya kalle ta ya ce: "Na ji kin ce ba za ki koma Ɗangwauro ba shi ya sa na kwashe yarana na kaisu gidan ɗan'uwana, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne." Taku biyu ya yi ya buɗe durowar kayansa ya zaro wata doguwar takarda ya ɗora mata akan gado yana faɗin, "Don haka na yanke wannan hukunci ina ganin zai fi zama masalaha, ki tattare kayanki wuri ɗaya saboda gobe zan turo a ƙarasa kwashe kayan gidan nan." Yana gama maganar ya fara ɗaura agogon hannunsa, ya ci gaba da harkar gabansa kamar ma bai san da mutum a wurin ba.

    Tuni jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi idanunta suka ciko da ƙwalla ta kasa ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Daddyn yara sakina ka yi saboda abin da bai taka kara ya karya ba?" Turare ya fesa a jiki sannan ya ɗauki wayoyinsa zai fita ta sha gabansa ta ci gaba da cewa, "Wallahi indai akan maganar auren Aseem ne bana ɗar ko dana-sanin hukuncin da ka yanke, tabbas na yadda Namiji ƙudan zuma ne (Littafin Maman Islam ne, ku neme shi don jin yanda labarinta yake mai tafe da ɗaukan darasi.) Na yarda duk yadda mace ta kai da shekaru a gidan aure, dole akwai shafin da namiji zai iya buɗe mata ba tare da inkiya ba. Na gode sosai da wannan son zuciya da kuka nuna min." Hawaye ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar bakinta.

Murmushi ya yi da jin kalamanta saboda ya san dama muddin ta yi tozali da takardar da ya ajiye mata abin da za ta kawo kenan, shi kuwa gani yake wane laifi za ta aikata masa wanda zai saka mata da hukuncin saki? Matar da ta aure shi tun yana malamin makarantar firamare har Allah ya ɗaga dajarasa ya zama babban malami a makaran jami'a. Yana tsaka da tunani ya ji ta ci gaba da cewa:

"Kai namiji ne ba lallai ka fahimci ɗacin abin da nake ji na mahaifiya ba, ace ina matsayin mahaifiyar Aseem a yi masa mata ba tare da sanina ba har sai bikin ya rage ƴan kwanaki. An ce za mu koma ƙauye rayuwar ƴaƴana za ta nakasta, duk wannan bai isa ba har sai da ka raba ni da ƴaƴana me ya sa ahalinku suka fiye san kansu ne?" Maganganunta sun taɓa shi sosai kuma tabbas kowacce mahaifiya ba za ta so abin da aka yi mata ba, amma hakan shi ne mafita tun da shima yana yi ne domin biyayya ga mahaifiyarsa. Tana shirin sake magana ya ɗaga mata hannu tare da cewa, "Maganar auren Aseem fatan alheri za ki yi masa, domin bakinki kamar yankan wuƙa yake idan kika aibanta auren ba Dubu kawai kika yi wa ba, bakinki zai iya faɗawa har kan zuri'ar da za su haifa." Yana gama maganar ya fice daga ɗakin. Sai da ta zauna ta ci kuka ta godewa Allah sannan ta ɗauki takarda ta wuce ɗakinta, ta fara haɗa kaya sannan ta wuce unguwar Ɗorayi gidan mahaifiyarta.

Duk abin da ka ga bai zo ba sai dai idan ba a ƙayyade masa lokaci ba,  ranar juma'a iyalan Yaya babba suka tarkato gabaɗaya suka koma sabon muhallinsu da ke cikin gidan Marigayi mai carbi. Hajiya Fauziyya ban da cika da batse babu abin da take yi, duk yanda ta kai ga biye-biyen malamanta akan komensu gidan abin ya faskara, sai dai ta ci alwashin sai ta gasawa Yaya babba aya a hannu cikin kisan mummuƙe ta yanda babu wanda zai gano ta. Hajiya Rahama dama macece mai sauƙin kai, tuni suka shirya da mijinta ta fauwalawa Allah lamuranta tare da neman alkairin komawar tasu. Sauran surukan cikin gidan murna a wurin abin baya musaltuwa saɓanin ƴaƴan Baba Abubakar da Baba Adamu da suke jin su kamar waɗanda suka koma rayuwar ƙunci. Yaya babba bakinta har kunne har wani annushuwa take ji da farinciki ganin kan zuri'ar Mai carbi ta haɗu wuri ɗaya.

Wannan kenan!

Aseem ya shiga cikin matsananciyar damuwa, har wata ƴar rama ya yi sai dogon wuya, fuskarsa ta yi fayau. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci rashin kwanciyar hankali ya samu matsuguni a jikinsa. Ko sati ba a rufa ba aka yi masa canjin aiki shi da Nasir, Nasir aka kai shi Kaduna shi kuma Aseem a ka kai shi garin Kano. Abin da ya daɗe yana so ne ya samu amma kuma wannan canjin aiki ya zo masa lokacin da baya buƙatar zamansa a kusa da gida. Amma babu yanda ya iya haka suka haɗa kayansa kowa ya koma wurin da aka yi posting ɗinsa.

Hajiya Nafisa tun da ta koma gida ta sanarwa da Mahaifiyarta abin da yake faruwa, da farko mahaifiyarta ta ji zafin Baba Abubakar amma daga baya ta riƙa nunawa ƴarta kuskurenta amma da yake idonta ya rufe, sai dai ta bi da Mahaifiyarta ta yanda take yi mata faɗa. Ƙanin mahaifiyarta Malam Mudam ne ya je gidan ake sanar masa da abin da ya faru, shi kansa ya ji haushin abin da ya faru don haka ya dubi Hajiya Nafisa ya ce, "Ke Nafisa saki nawa ya yi miki? Idan da kome zan nemi Abubakar ɗin mu yi magana. Ita rayuwa ai ƴar haƙuri ce, tun da ƙuruciya ba a yi wannan shashancin ba sai yanzu da girma ya zo." Hajiya Nafisa ta ɓata fuska ta ce, "Kawu ka barshi kawai ai sai ya ga kamar gajiya na yi da zaman nan ɗin." Daƙuwa ya yi mata da hannu ya ce, "Wannan sakarcin banza ne ai, duk abinki ke da Abubakar kun zama ɗaya." Hajiya Nafisa ta ce, "Ai ni tun da na sa takardar da ya bani a jaka ban ƙara bi ta kanta ba, tun da haka ya ga ya fi ai shi kenan." Ba don ta so ba haka ƙanin mahaifiyar tata ya tilas mata ɗauko takardar, tana  buɗewa kunyar duniya ta isheta. Babbar takarda ce sai kuma ƙanana guda biyu da basu kai ta farkon girma ba, sai kuma cheque ɗin kuɗi a tsakiya. Takardar farko rubutu ya yi mata kamar haka:

"A kodayaushe ina gaya miki girma ya riga da ya kama mu, tsayawa kace-nace bai da amfani. A lokuta da dama abin da muke ƙi shi ne mafi alheri a gare mu, don haka Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Kada a tsananta soyayya kuma kada a tsananta ƙiyayya." Bakin uwa na da matuƙar tasiri akan ƴaƴanta don haka ki yi wa Aseem fatan alheri, shi ne abin da ya fi alheri. Ni Abubakar ina ƙaunarki fiye da tunanin mai tunani, don haka idan na sake jin kalmar rabuwa a bakinki sai na hukuntaki da hukunci mai tsanani." Takarda ta biyu kuma gabaɗaya kalaman soyayya ne dattijon mijin nata ya cika mata da su, sai cheque ɗin kuɗi masu yawa da ya bata ya ce ta riƙe saboda sha'anin biki.

Lokacin da ta karanta wata irin soyayyar mijinta ta ji na ratsata, nan take ta sanarwa da Kawunta abin da yake faruwa. A take a wurin ya ɗaga waya ya kira Baba Abubakar ya sanar masa da abin da Hajiya Nafisa ta yi tare da sheda masa ya zo ya ɗauki matarsa a ranar nan take.

Bayan tariyarsu da kwana biyu Yaya Babba ta nemi ganin iyalan gidan gabaɗaya a sashenta ita da Inna Furai, kusan gabaɗaya iyalan gidan sun hallara, sai ƴan tsirarun da suke aiki a nesa da gida irinsu Aseem, da waɗanda suke fita fatauci garuruwa. A ƙalla iyalan da suke zaune a tsakar gudan sun haurewa mutum tamanin, kowanne yana zaune da matansa da ƴaƴansa sai Yaya babba da Inna furai da suke zaune akan wani dogon benci. Sanye suke da tamfarsu iri ɗaya tare da hijabinsu ruwan toka iri ɗaya kamar yanda suka suba tun farkon rayuwarsu a gidan marigayi.

Bayan buɗe taro da addu'a Inna furai ta fara da cewa, "Da farko za mu ce Allah ya jiƙan malam ya haskaka kabarinsa." Yaya babba ta saci kallonta a ɗan ƙufule don bata so ta yi mata katsalandam ba, gabaɗaya mutanen wurin suka amsa da, "Amin ya rabbi." Inna Furai da bata lura da irin kallon da Yaya babba take yi mata ba ta ci gaba da cewa, "Mun tara ku ne domin mu ƙara jan kunnenku domin gabaɗayanku babu yara a ciki, don haka babu wanda zai kawo mana zazzagar rashin ɗa'a a wurin nan."

Dubu da ke gefe ta yi karaf ta ce, "Inna yanzu Ma'azu da ake yi wa shayi shi ma ba yaro bane? Kin ga su Iro fa." Ta ƙarasa maganar tana nuna Iro  da yake kan cinyar mahaifiyarsa yana shan mama. Ai kuwa kamar mai jira Hajiya Nafisa ta ce, "To zaƙin zaƙafere... Ke kaɗai ce mai bakin magana manya na magana za ki sa baki saboda rashin ɗa'a." Baba Abubakar ya ɗago ya kalli Hajiya Nafisa amma sai ta kalli wani wurin daban don ta san haka za ta iya faruwa. Dubu ta watsawa Hajiya Nafisa harara tana mata fari haɗe da murguɗa baki, Hajiya Nafisa ta cije baki cike da takaici. Dama a ƙule take saboda kiran da Yaya babba ta yi mata ba don san ranta ta je shi ba saboda ko kaɗan ba ta san haɗa inuwa da sauran facalolinta don gani take ba ƙaramin zubewar mutumci ba ne a wurinta. Matan Baba Abubakar ma don ta san babu abin da nata mijin ya fi na su shi ya sa bata cika kawo musu wargi ba.

Baba Abubakar ne ya yi magana hayaniyar da ke tashi ƙasa-ƙasa a wurin ta lafa, amma kallon yanda Hajiya Nafisa take duban Dubu za ka tabbatar da babu ɗigon ƙaunar sirukar tata a zuciyarta.

Inna Furai cike da ƙwarin gwiwa ta ci gaba da cewa, "Fatan mu dai ku zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Allah ya sani bama son tashin hankali da gutsiri-tsoma, gabaɗaya tushe ɗaya kuke sai a ɗorar da zazzagar zaman lafiya. Amma duk wacce ta kawo mana wargi alƙur'an mai hana mu zazzage albarkar da ke kanta sai Allah ko ba haka ba Yaya." Yaya babba murya can cikin ƙasan maƙoshi ta ce, "Wacce falsafa za ki tambaye ni Furaira? Meye nawa a ciki kuma bayan tun farko baki bani girma da darajata ba. Ƙwarakwatsa dubu ba don kar na baki kunya a gaban su Auwalu da Ado ba, babu abin da zai hana watsa miki falsafar rashin ɗa'a." Yaya babba muryarta ta fara rawa alamar za ta yi kuka, ta dubi Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Alƙur'an ban taɓa sanin za ki yi ɗiban karen mahaukaciya da wasiyyar Malam ba. kaico! Rayuwar duniya." Inna Furai ta fara zuwa wuya don haka a ɗan hassale ta ce:

"Yanzu me ye ma ba ki yi mini ba, wacce irin albarka ce baki zazzage mini a tsakar ka ba." Sai kuma ta juya musu baya tana faɗin, "Allah ya sani Yaya kin zazzage mini kwandon ɗiban albarka." Yaya babba ta taɓe baki ta ce, "Ai kinsan dai ni ce babba a gidan, tun zuwanki gidan nan ni nake fara komai, amma ƙasa ta rufe idon Malam har kina neman kwara mini falsafar rashin mutumci." Inna Furai ta kusa kaiwa bango, a fusace ta miƙe za ta bar wurin tuni su Baba Munkaila suka fara sa baki ta zauna.

Inna Furai ta harari gefen Yaya babba ta ce, "Dama duk daɗinka da kishiya sai ta yi maka zazzagar rashin mutumci. To ni dai nan gani nan bari, kujera ce dola a zauna a kaina."

Wannan maganar ba ƙaramin ɓata ran Yaya babba ya yi, ai kuwa nan take ta fashe da kuka. Wurin shiru ya ɗauka ban da sautin kukan Yaya babba babu abin da yake tashi, Inna fura ta ɗauke kai gefe alamun ita ko a jikinta. Sai da Yaya babba ta yi mai isarta sannan ta fara leƙe-leƙe, daga can gefe ta hango Salisu, da ɗan yatsa ta nuna shi tana faɗin, "Salisu zo nan don girman Allah." Salisu na jin haka ya fara noƙewa don fatansa bai wuce, Yaya babba karta kunyata shi a gaban iyaye da sirikansa ba. Jin ya yi shiru ya sa Baba Sule ya yi masa magana jiki ba ƙwari ya fita ya je gefen Yaya babba ya russuna ya ce,

"Gani Inno."

Yaya babba ta ruƙo hannuna Salisu tana goge hawaye idonta, ta ce, "Allah shaida kaine shaidata Salisu, daga yau babu ni babu Furaira ko a lahira idan ta nuna ta sanni ban yafe ba." Tana rufe baki mutane wurin kamar haɗin baki suka ɗauki salati lokaci ɗaya. Yaya babba ta hango Sha'aban Jikan Inna Furai na huɗu shi ma ta ƙwala masa kira, yana zuwa ta riƙe hannunsa ta ci gaba da cewa, "Sha'aban na fasa wakilta Salisu saboda sam bai da ɗa'a bashi da kunya,  Kaine shaida ko a gaban Ubangiji ka za ka shede ni." Salisu zuciyarsa fes har zai bar wurin Yaya babba ta fisgo ƙugunsa ta tana faɗin, "Dawo munafuki babu in da za ka dama da biyu na shirya zaman nan, saboda kai da yarinyar nan Zulfa. Amma dai Allah ya yi wa Soja albarka, yaron nan shi kaɗai yake da kawaici." Yaya babba ta mayar da kallonta wurin mutanen da ke zaune kowa ya zuba idanu suna jiran abin da za ta faɗa.

"Munkaila!" Ta ambaci sunan Baba Munkaila a hankali ya amsa don yana gudun kar a kwatanta ta kwanaki. Yaya babba ta ci gaba da cewa, "Kwarankwatsa dubu ka shawarta da ƴan uwa wallahi auren nan janyo shi za a yi; ku rufa mini asiri ku aurar da yaran nan na daina jin miyagun maganganun da kunnena suke ji, wai ma saura kwana nawa?" Baba Munkaila ya haɗiyi yawo cike da fargaba don har zuwa lokacin bai gama haɗa kuɗin kayan gadon Zulfa ba, shi kuma baya jin zai iya taɓa kiwonsa ko kaza ce ya sayar. A hankali ya ce, "Yau saura kwana goma sha takwas."

"To a rage kwanakin nan gaskiya, don na gaji da jin falsafar rashin ɗa'a a kunnena. Ina dalili ina zaune ƙalau a janyo mana fushin mala'iku har cikin gida. A'a don Allah ka rabani da faɗawa halaka, me ye haɗina da Jahannama ana zaune ƙalau? A'a wallahi ina daga sahun farkon masoyiya Manzon Allah (S.A.W)" Kowa dai ya yi shiru cikin zuƙutansu da irin wasiƙar da suke karantawa.

Yaya Babba bata damu ba ta ci gaba da cewa, "Ku gane mini shi don Allah wa zai ce Salisu halin yahudu gare shi? Maganganun da ya faɗa rannan a ɗakina alƙur'an da ƙyar bacci ya ɗauke ni." Baƙin cikin duniya ya cika Salisu, ban da harare-harare babu abin da yake yi.

"Wai har da I musu yu, don Allah ku ji kalmar arnanci kamar me kiran muzuru, ni Soja nake yi wa kallon ɓatacce mai halin Yahudawa ashe ina tare da shi a kusa ban sani ba" Hajiya Nafisa ta cika fam wannan kalmar na ƙona ranta idan ta ji Yaya babba na danganta jininta da yahudawa.

Cike da takaici Inna Furai ta juyo ta ce, "Yaya raba kanki da aibanta mini jika idan ba haka ba alƙur'an babu mai hanani zazzage miki albarka a ka." Yaya baba ta sakar mata harar mai ɗauke da manufar, ai ba ke kika haifar mini mahaifinsa ba. Sannan ta ɗora da cewa, "Furai wa ya haifar mini Uban Salisu a gidan nan?"

Inna Furai ta taɓe baki ta ce, "Yoo don kin haifi ubansa ni da Malam ya yi mini kyautar ubansa tun yana tsammafa." Yaya babba ta saki dariyar ta ce, "Yoo wa yake bin wasiyyar matacce, Malam dai ya mutu Allah ya jiƙansa amma ba wanda ya isa ya yi mini iko da jinina."

Inna Furai ta ɓata fuska har da huccinta, ta kalli Auwalu ta ce, "Auwalu Allah idan baka rakani ofishin human rai (Human right) ba kwarankwatsa mai hanani zazzagewa gidan nan albarka sai Allah. Allah ko ka rakani a bi mini haƙƙina ko ku neme ni ku rasa daga nan nida Indo shari'a har ƙashen duniya." A tsorace Yaya babba ta dafe ƙirji ta ce, "Furai yau ni kike ambata da Indo gatsal? Wallahi magana dai na yi kai Sha'aban ga ƙarin wata shaidar, kwarankwatsa dubu ko a lahira ka shaida abin da Furai ta yu mini, yoo ƙarya na yi masa ba da kunnena na ji watsewar kalaman yahudawa ba wai I musu yu (I miss you), abin da ko a mafarki ban taɓa ji Soja na faɗa ba dukda shi ma ina kokwanto akan tauhidinsa, yo me ake da aikin Soja na aikin kafirai masu busasshiyar zuciya. Allah ya sani Garba ka cuceni da ka sa mini Jika a harkar ɓata don..."

Sallamar Aseem ce ta katse Yaya babba daga jawabin da take yi.

Zuwansa kenan daga garin Lagos, ya shiga cikin gidan ya ga duk babu kowa don haka ya yanke shawara zuwa sashen su Yaya babba. Yaya babbb na ganinsa ta fashe da dariya tana faɗin, "Kun ga Ɗan'halak. Soja zo nan." Da mamaki ya fara bin mutanen wurin, yana mamakin abin da ya kawo su suka tattaru wuri ɗaya. Bai ankara ba ya ji muryar Yaya babba raɗau a kunnensa tana ci gaba da cewa.

"Soja ka dubi Allah da Annabi, ka san dai Sule bashi da wuta da aljanna bare idan ya ji ka faɗi gaskiya a kan Ɗansa Salisu ya babbakeka. Ka gaya mini meye I musu yu? Don wallahi ba zan juri zama cikin fushin Ubangiji ba?"

Shafi na biyun ƙarshe🤸🏻‍♀️💃🏼  daga shafin gobe an gama free pages ku yi hanzari ku fara biya kar a yi babu ku💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

LAST FREE PAGES 13

       Guntun tsaki Aseem ya ja ba tare da kowa ya fahimce shi ba, yana daga wurin da yake ya ce, "Inno lafiya kuwa na ga mutanen gidan sun taru?" Ya yi maganar fuska a tamke don ba ya son ta sake jefa masa wata maganar, saboda gabaɗaya ransa a dagule yake. Bai rufe baki ba idanun mutanen wurin suka sauka a kansa, yadda ka san sun ga sabuwar hallita haka suka zura masa idanu. Dubu kuwa sai kallonsa take tana yashe baki, musamman da ta tuna irin huɗubar da Yaya babba ta yi mata akan kissa da kisisina, wai murmushi ma yana daga cikin abin da yake sace zuciyar namiji.  Don haka Dubu ta zage ta riƙa yashe haƙora tana kallon saitin wurin da Aseem yake, har sake miƙa wuya gaba take don ya fi hangota a kan sauran mutanen wurin.

Yaya Babba na jin kalaman Aseem ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Tsiya ta da kai kenan Soja. Don Allah ka ƙaraso ka taya ni jin wannan lamarin ko so kake na ji ni kaɗai?" A hankali ya fara takawa yana saƙale da jakar goyonsa wacce kayan aikinsa suke ciki, sai kuma trollybag wacce ke ɗauke da sauran kayansa suke ciki. Ƙirjin Hafsa ban da lugude babu  abin da yake yi, tana jin zuciyarta na wani iri kamar za ta faso ƙirjinta. Soyayyar Aseem na ci gaba da mamaye zuciyarta, a fakaice ta sunkuyar da kai ƙasa ta sharce hawaye ba tare da ta bari wani ya lura ba.

Aseem na ƙarasawa shi ma Yaya babba riƙo hannunsa tana faɗin, "Soja wai saura kwana nawa aurenku don Allah?" Nan take fuskar Aseem ta sake haɗewa ya ɗauke kai gefe ya ce, "Na manta." Ta yashe baki tana kallon mutanen wurin ta ce, "Kun ji abin da nake faɗa, alƙur'an  Soja da ba kallon da bana yi maka don Allah ka gafarceni. Allah ya sani ko Garba ba zai nuna maka kunya ba, don shi ma da kake ganinsa a lokacin samartaka ƴanmatan da ya yi Allah ne kaɗai masani. Allah mai sarauta irin soyayya da Garba ya yi da Kandala da gidan nan na magana da ya shede ni, bana buƙatar shedar Furaira don ko a lahira na yanke zumunci da ita."

Aseem bakinsa sai motsi yake yana san ya yi magana amma yana gudun ta fito mara daɗi, yana shirin cire hannunsa daga jikin nata ya ji Inna Furai ta ce,

"Me ye naki na ambatar sunana kuma? Wallahi ko a aljannah sai na zazzage miki albarka a tsakar ka." Yaya babba bata bi  ta kan Inna Furai ba ta ci gaba da cewa, "Amma dai har Garba ya auri uwarka wallahi ban taɓa jin kalmar Allah wadai a bakinsa ba, gaskiya ba da ni ba wannan falsafar dole a dakatar da ita, maganar gaskiya Shehu auren nan ranar juma'a mai zuwa za a ɗaura shi. A kai yaran nan ko ma huta; ina dalili laifinsu ya shafe mu, mu riƙa sallah ba a karɓa Mala'iku su yi fushi da mu." Ta ƙarasa maganar tana kallon wurin Baba Shehu.

Baba Shehu ya kwantar da murya ya fara cewa, "Inno da za a taimaka a bari lokacin nan ya zo, mun riga da mun buga katin gayyata duk mun aikawa mutane idan wani abin yaran nan suka yi bayan taro ya watse sai mu zauna a tattauna." Yaya Babba ta ƙura masa ido har ya gama sannan ta ce, "Dole ka nuna mini iyakata Shehu, ba sai ka faɗa ba dama ai ba ni na haifa muku su ba." Yaya babba ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka.

Wurin shiru ya ɗauka aka rasa mai bakin magana, Baba Aminu ya ɗago ya dubi mutanen wurin ya sallame su. Ɗaya bayan ɗaya haka suka fara wucewa suna barin wurin, dama Aseem da Salisu kamar a kan ƙaya suke tun Baba Aminu bai rufe baki ba suka wuce gaba.

Shiru wurin ya yi daga Yaya babba sai Inna Furai da sauran iyaye maza kowa yanayinsa ba daɗi. Baba Abubakar ya ƙarasa wurin  Yaya babba ya ciro hankicif ɗinsa ya miƙa mata ya ce,

"Inno share hawayenki."

Yaya babba bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, "Ka barni ya yi ta zuba idan ya ƙare na mutu kun huta ai." Murmushi suka yi don ta so basu dariya, ya juya wurin Inna Furai ya ce, "Inna don Allah ki sa baki ta tsaya mu yi magana." Inna Furai ta ɗauke gefe tana wurga masa harara ta ce,

"Wacce zazzagar kuke so na yi? Maganar gaskiya abin da Yaya ta faɗa yana hanya, wai me ye a ciki lamarin nan fa na gida ne kuma auren nan ko yau aka ɗaura shi akwai wanda zai ce don me?" Baba Abubakar ya yi shiru don ya lura gabaɗaya a rikice suke, Inna Furai ta ci gaba da cewa, "Ba zan hana Yaya ba saboda Allah ina dalili ana nuna muku Annabi kuna runtse ido." Yaya babba na jin haka ta sake rushewa da kuka. Sai da ta yi mai isarta ta miƙe za ta bar wurin, da sauri suka dakatar da ita sai da ƙyar suka shawo kan Yaya babba ta zauna. Amma duk yadda suka so a bar biki a lokacin da yake fir ita da Inna Furai suka ƙi amincewa. Babu yadda suka iya haka suka amince akan ɗaurin auren ranar juma'a mai zuwa wanda a lokacin gabaɗaya saura kwanan huɗu.

Tun a ranar su Baba Abubakar suka riƙa kiran mutane suna sanar da su janyo lokacin bikin, haka a cikin garin Ɗangwauro kafin wani lokaci tuni labarin ya karɗe ko'ina. Baƙin ciki a wurin Hajiya Nafisa har ya ƙi musaltuwa don ranar kwana suka yi suna yin babu daɗi ita da Maigidanta. Haka daga wurin Aseem ranar kusan kwana ya yi cikin takaici, amma Dubu ko a jikinta baccinta ta yi hankali kwance. Hafsa ma kusan kwana ta yi tana kuka don gani take lokaci ne ya yi da za ta rasa masoyinta ba tare da cikon muradinta ba.

Gari na wayewa Aseem ya fice daga gidan yana fita ya kira wayar Nasir ya sanar da shi, nan dai Nasir ya jajanta masa daga baya kuma ya tambaye shi ko akwai wani party da za su yi. Aseem na jin haka ya katse wayar, Nasir ya yi ta kiransa amma fir ya ƙi ɗauka.

  Shirye-shirye gabaɗaya sun gama nisa a cikin gidan, daga ɓangaren Mazan har matan. Da yake duk lamarin na cikin gida ne rana ɗaya aka kai lefen su Dubu wanda a lokacin bikin saura kwana biyu. Inna Furai da Yaya babba bilhaƙƙi suka dage da gyaran amare su ne jiƙa wannan, dafa wannan duk a basu. Sai kuma gyaran jiki da Hadiza take zuwa tana yi musu, Dubu ta yi kyau sosai hasken fatarta ya sake fitowa. Sai dai gashi shi ne ya yi mata cikas. Donma tana da kufan gashi kan ya yi dubu sumar ta fara fitowa, sai dai daga baya idan ka hangota sai ka rantse da Allah namiji ne. Duk wani abin buƙata da mace take yi na Party da wasu harkokin Baba Abubakar ne ya bawa Dubu, wannan dalilin ne ya sa ko kaɗan Dubu bata wani damu da rashin ganin Aseem ba. Ita kuwa Yaya babba da yake mutane sun fara cika gidan sabga ta sha kanta ya sa bata bi ta kansu ba.

Mutane sai mamaki suke da akan auren Dubu kasancewar duk sai daga baya aka ji zancen haɗin nata auren da Aseem, nan dai aka ci gaba da shagali. Aseem kuwa  daga Nasir babu wanda ya sanarwa a cikin abokansu, don gani yake ci baya ne ace an yi masa aure da yarinya kamar Dubu.

RANA BA TA ƘARYA...

   Kimanin ƙarfe biyu na ranar Juma'a aka ɗaura auren jikokin marigayi Mai carbi, ciki kuwa har Dubu da Aseem a babban masallacin gidan Sarki da ke cikin garin jihar Kanon Dabo. Mutane masu tarin yarawa ne suka shaida wannan ɗaurin auren, fuskar su Salisu abin ba a magana saboda farinciki. Shi kuwa Aseem ban da cin ɗaci babu abin da yake yi, daga Nasir sai abokansu da basu kai goma ba. Suma duk Nasir ne ya sanar musu lokacin da Aseem ya ji labari kiran Nasir ya yi, yai masa fata-fata har sai da suka yi faɗa a wurin. Daga wurin ɗaurin aure suka ɗungumo zuwa gida.

Daga can gida mata ne suke ta shagali, an kira masu kiɗan ƙwarya sai cashewa ake. Idan ka ga yadda Dubu take cashewa sai ka ɗauka ita ma ƴar taron biki ce ba amarya ba, su Yaya babba da Inna Furai an sha atamfa mai kyau sun yi anko sai fama ake da jama'a. Bayan angwaye sun dawo gida nan fa aka shiga hotuna angwayen da iyayensu fuskarsu fal farinciki. Abin da ya hana Aseem tafiya sashensu don kar ya kunyata Mahaifinsa, saboda ya san matuƙar ba a gan shi ba an riƙa tambayarsa kenan, don haka ya daure aka yi ta ɗaukan hotuna sai daga baya ya zame jikinsa ya wuce can sashensa shi da su Nasir.

Da daddare.

     Gabaɗaya angwaye da amaren aka haɗa a babban falon Yaya Babba, haɗe da iyayensu maza da mata, Sai Yaya babba da Inna Furai. Tun da magriba da doso Yaya babba take sharar ƙwalla, lokacin da aka tattaru a ɗakin duka amaren kansu na cikin mayafi a lulluɓe da alama kuka suke wanda bai kai har zuci ba. Wasu daga cikinsu ma babu ko ɗugon hawaye, Angwayen kuwa sai sunne kai ƙasa suke yi saboda wani irin nauyin Iyayen nasu da suke ji. Dubu da ke cikin mayafi a lulluɓe ban da satar kallon mutanen ɗakin babbu abin take yi, da ta gaji da kallonsu ta cikin mayafi sai ta riƙa ɗaga mayafin tana fakar idonsu tana leƙe, da sun haɗa ido da ɗaya daga cikin kawunnan nata sai ta maza ta sauke mayafinta.

Baba Mumkaila ne ya yi gyara murya haɗe da addu'a sannan ya ɗora da nasiha, daga ƙarshe ya buƙaci su Yaya babba da su yi wa amare d angwaye nasihar zaman aure.

Yaya babba har lokacin ban da kuka babu abin da take yi, ganin haka ya sa Baba Abubakar ya ce Inna Furai ta wakilci Yaya babba. Inna Furai ta rangwaɗa kai gefe sannan ta ce, "Garba ban ƙi ta taka ba amma ka san dai bin na gaba bin Allah? Tun da kuka taso a cikin gidan nan kun taɓa ganin na shige gaba a abu ba tare da Yaya ta fara yi ba." Yaya babba ta sharce hawaye ta ce, "Bar shi Furaira so yake ki kaucewa tarbiyyar Malam. To gaskiya ba haka mu ke ba, kar dai ka yi wani mugun halin a gaban yaran nan su ɗauka suma su idar a gidajen aurensu. Shi ya sa mu ke aikata alheri ni da ƴar uwata, don mu samu rabo da gidan Aljannah." Yaya babba ta ƙarasa maganar tana kallon Inna Furai. Baba Sule ya gyaɗa kai sannan ya ce, "To Inno bismillah!" Yaya babba ta gyara zama tana cewa:

"Ku ba ni hankulanku wuri ɗaya domin zaman aure ba wasa ba, ku dubi iyayenku kamar yau aka kawo mana su ɗakin nan ga shi yau sun aurar da ku. Zan fara da ku matan alƙur'an ku ji tsoron Allah ku yi wa mazajenku biyayya, idan ba haka ba har abada babu ni babu ku. Ga Furaira ita ce sheda ko a lahira kar wanda ya nuna ya sanni, tun da duk wacce bata bi aure ba kwarankwatsa dubu makomarta wuta. A'a ku raba ni da zan cen jahannama a na zaune ƙalau, meye haɗina da ita bayan ina sahun masoya Annabi (S.A.W). Ku yi biyayyar aure ku samu Aljannah mu haɗu da ku a zangon barka-barka a cikin Aljannah. Idan na hango Zulfa na ɗaga mata hannu sai na hango Dubu musha alkausara, mu ci abin da muke so mu sha abin da muke so. Yoo zaman duniyar nawa yake a kan idonku dai Munkaila yake gadinmu ni da Furaira, don masifa naman ma suna hanamu ci ina dalili. A'a rabani da wannan mugun halin ku yi biyayyar aure mu ci nama mu ci ƴan shiloli tare ba wanda zai mana iyaka, idan kun ƙi kum a kaiku Jahannama a haɗa ku da Mala'iku su yi muku walmukalifatu." Mutanan ɗakin ne suka sa dariya don yadda Yaya babba take haƙiƙancewa a zancen aljannah sai ka rantse da Allah tuni an yi mata bushara da tata aljannar tun a duniya. Ta juya wurin angwayen suma ta ƙare musu kallo ta saki murmushi tana faɗin:

"Allah mai iko ku dubi su Soja fuska sai walƙiya take, don Allah ban da aure wa zai yi maka haka? To ku saurareni da kyau don har ga Allah ba zan lamunci baku jikokina ku riƙa gasa musu aya a hannu ba, a'a raba ni da wannan falsafar. Yara dai amana muka basu ku kyautata musu da ma zaman aure sai haƙuri, iyayenku ma duk da haka suka kawo nan. Ga dai Ado nan ga sauran iyayenku tun da nake da su ban taɓa jin wata falsafar tashin hankalin ta ɓullo daga wurinsu da matansu ba. A cikinsu duk wacce ta ɓata muku rai ku zo ku same ni ku gaya min ranar mai cetonta a hannuna sai Allah, ku riƙa kula da su ɗan tsiren nan da ƴan kajin nan kun san  suma suna ƙara danƙon ƙauna. Allah dai ya ƙara yalwata kaji a faɗin duniya ba don su ba da tuni ba a haife ka ba Salisu, ga Uwarka nan ba zan mata ƙarya ba, lokacin da aka aurota alƙur'an bata ƙaunar Ubanka. Amma da yake Ubanka ma'abocin siyan kaji ne sai wayar gari na yi na ga uwarka da ciki, don Allah ka gaya min idan kaji suka yi ƙaranci ya ya gidan aure zai yi." Ɗakin dai kowa ya yi shiru ba su tanka ba. Yaya babba ta yi ƙasa da murya ta ci gaba da cewa:

"Kun san dai sha'anin tsoho sai haƙuri, ni dai tun da nake baku taɓa yi mini komai ba amma ni dai ku gafarce ni idan na ɓata muku rai, yanzu Furaira ta ci gaba da nasihar."

Amsa mata suka yi sannan Inno ta ci gaba da jawabi. "Ni dai ƴar taƙaitacciyar nasiha gare ni. Gabaɗaya zan ce su ji tsoron Allah idan ba haka babu abin da zai hana mu zazzage musu albarka a tsakiyar ka. Ku matan yi na yi bari na bari sai kwalliya kissa da kisisina kamar yadda muka koya muku, Allah ya sani idan kuka saɓawa Allah babu sa hannunmu a ciki. Ku kuma mazan ku ne jagorori idan laifi suka yi banda duka ko zagi, don Allah ya sani ba za mu juri haka ba duk wanda ya taɓa mana jika alƙur'an mai hana mu maka shi wurin human rai (Human right) sai dai idan bama numfashi. Da haka nake yi musu fatan alheri."
 
Daga haka iyayensu maza suka yi musu nasiha sannan Baba Adamu ya sa aka shigowa da kowanne ango ledar kajinsa da ledar drinks haka ya basu gabaɗaya. Daga nan suka fice sannan aka ɗauki amare aka kai su ɗakin mazajensu. Dubu sai da aka zo tafiya da ita ta sa kuka wai dole su tafi da Yaya babba, wannan kalamai na Dubu ya sake karya zuciyar Yaya babba da ƙyar aka lallaɓa Yaya babba ta yi shiru aka wuce da Dubu ɗakin mijinta Aseem.

   Ɗakin Dubu ya yi kyau sosai Baba Abubakar shi ya yi mata kayan ɗaki irin na ƴan birni, kayanta ba a yi ƙarya ba daidai rayuwar rufin asiri. Ɗan gidan gwanin birgewa komai sabo sai ƙamshi yake, Dubu aka kai aka ƙara yi mata nasiha sannan suka fito aka bar daga Dubu sai ƙawayenta biyu A'ilo da Raliya. Su Nasir sune kan gaba wurin rako ango, Aseem na gaba Nasir da abokansu biyu na rufa masu baya. Suna shiga Dubu ta ɗago kai ta mayafi tana satar kallonsu, tana ganin sun haɗa ido da Aseem ta mayar da kai cikin mayafi tana ƙyalƙyalewa da dariya. Nasir na zuwa ya ce, "Amaryarmu ga ango mun kawo miki da fatan za ki riƙe mana shi amana, don so muke nan da rana iya yau mu ga wannan ramin wuyan nasa ya shige." Aseem ya watsa masa kallo ya ce, "Nasir ranka zai ɓaci." Bai rufe baki ba ya ji Dubu ta ce, "Ai wallahi ko sati ba za a rufa ba sai kun yi mamakinsa, don baka san Laminu mijin ƙawata Zuwai ba yadda ka ga Me lob (My love) haka yake amma yanzu ko tunbinsa aka ɗora ma ka ji..."

Tsawar da Aseem ya buga mata ne ya sa sauran maganarta maƙalewa, ya dubi Nasir fuska ba walwala ya ce, "Bar min gida dama ban gayyace ku ba." Nasir na dariyar ƙeta ya ce.

"Ɗan iska ba sai ka nuna min ba matsayinmu ɗaya ba, ni ma kwanannan zan yi wuff da wata ka ga mun yi one-one." Ya ƙrasa maganar yana dire ledar da suka yi wa Aseem siyayya na shiga ɗakin Amarya, suna fita ya kalli su A'ilo da suka yi zuru-zuru ya buga musu tsawa, tun bai rufe baki ba suka miƙe suka fita, sai da suka yi gware ya kai sau biyu sannan suka samu ƙofa suka fice da gudu.

Suna fita Dubu ta fige mayafinta haɗe da ɓata rai ta ce, "Wallahi ka kunyata ni akan me za ka korar mun ƙawaye ko ladan siyan baki ba a ba su ba..." Ba ta ƙarasa magana ba ya bige mata baki ba shiri ta ja baki ta yi shiru.

Drower ya buɗe ya ciro sabuwar doguwar rigarsa ya fita falo sannan ya faɗa toilet ɗin tsakar gida. Yana fita Dubu ta yi maza ta buɗe akwati ta sauya kaya cikin doguwar rigar bacci, kannan nata ranƙwal babu gashi a kai kuma babu abin da ta sa a kan. Ledar kazar ta fizgo ta buɗe ta fara ci tana shan youghort ban da lumshe ido babu abin da take yi. Tana nan zaune Aseem ya shigo ya same ta, ba ƙaramin mamaki ta bashi ba binta yake da kallo yana ƙarewa kayan jikinta kallo, mamakinsa ɗaya yadda Dubu take da wayewar ido wai har ta san ta sa wasu kayan bacci, zama ya yi a bakin gado yana watsa mata kallo cike da takaici.

Bai tsinke da lamarin Dubu ba sai gani ya yi ta turo masa cinyar kaza saitin bakinsa ta ce, "Me lob kazar masoya." Ta ƙarasa maganar tana wani irin farfari da ido. Rasa abin yi ya yi yana juyawa ya fisgo wayar cazarsa da ya ajiye akan gado, Dubu na ganin haka ta yi tsalle ta fice daga ɗakin tana ihu, Aseem ya rufa mata baya ba su tsaya a ko'ina ba sai ɗakin Yaya babba.

Da gudu Dubu ta kwakume Yaya babba hannunta ɗaya ɗauke da kaza bakinta shane-shane da mai.

Yaya Babba ta rungume Dubu ta dubi Aseem tana faɗin, "Kayya Soja kai a komai sai ka nuna halin yahudawa da rashin imani. Dubu fa ƙaramar yarinya ce, a'a rabani da wannan falsafar yarinya ko kaza bata gama cinyewa ba kake niyyar afka mata."

ME KUKE TUNANI ZAI KASANCE? YAYA ZA A BUGA RAYUWA TSAKANIN SOJA DA DUBU?😂  WAI SHIN TA DAINA SHAƘIYANCINTA BAYAN AUREN KO KUWA SABON SHAFI ZA TA BUƊE😂😂😂😂  DON ALLAH KU HANGO MIN RAYUWAR AUREN SOJA DA DUBU MU JI YA ZATA KWASHE.

MAZA HANZARTA💃🏼  KI SIYA ƊARI BIYU BA YAWA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️  NA TABBATA BA ZA KI JI KAICO BA, KI SIYA KI SHA NISHAƊI DA BAN DARIYA🤸🏻‍♀️💃🏼💃🏼
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR

              FREE PAGE 1

Girma da nauyin cikin da ke jikinta kamar an kifa ƙwarya, bai hanata gudun da take yi na ceton rai ba. Gudu take zabgawa saboda miyagun hallitun da ta yi tozali da su, masu kawo mata farmaki da zimmar cafkar tsohon cikin da ya yi tsini tamkar zai fashe.

Zuwanta bakin wata bishiyar kuka mai duhun gaske ya bata damar tsugunnawa cikin haki, saboda ji take kamar bayanta zai ɓalle gida biyu saboda azaba, ajiyar zuciya take saukewa akai-akai kamar wacce ta shekara tana matsanancin gudu a tsakiyar rani. Dafe bayanta ta yi wani irin azabar ciwon baya da mara ya sarƙeta kamar ana tsaga marar tata da kaifaffiyar aska. Sannu a hankali ta waiga bayanta don ganin mummunar halittar da ke bibiyarta kamar yanda inuwar mutum take bibiyarsa. Kukan jarirai ne ya fara yi mata amsa kuwwa kamar saukar aradu a tsakiyar ka! Ta ko ina take jin sautin kukan na su kamar kunnuwanta za su tawatse.

Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu.

Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, "Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki." Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu!  A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata.

Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo.

   Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran 'yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da'irar ƙungiyar asiri.  Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.

    Kamar haɗin baki haka suka waiwayi wurin da take tsaye, tamkar 'ya'yan Birrai haka suka fara tsalle suna ɗane jikinta har Allah ya basu nasarar hawa jikinta. Lokaci ɗaya suka fara lasar jikinta, ihu take kurmawa kamar zautacciya amma babu ɗaya daga cikinsu da ya yi alamun dakatawa. Daga can ƙafarta ta hango Jaririn da ya fito daga jikinta yana bin jinin ƙafarta yana lasa. A haukace ta ƙwalla ƙara tana ambatar sunan Mahaifiyarta kamar wacce ake zare wa rai.

   Firgigit ta farka daga bacci tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta ci gasar tseren gudu, jikinta rawa yake kamar mazari, ta haɗa gumi sharkaf kamar wacce take gaban maƙera.

"Barka da tashi ranki shi daɗe." Ba ta yi aune ba ta ji kalaman Mama Uwani a tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago ta kalle ta har lokacin jikinta rawa yake, sai da ta jingina da bangon gadon ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Yauwa Mama Uwani."

"Kina buƙatar wani abu?"

Girgiza mata kai ta yi tana murza idanu, hamma ta yi haɗe da miƙa sannan ta dubi Mama Uwani tana faɗin, "Mama Uwani ki haɗa min Tea kafin na fito." Cike da girmamawa Mama Uwani ya russuna tana faɗin, "An gama shalelen Uwani, gabanki gata bayanki gata. Duk abin da kika faɗa haka za a yi uwar ɗakina." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Raihan miƙewa ta yi tana ɗan waƙe-waƙenta sannan ta faɗa toilet don ɗaura alwalar sallar asuba. Sai dai rana ta buɗe sosai wacce take nuni da gari ya waye tangararan don ƙarfe tara har da kwata a lokacin.

Sai dai har lokacin mafarkin da ta yi bai gama sakin jikinta, wani abin da ya bata mamaki bai wuce zuwan period ɗin ta ba alhalin ba lokacin zuwansa ba ne.

Mama Uwani tana fita bayan Raihan ta shiga toilet wata baƙar mage ce ta ratso daga bangon kusurwar ɗakin, idanunta jawur suke kamar gauta ga ƙarshen jelarta wani tafkeken kan maciji ne ban da sheƙi babu abin da yake yi. Kalle-kalle ta fara yi tana shine-shine  sannan ta fara girgiza cikin wani irin yanayi, lokaci ɗaya ta fara rikiɗa zuwa kaloli daban-daban. Sai da ta rikiɗa zuwa kaloli sama da goma sannan ta dawo kalarta ta farko, ta buga tsalle zuwa kan gadon da Raihan ta tashi wanda har ya ɗan fara ɓaci da jini. Tana hawa kai ta fara lasa sai da ta siɗe shi tas sannan ta sauko cikin takun ƙasaita tana kalle-kalle, a hankali ta taka zuwa kan mudubin Raihan da ke cike da kayan shafe-shafe da turarruka kala-kala.

Girgiza ta yi lokaci ɗaya ta rike zuwa wata mummunar hallita mai siffar dorinar ruwa da ranƙwalelen ƙaho a goshinta, a hankali ta fara zuƙe mayuka da tururrukan da ke cikin kwalabe da robobinsu, nan take komai ya zama wayam babu komai a ciki. Wani irin ruwa ta shiga ɗurawa mai yauƙi sai da ta gama cika su sannan ta hura iska suka dawo tamkar mayuka da turarrrukan da ke ciki da farko. Mama Uwani ce ta tunkaro ƙofar da sauri wannan hallitar ta sake rikiɗewa zuwa mage wannan karon jelar rabuwa ta yi gida biyu dukkansu ɗauke da kan maciji. Tana jin alamun buɗe ƙofa da sauri ta ratse ta jikin bango ta ɓace daga ɗakin, sai dai takaicinta ɗaya da bata samu ta ƙarasa cimma abin da yake tafe da ita ba.

Mama Uwani jere kayan abincin Raihan ta fara yi, a daidai lokacin Raihan ta fito ɗaure da towel. Da murmushi Mama Uwani ta riƙo hannunta tana faɗin, "Ƴar gatan Uwani me kike buƙata bayan wannan?" Ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, "Babu." Mama Uwani cikin wani yanayi ta fara bin ɗakin da kallo, Raihan ta ɗan ja guntun tsaki tana faɗin, "Mama Uwani ki bani wuri bana buƙatar hayaniya."

Mama Uwani ba don ta so ba ta juya jiki a sanyaye ta fice daga ɗakin tana waige, fitarta ke da wuya Mommy na kawo kai tana ganin Mama Uwani ta ce, "Uwani yarinyar ta tashi kuwa?" Mama Uwani cikin ladabi ta ce, "Ta tashi hajiya yanzu na kai mata abin kari." Mommy bata tanka mata ba ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, Raihan na gaban mudubi za ta fara shafa mai. Mummy ta kira sunanta tana ci gaba da cewa, "Raihan ba dai yanzu kika ta shi kika yi sallaha ba?" Raihan ta ɓata fuska ta ce, "Haba Mommy wai me kika mayar da ni, ni ba sallah ma zan yi ba period ɗina ya dawo." Fuska ɗauke da damuwa Mommy ta ce, "Period kuma, ina ce yau ko sati biyu ba ki da gamawa ba." Cikin rashin damuwa ta gyaɗa kai tana ci gaba da shafa mai, juyawa Mommy ta yi ta fi ce tana faɗin, "Gaskiya idan ya ci gaba da yi miki wasa dole mu je mu ga likita." Raihan ta tura baki gaba ƙasa-ƙasa da murya tana faɗin, "Kawai don period ɗina ya dawo sai ace sai na je wani Hospital ana zaune ƙalau." Turo ƙofar da aka yi ne ya sa Raihan waigawa a lokacin ta fesa turare tana saka wata doguwar rigar bacci, Mama Uwani ce ta sake shiga hannu ɗauke da kunun gyaɗa ta ajiye, Raihan na ganin haka ta saki murmushi mai sauti ta ce, "Mama Uwani dama kin yi kunu shi ne baki kawo min ba, ai kuwa da na cika cikina sai kin kwashe min tass kin ɗura min kunun nan."  Ta ƙarasa magana tana zame towel ɗin jikinta don ita Raihan bata kunyar ko a gaban waye ta cire kayanta ko ta sauya wasu.

Mama Uwani na ganin haka ta fice daga ɗakin, Raihan na cikin saka kaya ta ji kanta na sara mara lokaci ɗaya jini ya fara bin ƙafarta ga wani irin raɗaɗi da jikinta yake yi ta ko'ina, nan take ta yanke jiki ta faɗi a wurin. Wani irin hayaƙi ne ya fara zirarowa ta jikin ƙofa har sai da ya zo gaban Raihan da ke kwance jini ya fara malala daga jikinta, lokaci ɗaya  hayaƙin ya rikiɗa zuwa siffar mutum. Kallon kan mudubin Raihan ya yi yana girgiza kai cike da baƙin ciki, ɗaya bayan ɗaya ya fara zuƙewa mayuwan ciki da yake ganinsu da kalar ruwan nan mai yauƙi, kusurwa bangon ɗakin ya kalla ya ce, "Tabbas ba aikin kowa ba ne sai naki Mugaza, na lura kin fara wuce makaɗi da rawa amma ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Tun bai rufe baki ba magen nan ta sake ɓullowa ta bango, har sai da ta zo gabansa ta yi girgiza cikin surar wata matashiyar budurwa ta ce, "Ka ga laifina don na nakasta mai shirin tarwatsa farincikina? Ko kana tsammanin zan zura ido ka ɗauko mini kishiya alhalin ka san wannan haramtacciyar al'ada ce a zuri'armu. Wani abin takaici ma ka rasa wacce za ka aura sai bil'adam salon ka ja mini abin kunya cikin ahalina, wallahi ba zan lamunci haka ba kuma wannan somin taɓu ne ka zuba ido ka gani." Tana gama maganar ta sake rikiɗa zuwa mage ta ɓace daga ɗakin, cike da takaici ya kalli gadon Raihan sai kawai ya fara kiran sunan Hidaya. Sai da ya kira sau uku sannan wata matashiyar budurwa ta ratso ta ƙarƙashin ƙasa mai zubin siffar Raihan babu abin da ya bambamta su har kayan jikinta. Wurin abincin Raihan ya nuna mata ya ce, "Ki maye gurbinta kuma bana buƙatar a samu matsala idan ba haka ba har abada ke da biyan buƙatar ƙudurinki."

Idanunta ne suka ciko da ƙwallah ta ce, "Wuskarbat min kalsusbima wakfit karmu linkasbu muzrabatu fisgatmuha warmi Jalkisu Mu'az." (Don Allah karka yi mini haka, ka san duk duniya babu wanda nake ƙauna kamar Yarima Mu'az.)

Ɗaukan Raihan ya yi da ke kwance ya saɓa a kafaɗa sannan ya kalli jabun Raihan da ke  tsaye ya ce, "Dole ki ɗauki ɗabi'a irin ta Raihan hatta yare dole ki ci gaba da irin yarenta ba namu da muka saba yi ba. Na gaya miki idan aka samu matsala ke da Yarima Mu'az har abada." Yana gama maganar ya daki tsakar ɗakin nan take ƙasar wurin ta dare ya faɗa ciki hannunsa ɗauke da Raihan suna shigewa ƙasar wurin ta haɗe ta shafe kamar wani abu bai taɓa faruwa a wurin ba.

SHARE HILIS🌚

Daga yau za ki iya turo kuɗinki don karki bari ayi babu ke🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 2

https://chat.whatsapp.com/J0qrgC0rXNQ57u50VzeewR

        A hankali Jabun Raihan ta fara bin ɗakin da kallon, miƙewa ta yi ta fara buɗe drowers ɗin kayan Raihan sai kuma ta bi hotunan ɗakin Raihan da ke maƙale a jikin bango tana kallo ɗaya bayan ɗaya, tana jin motsi ta koma wurin kayan abincin ta zauna. Kallon abincin take don sam bai burgeta ba cikin zuciyarta take mamakin irin abincin bil'adam don ita bata ga abin daɗi a ciki ba. Goggo ce ta turo ƙofar tana faɗin, "Rehanu! Ke Rehanu wai ina kika shiga ne tun jiya ban ji wulgawarki ba, yarinya sai iya shege don kin ga na damu da ke." Turus ta yi tana kallon Jabun Raihan da ke cin abinci tana yamutsa fuska, daƙuwa ta yi mata da hannu tana faɗin, "Kin ci ƙaniyarki Rehanu dama kina jina kika yi shiru to kin wulaƙanta uwarki Abu. Meye wannan ɗin kike ci kina yamutsa fuska kamar abinci?" Jabun Raihan a daƙile ta ce, "Gashi kuwa kin gani."

Goggo ta shiga ɗakin ta yi tsaye a kan Raihan tana faɗin, "Oho dai kowa ya raina uwar wani tashi ya raina, wallahi duk maganar da kika gaya min uwarki da Ubanki kika gayawa." A fusace ta ɗago tana duban Goggo da ke tsaye tana zazzaga ruwan masifa, farantan gabanta ta kalla tana motsa baki lokaci ɗaya ta cinye abincin ciki sai kwanukan, tana kallon Goggo kamar wacce ta basu umarni sai farantan suka yi tsalle zuwa gaban Goggo, wuƙar da Mama Uwani ta haɗowa Raihan don ta riƙa yankar farfesun ƙafar sa ce ta yi tsaye a daidai fuskar Goggo saitin idonta tana wani juyi, kamar za ta tsokane mata ido. Jabun Raihan ta kalli Goggo fuska ba walwala tana cewa,  "Kika sake zagar mini iyaye sai na tsokane idonki, ke da sake gani har abada. Wannan kwanukan kuwa sai na basu umarni su yi ta ranƙwale miki kai har sai sun illataki." Goggo daskarewa ta yi a wurin, tuni fitsari ya jiƙe mata zani gumi sai yanko mata yake ta ko'ina. Tun Jabun Raihan bata gama magana ba, Goggo ta juya da gudu tana ƙawalawa Mahaifiyar Raihan kira, sai dai yadda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ya sa ta fice da rarrafe zanin jikinta kuwa tuni ya samu mutsuguni a bakin ƙofa.

Tana fita Jabun Raihan ta miƙe tana kaiwa da kawowa don gabaɗaya zaman wurin ya gundureta, abin da ya sa ta bi umarnin Huzaifa don biyan tata buƙatar amma ba don haka ba babu yadda za a yi ta amince da rayuwa cikin siffar bil'adam.

Huzaifa bai tsaya ko'ina ba sai cikin wani ƙasurgumin daji mai ɗauke da jajayen furanni, da jajayen ƙoramu. Komai na wurin ja ne hatta ciyayin da suke wurin, sai waɗansu korayen kifaye da su kaɗai ne suka bambamta da jajayen abubuwan da ke wurin. Kan wani jan dutse ya kaita ya kwantar da ita nan take ya fara gyara mata jikinta, kafin wani lokaci tuni ya gyara mata jikinta ya ɗauko wani ƙaramin jariri da ke kwance cikin wata ƙorama mai ɗauke da siffar kunkuru, sai dai kansa ɗauke yake da kawuna huɗu kowanne da surarsa. Akwai kai mai siffar jaki, agwagwa, mage da mai siffar kifi, a kowanne kai akwai manya kahunhuna guda biyu, daga jelar hallitar ɗauke take da tafkeken kan maciji. Yana zuwa ya ɗora shi a gefenta sannan ya ɗaga hannunta ya tura shi ƙarƙashin jikinta kamar yadda uwa take rungume jaririnta. Nesa da su ya koma yana sakin murmushin farinciki a fili ya fara faɗin, "Na jima ina burin haka ban samu dama ba domin gudin abin da zai ɓata miki rai, sai dai a wannan karon dole na ɗau wannan matakin domin haka ne kaɗai sai tseratar da ke daga kaidin Mugaza, idan ba haka ba duk yadda za ta yi sai ta halaka min ku. Ni kuma ba zan juri rabuwa da ke ba wanda ya nemi raba ni da ku zan iya hallaka shi ko wanene, ko da kuwa Mahaifina ne Jingas." Yana gama magana ya ɗaga dutsen da Raihan take kwance da jaririnta, naɗe su ya yi cikin wani kogon dutse sannan ya hura wani kogi da korayen kifayen nan suke ciki, nan take ruwan ya dare Huzaifa ya jefa su ciki ya sake hura ruwan ya haɗe gabaɗaya.

Mommy na daga falo ta fara jiyo muryar Goggo na ƙwala mata kira, da sauri ta nufi wurin da ta ji muryar Goggo tana zuwa ta yi turus ganin Goggo na rarrafe daga ita sai ɗan fatari. Da sauri ta sunkuya tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa ko ƙafar ce ta motsa?" Tun bata rufe baki ba Goggo ta ci gaba da faɗin, "Abu ki dubi Allah da ma'aiki ka mayar da ni Albasu wallahi na yafe zaman gidanki, ki maida ni Albasu na mutu cikin aminci tun bata tsaface ni a gidan nan ba." Goggo na maganar hawaye da majina na zuba, a gefe ɗaya fitsari ne ke zuba don Goggo ta yi fitsari daga ɗakin Raihan zuwa babban falo ya kai sau uku.

A ɗan tsorace Mommy ta waiga tana faɗin, "Goggo lafiya kuwa wace ce ta zama matsafiya?" Goggo ta fyace majina da gefen zaninta ta ce, "Wa kuwa kika sani idan ba Rehanu ba. Wallahi yadda na ga tana tsafi ido biyu na ga Annabi haka..." Tun bata ƙarasa maganar ba Mommy ta fara waige tana katseta da sauri cikin ƙasa-ƙasa da murya.

"Goggo don Allah ki daina faɗin haka wallahi Alhaji yana gida kar ya ji abin da kike faɗa, kin san fa baya kawaici a kan yarinyar nan Raihan." Tana rufe baki Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya tonu asirinku, ashe gulmar Ɗana kuke da jikalleta to ahir ɗinku wallahi ke Zinaru ki yi ta kanki arziƙi kika zo ci ba zan miki baƙin ciki ba, gida dai gidan Ɗana ne ba a isa a sawa jikata ido." Goggo takaici ya sake cikata tana ganin kamar gori Inno take yi mata, don haka a zafafe ta ce, "Allah ya sa ni na haifi Abulle har ɗan naki ya aura, magana ce na gama ta yau za a mayar da ni Albasu don wannan sheɗaniyar jikar taki ba za ta sayar da kaina ina ji ina gani ba." Inno na jin haka ta yi zaman ƴan bori daɓar sai kawai ta fashe da kuka, da sauri Mommy ta koma wurinta tana rarrashinta amma fir taƙi yin shiru. Suna nan zaune Alhaji Abdallah ya sauko cikin dakakkiyar shadda ruwan toka da hula baƙa, kayan ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Tun kafin ya ƙaraso Mommy ta fisge ɗankwalinta ta rufawa Goggo, yana ƙarasowa ya ce, "Lafiya dai Inno mai yake faruwa?" Inno na jin haka ta rushe da kuka tana faɗin, "Audullahi ka dubi irin sitirar da ka yi wa Zinaru ita da ƴarta amma da yake sun samu wuri wai cin naman ka suke da ƴarka ɗaya tilo a gidan duniya. Don Allah ko don darajar haihuwa Abulle ai da ɗagawa yarinyar nan ƙafa ina dalili tana uwarta tana cin namanta?" Goggo ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce:

"Audullahi wallahi tun wuri ka san halin da kake ciki, kwarankwatsa dubi Rehanu ta shiga ƙungiyar asiri."

Kamar wanda aka zagi iyayensa haka Alhaji ya ɓata fuska sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya ce, "Goggo kin san wa kike faɗa kuwa? Raihan ɗina ce ta shiga ƙungiyar asiri?"

"Ƙarya na yi maka kenan Audullahi?" Goggo ta tambaye shi tana ɗage kai gefe. Shiru ya yi don ya san idan ya buɗe baki a kan Raihan za a iya samun matsala shi kuma yana ganin girman Mahaifiyar matarsa, ba zai so wani abu ya haɗa su ta sanadiyyar Raihan ba. Ganin haka ya sa Mommy ta riƙo hannun Goggo tana cewa, "Goggo ta so mu je ɗaki don Allah." Inno na ganin haka ta fashe da kuka tana faɗin:

"Allah ya fini sanin dalilin da ya sa bai bani ƴa mace ba, amma ya yi mini komai da ya bani Audullahi da ban haihu ba sai na rasa mai kaini ɗaki nima." Tana gama maganar ta kalli Alhaji ta ci gaba da cewa, "Audullahi nima ka kaini ɗaki ba sai an goranta min ba, kuma wallahi aure za ka ƙara don ba za ka zauna da macen da bata ganin mutumcina ba."

Daddy na shirin yin magana suka ji Raihan ta turo ƙofa ta fito fuskarta murtuk babu fara'a, da sauri Goggo ta fara ja baya tana leƙenta. Daddy na ganinta ya saki murmushi ya rungumota yana faɗin, "Barka da fitowa habibtyn daddy." ƙarasowa wurin ta yi ta ce, "Daddy ba dai fita za ka yi ba?" riƙo hannunta ya yi ya ce, "Yanzu ma kuwa don na gama komai."

Fisge hannunta ta yi ta koma kan kujera tana faɗin, "Na faɗa maka gaskiya za ka yarda?" Murmushi ya yi ya ƙarasa wurinta ya ce, "Faɗi babyna."

"Ka haƙura da fita da baƙar mota idan ba haka ba za a samu matsala."

Mommy ta kalle ta tana faɗin, "Raihan me ya sa bakinki baya furta alheri ne? Ke kin san gaibu ne da za ki yanke masa wannan hukuncin." Goggo da ke gefe tana son yin magana tsoro ya hanata. Daddy ya gyara zaman agogonsa yana faɗin, "Baby sai abin da kika ce da wacce kike son da ita." Daga wurin da take ta ce, "Kowacce ka yi niyyar fita da ita amma ban da baƙar." Daga haka sallama ya yi musu Mommy ta wuce raka shi, Raihan na ganin haka ta ƙarasa gaban Goggo ta tsugunna a wurinta tana faɗin, "Wallahi na kuma jin kin danganta ni da ƙungiyar asiri Allah za ki yi mamakina, sai na kaiki Daulatul Jinnul nariy na azabtar da ke." Inno da ke gefe ta karɓe zancen da faɗin, "Wallahi kema kya gaya mata ai ni wallahi ban yafe wannan ƙazafin da ta yi miki ba. Ni dai wannan larabcin da kika yi ne ban san me kika faɗa ba, amma idan za ki tafi da ita don Allah ki kaini na ga yadda Zinaru za ta yabawa aya zaƙinta." Raihan bata bi ta kansu ba ta wuce kan dianning table, saboda yadda yunwa take sasaƙar cikinta don abincin da ta ci babu in da yaje mata. Tana zama ta fara buɗe kulolin da ke wurin nan take ta fara tasa kulolin a gaba, ɗaya bayan ɗaya tana cinyewa, kuloli huɗu ne a wurin amma da zaman ta ko minti biyar bata yi ba ta cinye abincin ciki gabaɗaya, tare da shanye shayin da ke cikin fulas ɗin ta kora da ruwa sannan ta dawo falo ta zauna. Lokacin da ta dawo tuni su Inno sun wuce sashensu don haka basu lura da abin da Jabun Raihan ta aiwatar ba.

Sanyin da yake busawa a wurin ne ya doki gangar jikinta wanda ya sa ta buɗe idanunta a hankali tana ƙarewa wurin kallo, cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙe zaune har lokacin kallon wurin take yi da tsananin mamaki. A hankali wannan jaririyar hallitar ta fara matsowa har sai da ta hau cinyar Raihan, zamanta a cinyarta ya sa ta lura da wurin a zabure ta miƙe tana ƙwalla ƙara haɗe da ja da baya zafin buguwar ya sa hallitar yin can gefe wanda yake nuni da jin zafin da ta yi. Waige-waige ta fara yi tana ambatar sunan mahaifiyarta, kamar daga sama ta riski muryar Mommynta tana faɗin, "Ga ni nan zuwa Raihan."

Tafiya ta fara yi daga wurin da ta fara jin sautin muryar, ta wani lungu ta hango Mommynta ta fito cikin doguwar rigar shadda tana sakar mata murmushi, kallo ɗaya ta yi mata ta ji gabanta ya yu mummunan faɗuwa. Dafa Raihan ta yi tana faɗin, "Kin tashi Raihan?"

Kuka Raihan ta fashe da shi tana faɗin, "Mommy ina ne nan menene wancan abin?" Ta ƙarasa maganar tana nuna wurin da wannan hallitar take rarrafowa a hankali, Mommy ta kalli wurin tana murmushi ta ce, "Taho mu je ki rabu da wancen abin." Har sun fara tafiya Mommy ta kalli Raihan ta ce, "Amma duk wanda zai ce miki ki bishi kar kije wurinsa cutar da ke zai yi ni ce mahaifiyarki babu abin da zan yi miki." Har lokacin Raihan a tsorace take don haka ta kalli yanayin wurin ta ce, "Amma mommy ya aka yi muka zo nan?" A ɗan tsawace ta ce mata:

"Za ki taho ko tambaya ta za ki tsaya yi." Ba musu Raihan ta bi bayan wacce take gani da siffar Mommynta, har sun kusa fita sai gani ta yi Daddynta ya diro da ƙarfin gaske yana faɗin, "Raihan." Da sauri ta waiga wurinsa tana shirin yin magana mai ɗauke da siffar Mommynta ta fara fisgar hannunta tana faɗin, "Karki saurare shi wuce mu je." Da sauri ya ƙaraso wurin rai a ɓace ya fisgi hannun Raihan sannan ya dubi Mai ɗauke da siffar Mommy yana faɗin, "Mugaza ki shiga taitayinki fa, na gaya miki ki fita harkar yarinyar nan ba na son na hukuntaki a kanta amma wallahi idan kika illatata sai na baki mamaki." Lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata mummunar hallita mai ɗauke da siffar ƙadangare sai dai kawunanta goma kowanne ɗauke yake da wasu irin manyan harsuna masu kama da kaifin takobi. Da gudu Raihan ta rungume mai ɗauke da siffar mahaifinta tana wani irin kuka tare da faɗin, "Daddy tsoro nake ji." Ilahirin jikinta ban da rawa babu abin da yake yi, rumgume ta ya yi tsam a jikinsa yana shafa bayanta cikin wata irin soyayyarta da take fisgarsa, don karta fahimci wani abu ya sa ya iya riƙe kansa ba tare da kusanceta ba. Wannan abin ba ƙaramin ɓata ran Mugaza ya yi ba, a shammace ta kaiwa Raihan cafka da ɗaya daga cikin harshenta a ƙafa, da sauri Huzaifa ya janyeta amma sai da harshen nata ya samu ƙafarta. Wata uwar ƙara ta ƙwalla sannan ta faɗa jikin Huzaifa wanda yake nuna suma ta yi.

Wata irin mahaukaciyar dariya Mugaza ta fara ƙyaƙyatawa lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana faɗin, "Ki je ki da wannan damuwar zan baki rata kafin na sake waiwayo ki." Tana gama maganar ta ɓace daga wurin.

Cike da tausayi Huzaifa da ke ɗauke siffar Daddy ya shimfiɗar da Raihan, a daidai wannan lokacin jaririn hallitar nan ya ƙaraso wurin ya kwantar da kansa a jikinta. Hannu biyu Huzaifa ya sa ya ɗago jaririn idanunsa ɗauke da ƙwallah ya ce, "Mahaifiyarka na fuskantar ƙalubalen rayuwa, amma daga yanzu zan tsaya mata tsayin daka don kare martaba da ƙimarta." Yana gama maganar ya sake ɗora mata shi a kanta yana motsa baki, lokaci ɗaya jaririn hallitar ya ɓace.

Yana ganin ɓacewarsa ya kalli Raihan da ke kwance ya ce, "Daga yau za ka kasance tare da Mahaifiyarka ko baby komai za ka riƙa ankarar da ni kamar yadda ka ankarar da ni kafin Mugaza ta cimma ƙuduri a kanta."

Share hilis🌚

Ummou Aslam Bint Adam🌚
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 3

     Mommy na shigowa ta nufi wurin dianning sai da ta zauna sannan ta kalli wurin da Raihan take zaune ta ce, "Mama Uwani ta ce min kin yi breakfast ko?" Jabun Raihan da ke zaune a kan kujera ta ce, "Eh na yi ɗazu." Mommy na juyawa ta buɗe kular abinci sai ta ga wayam, sake buɗe ɗayar kular ita ma babu komai; haka ta riƙa buɗe kulolin abincin amma sai taunannun ƙashi a ɗan tsorace ta tashi tana faɗin, "Waye ya cinye abincin nan Mama Uwani?" Cikin rashin damuwa Raihan ta ce, "Yanzu na cinye su." A ɗan tsorace mommy ta ce, "Gabaɗaya abincin ke kika cinye har fa da abincin rana na ajiye mana." Raihan ta miƙe ta nufi ɗakinta tana faɗin, "Wanda Mama Uwani ta kaimin bai ishe ni ba shi ya sa." Mommy sororo ta yi jikinta a sanyaye tana bin bayan Raihan da kallo.

Jabun Raihan na shiga ɗaki ta ji Huzaifa na ƙwala mata kira, ta kusurwar bango ta wuce cike da ɗoki don zamanta a cikin gidan jin ta take kamar a kabari take.

Huzaifa da ke tsaye a gaban Raihan ya dubi Jabun Raihan ya ce, "Mugaza ta yi mata rauni zan mayar da ita ga mahaifanta amma zan ci gaba da bata kulawa kamar yadda na kwashe dubban shekaru ina tsaye a kanta. Ki je na sallame ki idan da yuwar wani lokacin na buƙace ki za ki ji ni." Cike da farinciki jabun Raihan ta rikiɗe  zuwa siffar wani ƙaton tsuntsu mai ɗauke da manyan fuka-fukai ta ɓace daga wurin, daga wurin da yake ya ɗauki Raihan ya ɗora ta akan gadonta sannan ya ɓace daga wurin.

Bayan shigar jabun Raihan ɗaki ta fara kiran Mama Uwani, cike da girmamawa ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Ga ni hajiya."

Mommy ta kalli kulolin kan dianning ta ce, "Mama Uwani yau mun wayi gari da wani abin almara, dubi kulolin nan wai Raihan ta cinye." Da mamaki Mama Uwani ta zaro idanu ta ce, "Hajiya duka ita Uwarɗakin nawa ce ta cinye?" Mommy ta taɓe baki ta ce, "Dama ke ba ta laifi a wurinki ai, yanzu a sake dafa wani abincin bari na haɗa cornflakes." Mama Uwani ta fara tattara kwanukan tana faɗin, "Hajiy ai kowanne laifi kika ɗauko cewa kike ita ce, ni kuma uwarɗakina bata laifi." Tana gama maganar ta kwashe kwanukan ta wuce kitchen da su.

Raihan ba ita ta farka sai bayan azahar, a hankali ta buɗe idonta da suka yi mata nauyi dum! Tana ƙarewa ɗakin nata kallo. Lumshe idonta ta yi saboda yadda ta ji kanta yana sara mata kamar zai tarwatse, yunƙurawa ta yi zata tashi zaune ta ji jikinta ya yi mata wani irin tsami, ƙafarta ta hagu ta ji ta yi mata sanyi kamar ba a jikinta take ba. Da ƙyar ta samu ta fara dafa bango tana jan ƙafar tata da take jin ta yi mata nauyi kamar gungumen icce, tana zuwa falo ta fara yamutsa fuska tana bin ko'ina da kallo, a gefe ɗaya kuma ta fara wani shinshine-shinshine a haukace kamar mahaukaciya sabon kamu, da rarrafe ta fara watsi da kayan fallon cikin wani irin yanayi tana wani irin ƙaraji da gurnani kamar zakanyar da take tsaka da farauta. Ƙarar fashewar kayan ne ya fito da Mommy daga ɗaki a tsorace tana bin wurin da kallo, tana shirin yin magana su Goggo suma suka turo ƙofa suka fito don ganin abin da yake faruwa. Gilas ɗin center table da ta fasa ta fara ɗauka tana wurga musu tana faɗin, "Waye ya ɗauke min ɗana, ɗana ne wallahi duk wanda ya taɓa min shi sai na kashe shi." Inno da Goggo na ganin haka da rarrafe suka juya cikin ɗaki a tsorace, suna shiga suka bankawa ƙofarsu sakata jiki na rawa.

Mommy jiki na karkarwa ta ce, "Raihan lafiyarki kuwa?" Raihan ta sake wurgawa Mommy wata kwalba da sauri ta sa hannu ta kare, kwalbar ta yanketa a hannu jini ya fara zuba, jin ƙarnin jinin mommy ya sa ta fara wurga mata wani mugun kallo tana lasar baki. Ta ci gaba da surutai ba fasali, Mama uwani ta shigo a tsorace tana kallon abin da yake faruwa.

  Hanyar kitchen ta nufa tana zuwa a haukace ta fisgo wata ƙatuwar roba wacce take ciki da ɗanyan kifi, tana zuwa falo ta rungumeta da hannuwa biyu tana sauke ajiyar zuciya.

   Mommy na shiga ɗaki hankali a tashe ta ɗau waya ta fara kiran Daddy, ba a jima ba ya ɗauka ko jiran cewarsa bata yi ba ta fara faɗin, "Alhaji muna cikin tashin hankali, da alama ciwon Raihan na shekarun baya ne ya dawo sabo don Allah ka yi maza ka zo." Amsa mata ya yi sannan suka yi sallama ya katse wayar a gaggauce, Mommy na daga wurin da take a ɗaki tana jiyo ƙarara fashe-fashen kayan da Raihan take yi. Bayan wani lokaci shiru ne ya biyo baya, jin shirin ya sa Mommy ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin. A falo ta hango Raihan zaune rungume da ɗanyun kifi, gabaɗaya ta ɓata jikinta da falon da ruwan kifi ban da ƙarninsa babu abin da yake tashi. Daddy ne ya turo ƙofa ya shigo yana gaba Dr Hamza na biye da shi, sai dai ganin yanayin falon ya sa ya fahimci wannan ciwon nata har ya ninka na baya. Jin sallamar Daddy ya sa ta ɗago da jajayen idanunta tana yi masa wani irin kallo, a haukace ta zaburo kansu tana faɗin, "Kar wanda ya taɓa mini ɗana jinina ne ba zan laminta a raba ni da shi ba."  Tana rufe baki ta wurgowa Daddy wata kwalba saura kaɗan ta same shi a fuska ya kauce, Daddy ne ya fara kiran Yunusa mai gadi yana zuwa suka shiga kiciniyar riƙe Raihan sai da ƙyar suka samu nasarar riƙeta Likita ya yi mata allurar bacci, a take bacci ya ɗauketa ta faɗi gefe.

Kan kujera suka ɗorata Likitan ya fita yana yi wa Daddy bayani.

"Wato Alhaji da alama ciwon yarinyar nan ya dawo sabo, domin idan har abin da mahaifiyarta ta faɗa ne za mu iya cewa ya ninku a kan na da, saboda a da tana surutai kawai idan abin ya tashi, amma a wannan karon tana nuna kifi a matsayin ɗan cikinta. Akwai issue mai girma a game da lamarin ciwonta, za mu yi bincike mai zurfi a kai, sannan kar a riƙa wasa da magungunanta ta riƙa sha akai-akai." Jikin Daddy a sanyaye ya miƙawa Dr Hamza hannu yana faɗin, "Na gode sosai Dr don Allah a yi wani abu kai, ka san ina matuƙar son Raihan ba zan iya jure rashinta." Dr Hamza ya jinjina kai ya ce, "Insha Allah Alhaji kuma a ci gaba da addu'a everything will be successfully." Daga haka suka yi sallama da Likita. Yana komawa ciki tuni ma'aikatan gidan suka shiga hada-hadar gyaran falon, kusa da ita ya je ya zauna ya zura mata ido, hannu ya ɗora a kan goshinta zuciyarsa babu daɗi ya ce, "Wish you quick recovery dear, me ya sa al'amuranki basa zuwa da sauƙi why? Allah ya baki lafiya my baby." Mommy na ƙarasowa wurin ta dubi Alhaji cikin damuwa ta ce, "Habibi ni kam wata shawara gare ni." Bai furta mata komai ba ya ɗago yana kallonta ya yi mata alamar yana sauraronta. Jingina ta yi da bango ta ce, "Gani nake yi mai zai hana ciwon yarinyar nan a haɗa shi da na islamic chemist ko akwai shafar aljanu a ciki..." Tun bata dire zancenta ya buga mata tsawa da cewar, "Ba na son na ƙara jin kin danganta min Raihan da wani jinsin bayan bil'adam, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci. Me ye wani islamic chemist malaman da kaje wurinsu sai dai su fara yi maka turare da hayaƙi, da sun samu wuri za su fara yi maka maula. Idan ba za ki taya ni mu nema mata magani ba don Allah ki cire hannunki daga cikin maganar, ni kaɗai na isa na nema mata lafiya." Ran mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, amma babu yadda ta iya haka ta ja bakinta ta tsuke don ta san akan wannan maganar sai su haura sama su faɗo.  Daddy ne ya cicciɓi Raihan zai kaita ɗaki da sauri Mommy ta nuna masa ɗakinta tana faɗin, "Ka kaita Toilet ɗina zan gyara mata jikinta a can sai ta kwanta." Bai tanka mata ba ya wuce ya kaita ɗakin Mommy don har lokacin fushi yake yi.

Mommy da kanta ta gyara Raihan ta kwantar da ita a kan gadonta, zama ta yi a gefe tana kallon ƴartata cike da tausayawa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, ta sharce ƙwallah ta furta, "Wannan ita ce kalar tamu ƙaddarar, Allah ya baki lafiya Raihan."

Raihan ta jima tana bacci sai bayan wani lokaci sannan ta tashi, ɗingisawa ta ci gaba da yi har ta fito zuwa falo. A lokacin an gyara falon sai ƙamshin turare yake. A zaune ta hango Mommy Mama Uwani na zaune a ƙasa tana matsawa Mommy ƙafa, cike da farinciki Mama Uwani ta ce, "Uwar ɗakina kin tashi?" Kafin Raihan ta yi magana Mommy ta furta, "Barka da tashi My Princess." A ɗingishe ta ƙaraso wurin cikin damuwa mommy ta ce, "Me ya samu ƙafar taki?" Raihan ta yamutsa fuska ta ce, "Wallahi haka kawai na ta yi min nauyi. Mommy kamar mun je wani wurin ko? Ko dai mafarki na yi ne?" Mommy a tunaninta lokacin da ciwon Raihan ya tashi take nufi, ita kuma Raihan tana son tuna zuwanta Duniyar su Huzaifa amma kanta ya yi nauyi ta manta. Mama Uwani ta kafeta da ido sannan ta ce, "Uwar ɗakina sannu kin ji, ai ke kin zama ƙadagaren bakin tulu a karki a kar tulu a barki ki ɓata ruwa." Raihan ta ce, "Yauwa Mama Uwani, don Allah haɗo min ruwan tea." Ta yi maganar cikin jin daɗin kanbabawar da Mama Uwani ta yi mata, Nan take Mama Uwani ta tashi ta nufi hanyar kitchen. A hankali Goggo ta turo ƙofa ta fito falo, don tun lokacin da ciwon Raihan ya tashi da suka shige ɗaki babu wacce ta fito a cikinsu, kallo ɗaya za ka yi wa Goggo ka tabbatar da tsoro ya mamaye zuciyarta amma sai ta dake ta fara yashe baki tana faɗin, "Rehanu hutawa ake yi." Raihan ta taɓe baki ta ce, "Ni kam ko karatu ne wallahi Goggo ya ci ki haddace sunana, kullin sai na ce miki ba sunana Rehanu ba amma ina miyar kuka ta toshe ko'ina." Mommy ta ɓata fuska ta ce, "Gidanku Raihan." Goggo da ta lura Raihan ta dawo cikin hayyacinta, ta yi mata daƙuwa ta ce, "Gata a zaune ita kika gayawa haka." Goggo ta nemi wuri ta zauna tana faɗin, "Abu kunna mini wannan shirin da suke na ƙasashen labarawa ko idanuna sa ƙara ƙarfi." Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Allah ya sani ba za mu kalli masu jajayen kunne ba, ni dai ki kai mini shirinsu wannan yaron Adamu zango da Ali Nuhu, ki saka mana sangaya mu kallah." Mama Uwani ce ta ƙaraso da kofin shayi ta taimakawa Raihan suka wuce ɗaki, don ƙafarta sosai ta yi mata nauyi ɗingisawa take yi.

Shigar su ɗaki keda wuya, Mama Hasiya ƙanwar Daddy ta yi sallama cikin falon. Fara'a ɗauke a fuskarta ta shiga cikin falon. Mommy da murmushi ta tarbi Mama Hasiya tana faɗin, "Mai gidan da ba awo ba cefane, ba waya ba labari." Mama Hasiya ta zame mayafin jikinta tana faɗin, "Mutum da gidansa wacce waya zai yi." Mommy ta saki murmushi tana faɗin, "Barka da zuwa wai da yamman nan kike tafe." Mama Hasiya ta ajiye jakar hannunta tana faɗin, "Wallahi dole ce ta kawo ni, kin san Hubbi ya yi tafiya ƙafar Dubai to sun yi waya da DR John wai yau zai shigo gari so kin san matsalar hospital ɗin Dr John idan kana son ganinsa sai dare." Mommy ta sauya fuska cikin yanayin damuwa ta ce, "Allah ya sa a dace wai wancen karon ba ya ce ƙasa da six months komai zai iya faruwa ba? Ya ce za ki iya samu ciki a kowanne lokaci." Mama Hasiya ta jinjina kai ta ce, "To kin ga dai shiru, lamarin rashin haihuwar nan ba ƙaramin damuna yake yi ba. Tun hubbi bai fara damuwa ba yanzu na fuskanci abin ya fara damunsa, shekara sama da goma sha biyar ba haihuwa an ya ina da rabon ganin ƙwaina a duniya kuwa?" Mama Hasiya ta yi maganar idanunta na cikowa da ƙwallah. Cikin sigar lallashi Mommy ta dubi Mama Hasiya tana faɗin, "Komai kika ga ya faru da bawa da sanin Allah, ba a nan take ba. Komai fa lokaci ne mutane da dama akwai waɗanda suka fiki daɗewa kuma Allah ya kawo musu mafita, mu ci gaba da addu'a komai ya yi farko zai yi ƙarshe." Mama Uwani ta ƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da fara'a tana faɗin, "Hajiya barka da zuwa." Bayan sun gaisa ta fara kawo mata kayan ciye-ciye da shaye-shaye bata jima da barin wurin ba su Inno suka fito falo, nan take suka ci gaba da hira.

Mama Hasiya ƙanwar Daddy ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tana auren wani hamshaƙin ɗan kasuwa a unguwar Hotoro. Sun shafe shekara goma sha biyar da auren saurayi da budurwa, sai dai Allah bai basu haihuwa ba duk wannan tsahon shekarun, sun yi yawon ƙasashe amma duk ba a dace ba har sai da suka fara ganin wani likita Dr John, ta taɓa samun ciki ta yi ɓari har sau biyu daga haka ko ɓatan wata bata sake yi ba, don haka ta nace wa Dr John lokaci-lokaci take zuwa ganin likita.

DR JOHN SPECIAL HOSPITAL shi ne sunan asibitin da Mama Hasiya take zuwa ganin likita, asibitin a bayan gidan su Mommyn Raihan yake. Duk ranar da Mama Hasiya za ta zo ganin likita a gidan Daddy take kwana saboda asibitin sai goman dare Dr John yake fara ganin patient, wannan dalilin ya sa idan ta ga likita take dawowa gidan ɗan'uwanta ya kwana, yawaici tare suke zuwa da Mommy saboda mai gidanta yana tafiye-tafiye, kuma yawo babu inda ba su je ba don neman haihuwa.

Cikin Dare.

   Wata irin guguwa mai ɗauke da amsa kuwwa marar daɗin sauraro ta fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dodon kunnuwanta, a hankali iskar ta fara kaɗa labulayen ɗakinta. A hankali ta fara ratso bangawayen da gidan tana raɓewa ta jikin ƙananan shukokin da ke harabar gidan, ta jikin bangon ɗakinta ta ratso jikinta ɗauke da jajayen kaya masu ratsin baƙi haɗe da ɗishi-ɗishin busasshen jini a jikinta. Tana shiga ɗakin Raihan ta tsaya cak a bangon gudu, ta fara huro mata iska nan take Raihan ta miƙe zaune hannuwanta toshe a kunnuwanta ta dubi Intisar. Cikin wata irin girgiza ta ƙaraso wurin Raihan ta kama hannuwanta tana shirin yin magana Raihan ta ce, "Intisar me kika zo yi yanzu gidanmu?" Intisar bata bi ta kanta ba ta hura mata iska a fuska nan take ta fara layi tana shirin faɗuwa, da sauri Intisar ta tarota tana dafe kafaɗarta ta ce, "Za ki bi ni?" Babu musu Raihan ta gyaɗa mata kai, Intisar bata bi ta kanta ba ta riƙe hannunta nan take suka ɓace daga ɗakin.

Gudu suke zabgawa cikin sararin samaniya a can wani ƙasurgumin dajin wani makeken gida suka sauka, Raihan ban da ido babu abin da take bin ƙawarta Intisar da shi. A wani katafarn kogon dutse suka dira mai ɗauke da wasu irin mutane masu mummunar hallita, ɗauke suke da jajayan sitiru sai zanen jini a jikkunansu. Wata mummunar hallita ce a tsugunne mai ɗauke da kan barewa da manyan ƙahunhuna ga wani irin jini da yake ɗiga daga bakinta a cikin wani ƙaton faifai. Zuwansu ke da wuya wani tiƙeƙe da ya kasance babbansu ya dubi Intisar ya ce, "Hatsabibiya Bungulu na maraba da baƙuwa mai daraja." Intisar da dubi Raihan ta ce, "Ki yi gaisuwa ga Habibiya Bungulu ta saka miki albarka." Kamar bawa da uban gidansa haka Raihan ta dubi wannan hallitar ta duƙa kamar yadda ta ga suna yi ta miƙa gaisuwa. Da wani ƙaton sirinji wani ɗan tsamurmuri ya zuƙi jinin da wannan hallitar take ɗigarwa daga bakinta, a shammace ya samu damtsen hannun Raihan ya kafa mata har sai da ya juye jinin jikin sirinjin a jikinta, sannan ya zuƙo nata ya fesa a jikin hallitar. Lokaci ɗaya ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta duƙushe a wurin tana karkarwa.  Tana jima tana abu ɗaya sannan ta tsagaita da rawar ɗarin, a zabure ta miƙe tsaye cikin wani irin ƙarfi ta zurawa mummunar hallitar tana jiran umarninta.

Buɗe bakinsa ya yi nan take wasu baƙaƙen macizai suka fara fitowa daga bakinsa, suna faɗowa suke fasa kai suna zagaye Raihan. Cikin wani irin yanayi hallitar ta miƙe tsaye tana girgiza sannan ta fara magana da wani irin yare har sai da ta yi yare ya fi kala goma, sannan ta yi magana da harshen hausa.

"Tabbas mun yi babban kamun da muka jima muna jiran wannan rana. Domin ƙara tabbatar da abin da muke zargi goɗiya za ta kawo mana jini mafi muhimmanci wanda zan shayar da mai gidana domin samun lafiyarsa." Tun bai rufe baki ba Raihan ta russuna tana faɗin, "An gama Hatsabibiya Bungulu." Mummunar hallitar ta nunawa Raihan wata ƙatuwar ƙwarya mai cike da tafasasshen jini ta ce, "Babu buƙatar haka domin da alama ke shugaba ce, muna buƙatar jinin wannan matar yanzun nan..." Raihan ta amsa mata tun bata ƙarasa maganar ba da cewar, "Jininta ya halarta a gare ki, duk duniya babu jinin da za ki buƙata ya gagara a wurina." Tana rufe baki Hatsabibuya Bungulu ta miƙa mata wani busasshen ƙashi da alama ƙashin jikin bil'adam ne. Raihan na karɓa ta wuce cikin sararin samaniyar iskar sihiri bata tsaya ko'ina ba sai a katafaran cikin gidan Mahaifinta, sai da ta zaga ɗakunan gidan sannan ta dira a ƙofar ɗakin mahaifiyarta.

🤭🤭🤭 WASAN YANZU YA FARA, MAZA HANZARTA KI BIYA NA KI DON JIN WACECE AINIHIN ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ƊIN, SHIN A CIKIN SU WACECE ƳAR GABAN GOSHIN ALJANIN SOYAYYAR? SHIN WACECE WANNAN INTISAR ƊIN KUMA WACECE HATSABIBIYA BUNGULU? 😁 AMSOSHIN NA GABA DON JIN ƘULALLEN ƊAURIN DA KE CIKIN LABARIN.

Share Fisabillah🌚
[7/10, 10:33 AM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 4

     Raihan na fita Intisar ta ƙarasa gaban Hatsabibiya Bungulu rai a matuƙar ɓace ta ce, "Hatsabibiya uwar hatsabibai, sai kai mai siffar dabba a bayan fage ki koma bil'adama. Babu hallitar da ta gagare ki rikiɗa duk girmanta duk ƙanƙantarta, yaya ina tunanin lokacin share mini hawayena ya zo amma na ga wankin hula yana shirin kaini dare. Na kawo Raihan domin a salwantar mini da rayuwarta amma da alama tana shirin samun fada a wurin nan, yake Hatsabibiya tun farko kin san ba haka muka yi da ke ba."

Hatsabibiya Bungulu ta yi girgiza lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata kyakkyawar budurwar, zaune take tsirara sai wasu sassan gaɓɓoɓin jikinta da ke rufe. Wani malalacin murmushi ta saki sannan ta dubi Intisar ta ce, "Da mun san kina da wannan yarinyar da tuni mun jima da umartarki ki kawo mana ita, sai dai kash! Silar saninta na daga gare domin biyan buƙatarki. Kin kawota domin mu kashe ta sai dai ba za ta mutu ba." Da hannuwa biyu Intisar ta sa ta toshe dodon kunnenta saboda yadda ta ji kalmar a kunnenta, a duniya idan da wacce ta tsana to Raihan ce. Lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana shirin yin magana Hatsabibiya ta ci gaba da magana.

"Na tabbata baki san wacece Raihan ba, da kin san amfanin da za ta yi mana a cikin ƙungiya da bakinki bai furta kalmar kisa a tattare da ita ba. Shin ko kinsan Muraza?" Da sauri Intisar ta ɗago da kai tana kallon Hatsabibiya tana girgiza kai bakinta na rawa ta ce, "Ina zan santa ya ke Hatsabibiya mu da muke nemanta ido rufe." Matashiyar budurwar da ake kira da Hatsabibiya ta yi girgiza nan take ta rikiɗe zuwa surar wani ƙaton tsuntsu, sai da ya yi tsalle-tsallensa sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da magana cikin siffar tsuntsu.

   "Tabbas Raihan ita ce Muraza, tun shigowarta kogon dutsen nan alaminta da babban matsafi ya sanar da mu suka bayyana. Ƙofar nasarorinmu ta buɗe ƙarfin iko, tsafi da sihiri da ƙarfin ƙungiyar asirinmu za ta sake dawowa da ƙarfin ikonta, domin haske ya bayyana inuwarta ɗauke take tartsakin wuta mai halakar da magautanmu, za mu riƙe hannu bibbiyu domin saminta tamkar samun lu'ulu ne a ƙarƙashin teku, idan muka yi sake ta kubce mana tabbas mun tafka babbar asara." Intisar ta faɗaɗa murmushinta sai da ta yi taku biyu sannan ta waiwayo ta ce, "Haƙiƙa zan jinkirta buƙatata har tsawon wani lokaci bayan mun cimma matsayarmu, amma tabbas ko ba yanzu ba akwai ranar da Ya za ta ɗakin ƙanwa, lokaci na tafe zan aiwatar da abin da yake ci mini tuwo a ƙwarya. Ni ma lokaci ya dawo mini da zan karɓo sihirtacciyar sandar mahaifiyata Bokanya Shirzan, a lokacin ne duk wani cikar ikona zai dawo." Tana rufe baki suka fara ƙyaƙyata wata irin dariya mara daɗin sauraron mai ɗauke da amsa kuwwar kukan jakuna, suna tsaka da kuka sai ga wani matashin saurayi ya diro cikin ɗakin hannunsa ɗauke wani jariri sabuwar haihuwa. Jaririn sai mutsu-mutsu yake ko jikinsa ba a gyara ba balle a yanke cibiyarsa, a kan tafin hannun wani gunkin tsoho da ke tsaye ya wara hannuwansa. Yana ɗora jaririn a kai nan take wannan Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar tsuntsu ta taso ta dira a kan cikin jaririn. Wata ƙara ya ƙwalla saboda wata irin azaba da ke ratsa sassan jikinsa, da ƙafafuwansa tsuntsun ya huda ƙirjin jaririn ya kafa kai yana tsotsar jinin jaririn. Kafin wani lokaci tuni idanun jaririn sun ƙafe jikinsa ya saki numfashinsa ya ɗauke, tana ganin haka ta tashi daga kanta sai Intisar ta ƙarasa ta banƙare ƙirjinsa ta ciro zuciyarsa ta wurga bakinta ta cinye.

Ɗaukan gawar jaririn ta yi ta miƙawa sauran mutanen wurin, da sauri suka caɓe shi suka buɗe wani ƙaramin ɗaki mai ja da baƙin labule suka wurga ciki.

   Raihan na zuwa gida a hankali ta fara zaga bangon da ke cikin ɗakunansu, ga mamakinta tana bi ta cikin ɗakinta ta hangi mai siffarta kwance a kan makwancinta a gefe ɗaya ga Mama Uwani tana zaune tana gadinta. Amma ga mamakinta sai gani ta yi ta gifta ta gabanta ba tare da ta lura da ita ba. Hasalima ratsawa take yi ta ko'ina ba tare da gini ko ƙofa sun yi mata shamaki ba, a hankali ta ci gaba da tafiya kamar mai tafiya a sararin samaniya har ta dira a ɗakin Mahaifiyarta sai da ta ƙare mata kallo sannan ta wuce ɗakin da Mama Hasiya take kwance tana bacci. Kamar yadda Hatsabibiya ta umarceta haka ta tsaya a saitin kanta, ƙashin hannunta ta kai saitin fuskar Mama Hasiya lokaci ɗaya ta buɗe idonta firgigit ta sauke su a kan Raihan, sai dai a cikin idanunta gani ta yi Raihan ta siffanta da wata mummunar hallita, cikin rashin tausayi Raihan ta ƙarasa gabanta ta damƙo maƙogaronta, nan take Mama Hasiya ta fara kakari idanunta suka firfito waje.

Da murya mai wahalarwa Mama Hasiya ta fara karanta kalmar shahada, tana yi tana ambaton sunan Maigidanta da duk sunan wanda ya zo bakinta.

Ana cikin haka wasu tafka-tafkan kunamu suka fara ratsowa ta jikin bango girman kowacce ɗaya ya fi girman kan jariri, da gudu suka fara rarrafowa suka haye gadon sun kai kusan goma suka maƙale a jikin Mama Hatsiya kowacce ta kafa bakinta suka fara zuƙar jini.

    Cikin tsananin azaba Mama Hasiya ta fara wani irin ƙaraji da gurnani, tun tana cikin hayyacinta har ta fara fita daga haka idanunta suka kafe rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka ta saki wuyan gawar Mama Hasiya ta faɗa kan gado yaraf ta ja mayafi ta rufeta sannan ta miƙawa kunamin nan hannu lokaci ɗaya suka maƙaleta, ta ɗago da su saitin fuskarta. Haƙoranta ne suka fara girma ga wata fiƙa irin ta karnuka da ta fito mata, bakinta ya fara zubda wani baƙin jini mai yauƙi. Ƙwayar idanunta zazzago suna wani irin juyi, a hankali ta fara takawa ta fice daga ɗakin ta koma ta sashen ɗakin Mahaifiyarta, ta jima a bakin window sai da ta yi ƙwafa sannan ta ratsa ta jikin bango ta fice daga gidan.

  Bayan sun wurga Jaririn cikin wannan ɗakin wata irin tsawa aka yi mai haɗe da walƙiya, a hankali hatsabibiya ta shiga ɗakin tuni wata mummunar hallita mai ɗauke da kawuna har guda goma a jikinta, a kowanne baki akwai aikin da yake aiwatarwa. A ɗaya daga cikin kan mummunar hallitar ta cafke jaririn tana laƙumewa, wani kan kuma ya fara amayo da kuɗaɗe kala-kala har da na ƙasashen waje, ya yin da wani kan ya fara tatsar da wani ruwa mai yauƙi yana zuba watsu ƙananan ƙwari suna zuwa suna tsotsa.

   Suna nan tsaya Raihan ta diro cikin gidan, hannuwanta biyu saƙale da kunamu tana tafe cikin takun ƙasaita dauke mummunar hallita. Tana zuwa Hatsabibiya ta fito fuskarta ɗauke da murmushi, shigar Raihan wurin ya sa jikin wannan dattijon ya fara ɓamɓarowa daskararran jikinsa ya fara rozayewa a hankali har ya rozaye gabaɗaya. Wata irin girgiza ya yi nan take ya fara kallon mutanen wurin ɗaya bayan ɗaya, Hatsabibiya ta tako a hankali fuskarta ɗauke da annuri ta ce, "Barka da dawowa cikin rayuwarka ta ainihini Ya masoyina." Hannuwanta ya riƙo yana bin ta da kallo lokaci ɗaya ya rungume ta yana shafa bayanta sannan ya ce, "Ina godiya da sadaukarwarki, amma ya aka yi kika samu tsarkakken jini alhalin an ce sai ta silar Muraza shin kun samota ne?" Hannunsa ta ja bakin wata tsohuwar rijiya da ke cikin ɗakin tana faɗin, "Mu je turaka zan baka labari." Tana rufe baki suka faɗa cikin rijiyar shigewarsu keda wuya wurin ya shafe tamkar ba a taɓa hallitar wani abu a wurin ba.

   Wani tutturnan mutum da suke kira da Mataimaki shi ya ƙarasa wurin Raihan ya karɓi kunamin hannunta, ya zuba su a cikin wani ƙoƙon kai sannan ya dubi Raihan ya ce, "An gaishe ki Jaruma, Shugaba mai cikakken iko sai ke gagabadau. Za ki iya tafiya sai ranar taro na gaba amma a ranar muna buƙatar tukwicin sabuwar gawar mace mai ƙarancin shekaru kar su yi ƙasa da talati kar kuma ta haura shekara arba'in." Raihan ban da jinjina kai babu abin da take yi, tana gama sauraronsa ta dubi Intisar alamar su tafi. Intisar ta nuna mata wata ƙoriyar ƙwarya mai cike da wani ruwa mai ɗauke da launin jini kamar anwanke nama, sannan ta ce: "Ki kuskure bakinki da ruwan tsarki domin samun albarka." Ba musu Raihan ta ƙarasa ta ɗauki ƙwaryar ta kafa kanta, tana kafa kai ta ji kanta ya sake yin nauyi dumm! A hankali ta iya kai ƙwaryar bakinta ta kuskure wata irin kasala ta mamaye jikinta, ga wani irin addababban bacci da ya lulluɓe idanunta. Tana ajiye ƙwaryar ta tafi luuuu za ta faɗi da sauri Intisar ta taro ta jikinta, sannan ta saɓa ta a kafaɗa ta fice daga cikin kogon dutsen kai tsaye ta wuce gidan su Raihan.

    Intisar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsakiyar ɗakin Raihan, tana kallon Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi. Kwantar da Raihan ta yi sannan ta fara zagaye ɗakin ba tare da idanun Mama Uwani sun gane mata Intisar ba, lokaci ɗaya ta saki wata mahaukaciyar dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta durƙushe a wurin sannan ta ratse ta ƙarƙashin ƙasa ta fice daga ɗakin.

  WASHEGARI

    Da Asuba bayan su Inno sun gabatar da sallah suna zaune kowacce a sallayarta suna jan carbi, Goggo ta dubi Inno ta ce: "Wai ni kuwa yarinyar ta tashi sallah kuwa don ko motsinta ban ji ba, saboda Allah neman haihuwa ya fi bautar Ubaniji. Jiya na ga saboda neman haihuwa raba dare suka yi a wurin wancen Kafiriin, gaskiya a tambayi Malamai an ya; ya hallata neman haihuwa wurin kafiri." Inno takaici ya fara rufeta, ta dubi Goggo ta ce, "Zinaru ki yi ta kanki idan kika kafirta min yarinya a yau ba sai gobe wallahi sai Audullahi ya mayar da ke Albasu. Kafira ce da har yanzu za ta zauna babu sallah babu salati?" Goggo cikin nuna rashin damuwa ta wara hannuwa tana faɗin, "Allah shi ne masanin daidai, ba zan amsa ba ki sa na yi wa ƴar mutane ƙazafi akan abin da ban ji ba ban gani ba, ni dai na san da Hasiya ta tashi za ta leƙo wurinmu. Bari ki ga na je na tashe ta ko na samu lada mai tsoka, bar zancen Albasu tun da ko jini baki taɓa zubarwa a cen balle a binne mabiyyarki." Goggo na ƙarasa maganar ta fice daga ɗakin, tana tafe tana mita har ta ƙarasa bakin ƙofa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar sai ga Inno ta rufo mata baya ta ƙaraso wurin tana faɗin, "Saboda Allah Zinaru in haifi abartawa a ciki amma ki nemi ki yi mana farraƙu da ita, Allah ya sani idan Hasiya ta ga ban tashe ba na ɓalɓalce don ɗauka za ta yi baƙin cikin shiga aljanna nake yi mata." Goggo bata bi ta kan Inno ba ta tura ƙofar tana rangaɗa sallama, kamar haɗin baki suka shiga ambatar sunan Hasiya amma shiru suka ji kamar an shuka dusa. Inno ce ta yaye zanin rufar jikinta nan take suka yi tozali da gawarta, kusan suman tsaye suka yi aka rasa mai furta koda kalma ɗaya ne.  Nan take Inno ta yanke jiki ta faɗi, Goggo jiki na tsuma ta juye hanyar waje tana ƙwalawa Mommy kira. Can sashenta ta wuce saboda fargaba tini ta zubar da carbi don lokaci ɗaya ya tsinke ya tarwatse, da kusan rarrafe Goggo ta hau sama tun bata ƙarasa ba suka ci karo da Mommy shi kansa Daddy kiran Goggo ne ya sa shi fitowa daga ɗakinsa a lokacin yana zaune yana cike-ciken takardu.Hankali a tashe  suka shiga jera mata tambayoyi ban da nuna musu ƙofa babu abin da take yi, sai da ƙyar suka samu ta iya furta, "Hasiya babu ta riga mu gidan gaskiya." Cikin rashin fahimta suka ce, "Wace Hasiya?" Saboda ko a kaɗan basu kawo Hasiya a ransu ba. Goggo cike da jin haushi ta ce, "Hasiya dai ƙanwarka Audullahi ko kana da wata Hasiyan ne." Kusan tare suka nufi hanyar sauka don zuwa su ganowa idanunsu.

   Kamar masu rige-rige haka suka shiga ɗakin da Hasiya ke yashe a kan gado, Daddy ne ya fara zuwa kan Inno Mommy ta ƙarasa wurin gawar Hasiya ta fara tattaɓata tana ambatar sunanta amma shiru tafiya ta miƙa. Da hanzari Mommy ta wuce firji ta ɗebo ruwa ta fara yayyafawa Inno sannan ta yayyafawa Hasiya, nan take Inno ta fara motsawa saidai da alama bata cikin hayyacinta amma Hasiya ko alamar motsi bata yi. Daddy ne ya rungumo Inno ya fita a guje yana ƙalawa maigadi waya, kusan gware suka yi a hanya Daddy ya nufi wurin motoci yana faɗin, "Maza-maza buɗe min gate." Tun bai rufe baki ba Driver ya fara kiciniyar buɗe ƙofa nan take bawa motarsa wuta ya fice daga gidan, Mommy jiki a sanyaye ta bi bayan motar da kallo fuska ɗauke da hawaye. Ɗakin ta koma ta janyo hannun Goggo ta rufe ɗakin, kan kujera ta zauna ta rafka tagumi ban da hawaye babu abin da take yi, saboda ba ƙaramin shaƙuwa suka yi da Hasiya ba. Goggo ban da sintiri babu abin da take yi tana nan tsaye suka ga Mama Uwani ta fita, cikin rashin sani ta fara tambaya, Goggo da sai a lokacin kuka ya kubce mata cikin shassheka ta ce, "Bari Uwani yau mun wayi gari da tashin hankali Hasiya babu, yarinyar nan jiya-jiya muka gama hira da ita amma yau sai labari." A tsorace Mama Uwani ta nufi ɗakin don ganewa idonta, tana shiga ta samu gawar a kan gado cikin hanzari ta buɗe ta tana ƙarewa gawar kallo.

   Ido ta zurawa gawar tana jinjina kai a hankali ya furta, "Tabbas akwai lauje ciki naɗi amma akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da gawar nan." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin zuwa falo, ba a ɗauki lokaci ba sai ga Daddy ya dawo. Dawowarsa babu wuya mommy ta tashi Raihan ta sanar da ita halin da ake ciki, murtsuke ido ta yi tana yamutsa fuska ta ce, "Mommy waye ya mutu?" Mommy ta sake maimaita mata, "Mamanki Hasiya yanzu haka gawarta na ɗaki mutane sun fara taruwa." Lokaci ɗaya ta ji kanta ya yi mata nauyi dum! Har sai da ta runtse idonta ta buɗe ta dafa kanta da hannu biyu ta ce, "Mommy me ya sameta ta mutu?" Da sauri Mommy ta rufe mata baki tana faɗin, "Raihan wa yace miki sai an yi ciwo ake yin mutuwa?" Jikin Raihan ba ƙaramin mutuwa ya yi ba, a hanakali ta tashi tana haɗa hanya jikinta sanye da rigar bacci shara-shara babu abin da ta ɓoye na surarta. Ɗakin da Mama Hasiya take ta tunkara Mama Uwani na hangota da sauri ta nufi wurinta ta rungomata tsam a jikinta tana faɗin, "Uwar ɗakina sai haƙuri." Wani iri Raihan ta ji a jikinta yarr a lokaci ɗaya kanta ya yi mata yaaaam! Tsigar jikinta ce ta ci gaba da tashi, a hankali ta saki hannunta tana bin Raihan da wani mayatattacen kallo.

Kafin wani lokaci tuni gidan ya cika da mutane ban da koke-koke babu abin da ake yi, Raihan can gefe ta raɓe ta fashe da wani irin matsanancin kuka. Mai gidanta da aka gaya masa da farko ƙaryatawa ya yi sai da ya zo ya ganta, zama ya yi kamar mace ya yi ta kuka sai da ƙyar ya yi shiru. Kimanin ƙarfe goma aka gama wanke gawarta aka shiryata, ana gabda za a fita da ita sai ga Intisar ta turo ƙofa ta shiga gidan tana kallon mutanen gidan ɗaiɗai tana shigowa ana ɗaukan gawar, tana kalle-kalle Mama Uwani ta fisgi hannun Intisar ta ja ta ɗakin baya wanda baƙi suke sauka a ciki. Rai a matuƙar ɓace ta dubi Intisar ta ce, "Me ya kawo ki gidan nan?" Intisar dariya ta yi ta fara takawa a hankali sai da ta yi taku uku sannan ta juya ta kalli Mama Uwani ta ce, "Abin da ka ke yi cikin suffar tsofaffi shi ne ya kawo ni a wannan suffar."

[7/1, 6:00 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 1

     Babban gida ne mai ɗauke da ɓangare daban-daban har kusan sashen mutum goma sha biyu. A taƙaice za mu iya cewa gidan gandu ne da ya haɗa Kakanni, 'ya'yaye da jikoki. Garin Ɗangwauro yana ɗaya daga cikin ƙanana ƙauyukan da ke cikin ƙwaryar Kano, Allah ya azurta su da noma, kiwo da kasuwansu. Gidan Malam Muhammadu mai dogon Carbi sanannan gida ne a kaf cikin garin Ɗangwauro. Tun daga titi idan ka tambaya za a kai ka har cikin gidan, sakamakon gida ne gidan yawa don wani lokaci mutane na yi masa laƙabi da gidan 'Ya'ya da yawa.

  Gidan Mai dogon Carbi cike yake da mutane sakamakom wayar gari da suka yi da rasuwar rashin wannan Dattijo mai yawan shekaru, ba iya gidan ba hatta garin Ɗangwauro ya girgiza da rashin wannan Dattijon mai dogon zamani. Yaya Babba da Inna Furai sune matan wannan Dattijo da ya rasu mutuwar ba ƙarmin taɓa su ta yi ba.

   Bisa ga al'adar Malam bahaushe a ranar da aka yi mutuwa mutane sun fi nuna damuwarsu ta hanyar koke-koke, kukan ma yana taƙaita yawancin bayan ankai mammaci. Hakan ce ta faru a gidan Mai dogon carbi domin an fita da gawarsa a yi mata sallah yara da Manya sai kuka suke yi.

   A gefe ɗaya Hali dubu na hango rakuɓe sai muzurai take lokaci-lokaci tana share hawaye, sai dai cikin zuciyarta haushin mutanen gidan take ji saboda ta lura babu wanda yake bi ta kanta don ya rarrasheta, duk kuwa da irin gursheƙen kukan da take yi. Kallonsu ta fara yi tana ayyana irin abin da za ta yi domin ta janyo hankulansu kanta. Tun da ai ita gani take kamar ta fi su jin mutuwar koda suna yawan faɗa da Mai dogon carbi amma kafin ya rasu,  ai ita ma Kakanta ne.

   Sumi sumi sumi ta tashi da yaƙunannan hijabinta ta bi hanyar soron gidan tana waiwaye, sai da ta je soron ƙarshe daga shi sai fita Hali dubu ta ɗora hannuwa biyu akanta ta dawo cikin gidan da gudu tana cewa, "Wayyo Allah! Wayyo ni na shiga uku na lalace." Lokaci ɗaya hankulan mutanen gidan ya dawo kanta, da sauri aka yi carko-carko a kanta masu jero tambaya na yi. Zuciyarta ƙal don ko ba komai ita ma za a rarrasheta kamar yanda aka saka su Yaya Babba ana basu haƙuri. A fakaice take satar kallonsu tana sake sharce hawaye amma ta yi biris babu wanda ta tankawa duk irin tambayoyin da mutane suke yi mata. Baba Munkaila ne ya shigo ya hango cincirindon mutane a tsaitsaye da sauri ya ƙarasa wurin, ganin Hali dubu a zaune ya sa ya ja guntun tsaki sannan ya buga mata tsawa, "Ke lafiya kike yi wa mutane ihu?" Kamar sabuwar Marainiya haka ta ɗago shanyayyin idanuwanta ta kalle shi sai kuma ta waiga ta saci kallon ƙofa ta kuma duƙunƙune  kanta cikin alamun tsoro da firgici. Kamar haɗin baki dukansu suka kalli bakin ƙofar suna neman ƙarin bayani, babu abin da ta furta musu sai ma kuka da take yi tana nuna musu ƙofar da ɗan yatsanta. Baba Munkaila tsawa ya sake buga mata ya ce, "Me ye a cen ɗin?" Hali dubu ta kuma kallon ƙofar ta rushe da kuka tana cewa, "Baffa ne!" Cikin haɗin baki duka suka ce, "Baffa kuma? Wane Baffan?"

   Bata bi ta kansu ba sai kawai ta baje a wurin ta fara wata irin birgima tana cewa, "Wayyo Baffa ne ya tafi ya barni!" Takaici ne ya rufe Baba Munkaila domin ya san za a rina don ya tabbata ganin Dubulliya tana wannan kukan ba banza ba. Cikin faɗa-faɗa ya fara yi mata magana amma ko gezau ba ta motsa ba. Can gefe ya hango wata igiyar dabbobi ai kuwa bai yi wata-wata ba ya fara tafka mata, tana jin shigar bulala ta tashi ta yi cikin gida ta gudu.

   Can ɗakin Yaya Babba ta shiga ta haye ƙarshen gado tana kuka, ga haushin Baba Munkaila ya tsinkata a cikin mutane. Tambayar duniya Yaya Babba ta yi amma Dubuliyya kanzil! Bata ce da ita ba. Sai ma ta yi zamanta a nan domin duk duniya babu abin da tafi tsana kamar taron jama'a a gidansu. Domin ba ƙaramin takura take yi ba, dalilinta na haka kuwa ta yanda za ta ji mutane na bata ji ko kuma ta cika rashin ji kamar ƴar aljanu. Tana daga kwance dabara ta faɗo mata ta yanda za ta kore jama'ar gidan ta ruwan sanyi domin ta san yanda danginsu suke sai a kusa arba'in da mutuwar da sauran baƙi tsiraru. Saboda haka Baffa mai dogon Carbi ya saba musu tun yana raye, idan suka zo taro baya barin ƴan uwansa su koma a kwana kusa. Wannan dabara tata ba ƙaramin daɗinta ta ji ba don har sai da ta murmusa saboda farin ciki. Kamar wacce aka tsirawa allura haka ta zabura da sauri ta fice daga ɗakin Yaya Babba, ita kanta Yaya Babba ba ƙaramin daɗi ta ji ba kasancewar duk duniya babu Jikarta da take so kamar ita sakamakon Marainiya ce gaba da baya.

   Dubu tana fita ta yi garau da ita kamar ba ita ta sharɓi kuka ba, nan fa mutane suka fara yi mata tsiya, har da masu cewa dama ita zuma ce sai da wuta. Wasu kuma su ce gara da ya yi mata haka ga shi ta ware ta fara harkokinta. Shiru ta yi babu wacce ta tankawa sai dai duk wacce ta yi magana tana auna maganar tata a mizani domin ta san irin hukuncin da za ta yi mata.

   Tun da Magriba ta doso Dubulliya ta fara haɗa kayan aikinta a fakaice cikin hikima da basira, ba tare da wani ya fahimci halin da take ciki ba. Sakamakon babban gida ne kowa da wurin da yake nema ya kwanta saboda ko ina a wadace yake hakan ne ya sa Yaya Babba bata damu ba da Hali dubu ta ce za ta sashen Baba Munkaila ta kwana a cen.

   DA DADDARE

    Da daddare gidan ya yi tsit ban da kukan tsintsaye da ƙananan dabbobi babu abin da yake tashi, sai munsharin  bacci da yake tashi daga ɗakunan daban-daban. Dubuliyya tana daga sashen Baba Rufa'i cikin ɗaya daga cikin ɗakunan ƴaƴan gidan. Sai da ta ci baccinta ta more sannan ta farka cikin talatainin dare ta ji gidan tsit kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki ta zaro kayan marigayi Baffa ta saka rigarsa da babbar riga har da hula ta naɗa rawaninsa ta ɗauki zabgegen carbinsa ta maƙala ta fito, hasken farin wata ne ya haska mata hanyar da za ta rinƙa bi har fice daga sashen gabaɗaya. Can wurin da ya zamewa Marigayi Baffa mai carbi wurin alwala can ta je ta tsugunna, daga nesa idan ka hango Dubu a tsugunne sai ka rantse da Allah Baffa ne, sai da ta waiga hagu da dama sannan ta taƙarƙare ta fara zabgo kaki irin yanda Baffa yake yi, Baba Sule da ke kwance cikin baccinsa ya fara jin alamar kaki tamkar yanda mahaifinsu yake yi duk asuba. Fakare ya yi yana zare idanu, yana cikin wannan yanayin ya sake jin an yi kaki har da irin tarin tsofaffin nan da Baffa yake yi. Janyo wayarsa ya yi yana dubawa ya ga ƙarfe biyun dare, nan take ya hau murza idanu yana sake kasa kunne. Dubu kamar ta san ana sauraronta ta kausashe murya sai ka rantse da Allah Baffa ne yake magana ta fara cewa, "Tabbas rayuwar barzahu daɗi gare ta." Baba Sule ya waro idanu wace cikinsa na karta masa, don ya tabbata hatta dabbobin gidan da suna magana za su ce sun shaida maganar Baffa ce cikin daren nan.

   Dubu na tsugunne ta ji alamun tahowa wata zuciyar ta ce mata ta tashi ta ɓuya, wata kuma ta ce ta zauna ta ci gaba da abin da take yi. Tarin Inna Furai ta ji ta saci kallonta ta hangota da ƴar buta a riƙe za ta je banɗaki. Dubu wani kakin ta sake yi tana daga tsugunne, hasken farin wata ne ya hasko mata mutum durƙushe da fararen kaya da rawani tamkar marigayin mijinsu. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa ta fara motsa baki cikin addu'a don a zatonta mugun gamo ta yi.

  Ɗauke kai ta yi don ma kar ta ci gaba da kallon wurin da Dubu take ta ci gaba da tsoratata, sai da ta kusa da wurin da Dubu take ta ji muryar marigayin mijinsu raɗau a kunnenta yana cewa, "Wato ita dai rayuwar barzahu daɗi gare ta. Babban daɗin idan ka kawo ziyara tsohuwar rayuwarka sai kuma ka tafi da matarka." Inna Furai na jin haka ta dafe ƙirji tana ja da baya jikinta har tsuma yake ta ce, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa ni Furaira. Allah na roƙeka karka jarrabe ni ta wannan fannin." Dubu na jin haka ta miƙe tsaye tana gyara zaman babbar rigar jikinta ta sake kausashe murya ta ce, "Wuni ɗaya har na yi abokai miliyan ɗaya da ɗari biyar a cikin Fatalen har da masu tashi sama. Ƴan sama jannati ku zo ga wani naman mun samu, kuma daga yau mun fara ɗauka kenan a gidan nan. Duk wanda ya wayi gari ya ga likkafani a jikin kayansa shi za mu yi wa ɗaukan amarya." Inna Furai tuni fitsarin da take riƙewa ya samu sukunin tsiyayowa, sakin butar hannunta ta yi jikinta na tsuma donma bongon da ke bayanta ya tokareta.

   Dariya ce ta so ƙwacewa Dubu amma ta maze ta ce, "Ƴan uwana ƴan sama Jannati! Ku zo na fara samo muku ƴar uwa." Inna Furai ta saki salati tana cewa, "Yau na haɗu da zazzagar rayuwa shi kenan tawa ta zo ƙarshe." Dubu sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara takowa gaban Inna Fuarai ta ce, "Idan kina son fansar kanki sai kin sake shayar da ƴaƴanki tamkar yanda kika shayar da su suna jarirai, tun daga kan Larai (Ita ce babbar Ƴar Inna Furai) har zuwa kan Sabi'u (Shi ne autanta) idan kika kuskurewa haka tabbaci haƙiƙa sai mun zo ido biyu mun tafi da ke babu wanda ya isa ya hana."

    Baba Sule tuni cikinsa ya ɗuri ruwa yana son fita domin ceton Matar Mahaifinsa tsoro ya cika masa ciki, bai gama tsinkewa da lamarin ba da ya ji an fara kiran yan sama jannati. Dubu don ta ƙara razana Inna Furai ta sake dakushe murya ta ce, "Ki isarwa da mutanen gidan nan saƙona muddin suka ci gaba da kwanaki sai na yi musu ɗauki ɗaiɗai. Shi kuma na ɗaki da yake laɓe yana sauraronmu, shi kuma ɗauke shi za mu yi gabaɗaya." Dubu na cikin magana sai gani ta yi Inna Furai ta zube ƙasa. Gabanta ne ya faɗi ta ji fargabar kar tsohuwar mutane ta mutu a hannunta. Da sauri dubu ta waiga sai kuma ta kurma ihu tana maƙe murya ta zunduma ihu, sannan ta zuba a guje ta yi cikin gida. Ta nufi ma'ajiyar kayan Baffa ta lallaɓa ta shige ta kwanta.

   Ihun da Dubu ta yi ba ƙaramin razana Baba Sule ya yi ba da jim kalaman da da aka ce za a ɗauke shi matuƙar ya saki hannun matarsa. Yana daga gefen gado da sauri ya matsa ya kama hannuwan matarsa ya riƙe ƙam, don kar a neme shi a rasa. Cikin bacci Sahura ta fara masifa da yake Allah ya yi ta masifaffiyar macece. Tana jin ya riƙo mata hannu ta ce, "Don Allah sakarni Uban ƴan naniƙa." Da yake bacci ya hau kanta bata kuma tanka masa komai ba.

   Daga ɗaki mai kallon gabas Baba Auwalu ne ya ɗaga labule yana haskowa da fitila zaraf matarsa Yahanasu ta miƙe tana tambayarsa da yake su sabbabun amare ne. Daga can nesa suka hango Inna a yashe tana ko numfashi bata yi. Gabansa ne ya faɗi yace, "Wa nake gani kamar Inna a ƙasa." Sahura ta dafa kafaɗarsa ta ce, "Auwaluna ni ban yarda ita bace kawai magauta ne suka yi maka ture."

    Duk duniya babu abin da Auwalu ya tsana sama da a ɓata ran Yahanasu amma tabbas wannan karon ba zai iya haƙura ya bar Mahaifiyarsa a wannan yanayin ba. Kasancewar dare ne amma bai hana sakar mata murmushi ba ya ce, "Allah shi zai kare ni amma bana tunanin wani zai yi mini ture cikin dare." Kafin ta yi magana tuni Auwalu ya yi gaba, ganin haka ya sa ta ja tinga ta tsaya don har ga Allah a tsorace take musamman da ya kasance ranar ne aka yi rasuwa.

   Hankali a tashe ya fara yayyafawa Inna ruwa ganin ta fara motsi ya sa ya kamata yana bubbuga ƙofar Baba Sule, Baba Sule na ji ya yi fakare kamar mai bacci don gabaɗaya ya gama rikicewa. Sama-sama Sahura ta fara jin bugun ƙofa firgigit ta miƙe sai ji ta yi Sule ya riƙe hannunta gam, tana shirin yin magana Baba Sule ya janyota cikin raɗa ya fara cewa, "Kada ki yi magana za su yi sama da ke" Waigawa Sahura ta yi tana kallon ƙofa don ita a tunaninta masu buga ƙofar ne za su yi sama da ita. Suka ƙarajin bugun ƙofa Auwalu yana cewa, "Yaya Sule fito ka taimaka mini jikin Inna ya yi tsanani ina jin makewayi za ta ta faɗi." Sahura ta ja guntun tsaki ta ce,

  "To! Sai ka tashi tun da ta ka ji muryar Auwalu." Baba sule ya sake ƙasa da murya yanda daga shi sai Sahura ne za su ji abin da yake faɗa ya ce, "Ki koma ki kwanta kawai ina ji a jikina waɗannan ƴan sama jannati ne suka rikiɗa. Takaici ya kama Sahura yanda ta ga Maigidanta yana rawar ɗari ga shi ba lokacin zafi ba, ta miƙe tana fusgar hannu ta ce, "Sakarni ko ƴan ƙasa jannati ne babu abin da zai hanani fita."Tana jan hannu Baba sule yana ja don a tunaninsa muddin ta saki hannunsa shi kenan za su yi sama da shi.

Sororo Sahura ta yi tana kallon ikon Allah, don ita a iya saninta da Sule ba su taɓa irin wannan wasan da shi, don haka ta sake ɓata fusaka ta ce, "Sule wai wani abu ne yake damunka ko gamo ka yi cikin dare n sani ba?" Baba Sule ya yi wura-wura yana kallon hagu da dama ya sake ƙanƙance murya ya ce, "Sahura a kowanne lokaci za a iya yin sama da ni." Wani takaicin ne ya sake rufe ta, ta miƙe tana ƙoƙarin fisge hanunta amma abin ya ci tura don ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya.

   Auwalu da ke jin ƙusur-ƙusur a ɗaki sai ya sungumi Inna don a ganinsa bai kamata ya sake buga ƙofar ɗakin ma'aurata cikin dare ba. Can sashen su Inna Furai ya nufa Yahanasu ta ƙwalla masa kira tana cewa, "Auwaluna ina za ka ni dai tsoro nake ji." Auwalu ya waigo ya ce, "Shiga ɗaki Inna zan kai na dawo."

   Dubu na daga ɗaki tana jin duk abin da yake faruwa, tana jin Baba Auwalu ya tafi ta yi zaraf ta fito cikin sanɗa sai da ta zo daga bakin ƙofar Yahanasu ta yi gyaran murya ta sake kausashe murya irin ta Marigayi mai carbi ta ce, "Wato ita rayuwar barzahu daɗi gare ta ni Mamman. Yanzu tun da na zagayo rayuwata ta baya dole na ɗauki mai ɗakin nan." Cikin Yahanasu ne ya kaɗa nan take jikinta ya hau karkarawa kamar mazari.  Dubu ta yi irin tarin tsofaffin ta sake cewa, "Amma ita Yahanasu za mu ɗaga mata ƙafa sai dole ta bi sharaɗinmu ko ba haka ba ƴan sama jannati?" Dubu ta sake sauya murya ta ce, "Ai dole ma ta bi umarninmu ko yanzu mu faɗa ɗakin." Yahanasu bata san lokacin da ta yi farat ta ce, "Wallahi ku faɗa ko meye zan bi."

  Dubu ta maƙale murya ta ce, "Dole ki zama makauniyar ƙarfi da ya ji muddin kika buɗe idonki sai dai ki wayi gari a ƙiyama." Tun Dubu bata rufe baki ba Yahanasu ta runtse ido biyu ta ce, "Wallahi na rufe har abada ba zan sake buɗe su ba amma don Allah karku cutar da ni."

  Dubu har da ƴar tsawarta ta ce, "Kin tabbata kin rufe ko na aiko da Ƴan sama jannati su shigo?" Yahanasu ta sake runtse idonta tana cewa, "Na rufe wallahi na rufe." Dubu ta saki murmushin mugunta a ƙasan zuciyarta tana cewa, "Yau zan ga ƙaryar soyayya kullin a ishe mu da Auwaluna." A fili Dubu ta ce mata, "Maza tashi tsaye ki rungume bango."  Da sauri Yahanasu ta fara lalaube-lalube har ta taɓo bango.

  A hankali Dubu ta zura kai ta leƙa ta hango Yahanasu na rungumar bango, zuruf ta faɗa ɗakin cikin sanɗa. Sai da ta je daidai wurin Yahanasu sannan ta ɗaga zabgegen Carbin Marigayi ta zabgawa Yahanasu a ƙeya, sai ta fara wani gunji tana cewa, "Gargaɗin yan sama jannati kenan." Tana faɗar haka har ta fice daga cikin ɗakin.

Yahanasu tun da ta gantsare take hawaye a tsaye sai dai ta kasa buɗe idonta saboda tsoron abin da kaje ya zo.

  Duk abin da yake faruwa a kunnen Sahura da Baba Sule, cikin Baba sule ne ya sake ɗurar ruwa. Sahura ita kanta jikinta ya fara sanyi musamman da ta jiyo Ihun Yahanasu, shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta duk masifar da take yi ta daina. Domin da alama zancen Sule ya tabbata.

  Lokacin da Auwalu ya ƙarasa ɗakin Inna Furai, har lokacin bata dawo hayyacinta ba. Yana shiga ya kwantar da ita akan ƙaramin gado, sannan ya fara tashin ƙanwar Mahaifinsu Lantan da ta zo daga garin Zariya. Ganin halin da Inna Furai take ciki ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen ɗakin ya yi ba. Auwalu ya juya zai fita Inna Furai ta riƙo hannunsa ta ce, "Auwalu! Yau na haɗu da zazzagar rayuwa. Don haka ka haɗo mini kawunan ƴan uwanka mazan su da matan su a yanzun nan. Idan ba haka ba wallahi sai na zazzagar da albarkasu kowa ya lalace."

  Auwalu da sauran mutanen ɗakin sun yi tsammanin zafin ciwo ne ya sa Inna Furai take sumbatu. Lantan ta ƙara matsawa kusa da Inna Furai ta ce, "Furaira sanu kin ji Allah sa dai ba akan makarai kika faɗi ba." Wannan magana ba ƙaramin fusata Inna Furai ta yi ba, a zafafe ta ɗago ta ce, "A kan bulikiya na faɗi! Lantan bana son zazzagar wulaƙanci. Kai Auwalu ka tara mini ƴan uwanka a daren wallahi tun ban zazzage albarkar da ke kanka ba." Kamar sabon munafiki haka Auwalu ya fice sum sum sum daga ɗakin. Haka ya rinƙa bi ɗaya bayan ɗaya yana taso su. Wannan tashin da Auwalu yake yi wa ƴan uwansa ne ya sa kusan rabin mutanen gidan suka tashi daɗin daɗawa idan kowa ya ji ance Inna Furai ta faɗi a hanyar banɗaki sai ya wartsake masu tafiya ɗakinta na yi masu jaje suma suna yi.

   Kafin wani lokaci tuni ɗakin Inna Furai ya cika da ƴaƴanta su rai takwas maza biyar mata uku. Sai da ta kalle su ɗaya bayan ɗaya sai kawai suka ga ta ɗaga riga ta ce, "Larai bisimillah"  Larai zuciyar ta ɗaya ta ɗauka Inna Furai so take a ƙarasa cire mata riga, nan take ta fara cikiniyar tuɓe mata riga. Cikin ƙaraji Inna Furai ta fisge tana cewa, "Larai yanzu bijirewa umarnina za ki yi? Ni za ki zazzagewa albarka a ka" Sai ji suka yi Inna Furai ta fashe da matsanancin kuka. Lokaci ɗaya suka kalli juna domin ba su ga abin da zai sa Inna Furai kuka ba. Auwalu ya sunkuyo ya ce, "Inna ki yi hakuri me kike so?"

   Inna Furai ta ɗago mamanta ɗaya ta ce, "Mahaifinku ya zazzage mini albarka ɗazu nan domin daga zuwansa lahira har ya haɗa kai da ƴan sama jannati. Ba zan zazzage maka bayani gabaɗaya ba amma Auwalu ungo sha ka ji."
[7/1, 6:02 PM] My Data sim number: *DUBU JIKAR MAI CARBI*

            ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER'S ASSO...

*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 2

          Auwalu sam bai fahimci inda maganar Inna Furai ta dosa ba, don tun da ya ji ta ambaci Mahaifinsu ya tabbatar da zafin ciwo ne yake damunta da kiɗimewar rashin da aka yi musu. Saboda gudun faɗanta ya sa ya wayance da cewa, "Inna ban fahimci abin da kike faɗa ba. Amma kuma duk wanda ya mutu kin san sai dai mu bishi da addu'a ita ce mafita." Inna ta yi ƙuri tana kallonsa sai zuwan can kawai ta fashe da kuka. Lantan da ke gefe takaici da baƙin ciki gabaɗaya suka turniƙe ta, don gani take kamar har da biyu Inna Furai take lanjarewa. Kasa haƙuri ta yi ta ce: "Furaira don Allah ki shafa mana lafiya ki bar mu, mu ji da abin da yake damunmu. Haka kawai ki tayar mana da balli a tsakiyar dare akanki aka fara mutuwar miji? Ko kuma ke kaɗai kika san zafin miji muna zaune ki ishe mu da zancen fatalwa. Ki barni na kwanta na yi baccin da ban samu na yi shi jiya ba."

Inna Furai  ta fyace majina da gefen zaninta ta waiga ta ce, "Wallahi babu ƙatuwar Matar da za ta zo mini ɗaki ta nemi kawo mini zazzagar albarka ido biyu. Idan ba za ki iya ba ki tashi ki fice dama ni bana gayyar tsintsinya da bulugari, bare kuma mafici abin banza."  Lantan jin maganar Inna Furai ta yi kamar ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta zaburo a hasaale ta ce, "Ban da ƙaddara da rashin ɗan'uwana da na yi,  me zai kawo ni ɗakinki kaico Allah ya jiƙanka Yaya Mamman. Wai yau jininka ake wulaƙantawa saboda ƙasa ta rufe mata ido, kai jama'a ɗan'adam butulu. Wanne irin karamci ne Ɗan'uwana bai yi miki ba?"

Inna Furai ta jingina da ƙarfen gado sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, tana yi tana fatar majina. Abin duniya goma da ashirin ne damu su Auwalu, don haka kowa ya yi jim! Babu wanda ya iya tofa magana ɗaya sai gani suka yi Inna Furai ta fara haɗa ƴan kayayyakinta na sawa da ke kan gado. Sabi'u ya ce: "Inna lafiya kuwa wai me yake faruwa ne  kike haɗa kaya?"

  Inna Furai ta juyo a fusace ta ce, "Zaman ku a nan bai amfane ni da komai ba.  Kuna gani ta gama zazzage mini rashin mutumci a ka babu wanda ya tanka mata. Wallahi ko ku bi mini haƙƙin zazzagar albarkar da ta yi mini a ka ko kuma yanzu na fice na baku wuri ku yi yanda kuke so. Gara ni tawagar Malam da ƴan sama jannati ta zo ta ɗauke ni ko kowa ya huta, dama na kiraku ne domin mu kashe mu binne amma da alama ku dai ba ƴan goyo ba ne, don na lura za ku iya zazzage mini sauran albarka da ta rage mini a kaina.

Gabaɗaya shiru suka yi suna nazarin abin da yake damun Mahaifiyarsu, don rikici sun san Mahaifiyarsu mace ce mai matuƙar rikici amma wannan karon gani suke har da mutuwar mahaifinsu da ta taɓa ta.

  Lantan na gama sauraron Inna Furai ta miƙe tsaye tana shartar ƙwalla, ɗan ƙullin kayanta da ke ƙarƙarashin gado ta janyo ta fara kiciniyar ɗorawa a ka tana matsalar hawaye. Da sauri Auwalu ya miƙe ya riƙe kayan yana cewa, "Inna Lantana don Allah ina za ki a tsohon daren nan?" Lantan ta kunto mayafinta ta yafa a kanta ta ce, "Auwalu don Allah karka kawo mini maganar da za ta tunzurani har ta kai ga na nemi shaƙe wannan tsohuwar har lahira. Duk irin cin mutumcin da ta yi mini a gabanku baku gani ba za ka taso tsalo-tsalo kana tambayata ka bar ni yau ko ƙasa da sama za ta haɗe ba zan kwana a gidan nan ba."

Nan fa hayaniya ta fara ta shi a cikin gidan, Inna Furai na gama saurarar maganar Lantan ta sa hannu bibbiyu ta dafe ƙirji a razane tana zare idanu kamar wacce ta yi tozali da kumurcin maciji. Bata tanka musu komai ba sai gani suka yi ta sauko ƙasa daidai wurin da Lantan take tsaye ta fashe da kuka haɗe ta rungumo ƙafafuwan Lantan tsam a jikinta. Tana cikin kuka ta ɗaga kai ta dubi Lantan tana cewa, "Wallahi ba za ki bar ɗaƙin nan ba sai kin zazzage ragowar numfashin da nake shaƙa, Lantan yau ni kike muradin kashewa a gaban ƴaƴana. Ai kuwa ko ba yanzu na mutu ba na rataya a wuyanki Kai Auwalu ku shaida haka."

  Inna Furai ta juya ga su Auwalu tana musu mugun kallo ta ce, "Allah na tuba wacce uwar na haɗa da su bayan alaƙar haihuwa? Da su Auwalu da Sabi'u kuma ni kam gara ma a ce ban da kowa tun da babu mai tare mini faɗa a gidan nan. Har ana niyyar halakani da sauran rayuwa kai jama'a Lantan an ya kina tsoron Allah kuwa? Duk wanda ya kashe wani dai wuta za shi."

  Lantan ta yi tsalle can gefe abin ka da da marar  jiki, can gefen babban gado ta matsa tana cewa, "Laƙadi ja'akum... Tuf! Aniyarki ta faɗa kanki karki ja mini masifa ki maƙala mini sharrin kisan kai ina zaune ƙalau." A wannan karon Inna Furai bata tanka mata ba sai gani suka yi zaraf ta fice daga ɗakin, da sauri iyalanta suka bi bayanta suna roƙon ta dawo ɗaki saboda dare.

  Tana fita ita ma Lantan ta sa ƙafa ta fito ganin haka ba ƙaramin ɗaga hankalin su Auwalu ya yi ba, musamman shi da yana tsaye a nan ne amma zuciyarsa na wurin Yahanasu yana tunanin halin da take ciki. Inna Furai na ganin Lantan ta fito ta bita jiki a sanyaye kamar kazar da ake jefa da gishiri ta ruƙo hannunta sannan ta fashe da kuka. Ita ma Lantan zuciyarta ce ta karye sai kawai ta fashe da kuka, sai da suka yi mai isarsu sannan Inna Furai ta ce, "Yanzu Lantan da na barki tafiya za ki yi a daren nan?" Lantan ta fyace majina a haɓar zaninta ta ce, "Ina zan iya tafiya na barki Furai kina cikin jimamin rashin miji, Furaira rashin miji tashin hankali ne har kin tuno mini da rasuwar Mahaifinsu Ɗan'iya kai rayuwa babu tabbas Allah ya jiƙanka Malam Mudassiru." Lantan ta rushe da matsanancin kuka. Rabe ya matso da niyyar rarrashinsu Inna Furai ta doke hannunsa tana cewa, "Allah wadaran naka ya lalace. Wallahi kaf gidan nan banga wanda zai hanani zazzage muku albarka ba. Wai kamar yanda Lantan take a wurina ta tashi za ta tafi cikin dare amma babu mutum ɗaya da zai hanata tafiya kaico! Wallahi kun ji jiki ƴan bakinciki bantaɓa sanin bakwa ƙaunar aminiyata ba kuma ƙanwar Mahaifinku ba sai yau."Inna Furai na gama maganar ta ja hannun Lantan suka bar su Auwalu a tsaye sake da baki.

Ba su da zaɓi haka suma suka bi su Inna Furai ciki, cikin ƙaguwa Auwalu ya ce, "Inna za mu iya tafiya yanzu?"

Inna Furai ta saki salati ta na kallon Auwalu da wani yanayi har sai da ya tsargu ya ɗan fara sosa ƙeya sannan Inna Furai ta ce, "Wallahi kai dai Auwalu na riga da na san matsayina a wurinka. Tun mahaifinka na raye har ya mutu ban taɓa musa wa maganarsa ba, sai yau don ƙasa ta rufe masa ido?" Ta fashe da kuka tana ci-gaba da cewa, "Ban shirya mutuwa da shiga jahanna ba. Sharaɗi fatalwar mahaifinku ta bani sai na shayar da ku mama kamar yanda na shayar da ku kuna yara, kuma ban ga wanda zai hanani bin umarninsa ba."

  Lokaci ɗaya suka ɗauki salati gabaɗaya saboda ta'ajibin jin maganar Mahaifiyarsu, Larai cikin matsananciyar damuwa ta ce, "Inna kin san me kike faɗa kuwa? Yanzu kina nufin Baba ne ya yi miki fatalwa? Inna don Allah kar wani abu ya ruɗe ki ko ya tsorata ki saboda wanda ya mutu ya mutu kenan ba zai ƙara dawowa ba. Sai dai idan shaiɗan ne yake son razanar..."

A hassale Inna Furai ta katse Larai da cewar, "A'uzubillahi minasshaɗanirrajim. Ba zan ga shaiɗan da idona ba Larai kafirta ni kike son yi da za ki haɗa ni da Shaiɗan la'anannan Allah?" Larai rasa hanyar da za ta ɓullowa Mahaifiyarta ta yi don gabaɗaya sun rasa gane kanta. Lantan da ke gefe ta kalli Larai ta ce, "Wallahi ki tubar wa Allah idan ba haka ba, azabar Allah tuni za ta yi fata-fata da ke. Kuma ni gani nake maganar Furaira tana kan hanya don ni kaina lokacin da Malam Mudassiru ya rasu har gizo ya riƙa yi mini a tsakar ɗaki. Don haka ku yi biyayya idan ba haka ba duk cikinku babu mai kaucewa azabar Ubangiji, musamman kai Rabe da ka fi tsoka wallahi tuni wuta za ta tsotse namanka ka lalace a jahannama."

Ganin wannan lamarin yana ƙoƙarin zama babba ya sa Auwalu ya zame jikinsa ya je Shagon Soro ya taso Yayan mahaifinsu ya sanar da shi halin da ake ciki. Har ɗakin Inna Furai ya shiga yana shiga ya same ta, ta yashe riga a sama tana kumfar bakin Larai ta tsugunna ta fara karɓa tun da sauran mazan taurin kai za su nuna mata. Da sauri ya ɗauke kansa gefe don bai yi tsammanin abin da suka faɗa da gaske ba ne. Nan take ya shiga yi mata nasiha amma duk da haka Inna Furai ta shafawa idonta toka ganin haka ya sa ya fara lallashin ta bari zuwa safiya sai a san abin yi. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu shawo kan Inna Furai ta haƙura zuwa safiya sannan kowa ya kama gabansa. Bayan tafiyarsu Lantan ta zabga uban tagumi sannan ta ce, "Yanzu Furaira da idanunki biyu kika yi tozali da Yaya Mamman ni fa ɗazu ƙarya na kirfo da na ce ina ganin Fatalwar Mudassiru, saboda yaran nan sai su raina mu ni kuma a duniya babu abin da na ƙi jini irin raini."

  Inna Furai ta miƙawa Lantan hannu ta ce, "Lantan taɓa ni na ji." Da sauri Lantan ta kai hannu tana shafa hannunta. Inna Furai ta mirtsika ido ta ce, "Billahilazi idan har wannan taɓawar da kika yi mini mafarki ce to a mafarki na ga Malam. Wallahi da idanuna na ganshi a wurin zaman alwalarsa amma tun da baku yadda ba nan gaba na kuma ganinsa nasa ya fitowa kowa a zahiri."  Kamar wacce aka tsamo daga ruwan sanyi haka jikin Lantan ya yi sanyi ta rasa abin faɗa don hantar cikinta ta fara kaɗawa musamman da ta san Inna Furai ba ta yin rantsuwa sai da ƙwaƙƙwaran dalili. Kwanciya suka yi sai dai kowa da abin da yake wassafawa a cikin zuciyarsa.

Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,

"Yahanasu lafiya kuwa?" Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, "Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni." Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, "Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?" Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, "Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona." Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, "Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa." Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata.

  Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.

   Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.

  Washegari.

  Jama'ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko'ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.

   Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, "Ina za ki tafi ki bar ni?" Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, "Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba." Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, "Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba." Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, "Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?" (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa  ta zo ƙarshe.

  Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, "Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka." Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, "Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni."  Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita.

Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan  Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.

  Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.

  Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaɗaya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa'azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.

Inna Fuarai ta karkace ta ce, "Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi." Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, "Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare." Auwalu ya rumgumota yana cewa, "Ba za ki mutu ba Yahanasuna" Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, "Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin.

  Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taɓa kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce ɗakin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma'a da su. A wanke suke a goge fari ƙal da su, sai da ta bubbuɗa su ta je bakin katangar banɗaki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saƙale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake ɗanawa wuta tana cewa, "Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da ɗankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige ɗakin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faɗuwa can bakin ƙofa.
[7/11, 7:44 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 5

     Fuskar Mama Uwani ce ta rune saboda ɓacin rai nan take ta fara fesar da numfashi mai ɗauke da turirin hayaƙi mai zafi, sannu a hankali Hannuwanta suka fara fidda wasu irin baƙaƙen farata masu matuƙar kaifin gaske, harshenta ne ya fara zazzagowa haɗe da fidda waɗansu irin jeluna masu tsawo da santsi tamkar ƴaƴan maciji, fatar jikinta ce ta fara sauya launi zuwa kalar ja haɗe da wani gashi da ya fara tsattsafo mata. Cikin wata irin murya mara daɗin sauraro ta fara magana.

"Wace ce ke?" Intisar ta saki malalacin murmushi ta fara zagaye ɗakin tana ƙarewa Mama Uwani da ke ɗauke da mummunar siffa ta ce, "Menene damuwarka har kake son sanin ni wacece? Dama ka yi abin da yake gabanka don sanin wacece ni ba zai amfane ka da komai ba." A haukace Mama Uwani ta buga uban tsalle da waɗansu manyan fuka-fukai da suka fito daga ƙasan hammarta, ta dira a gaban Intisar haɗe da karta mata faratanta bisa tsautsayi farcen ɗan yatsanta ɗaya ya karci gefen fuskarta. A zafafe ta matsa baya cikin huci, nan take fatar jikinta ta fara darewa tsokar namanta ta fara bayyana  a fili, kanta ya fara rabewa gida biyu wani dogon ƙaho ta fara tsorowa daga tsakiyar kanta. Tana shirin mayar da martani daga can bakin ƙofa suka ji maganar Mommy na ƙwalawa Mama Uwani kira, kamar ƙiftawar ido tuni suka koma hallitarsu ta ainihi. Mama Uwani ta zubawa Intisar wani mugun kallo cike da takaici ta furta, "Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za a haɗu."

Intisar ta ɗaga kafaɗa cikin rashin nuna damuwa ta ce, "Kamar yadda Ungozoma ke jiran mai naƙuda haka koyaushe nake dakon haɗuwarmu domin nasan ba a dauwama da kashi a ciki." Dire zancen Intisar ya yi daidai da shigowar Mommy cikin ɗakin wasu baƙin mata na biye da ita, kallon Mama Uwani ta yi a ɗan faɗace ta fara faɗin, "Mama Uwani kina ji ina ta magana lafiyarki kuwa?" Kamar yadda ta saba ladabi a gaban su Mommy haka Mama Uwani ta dausashe murya ta ce, "Hajiya a yi haƙuri yanzu na zo wuce wa na hangi wannan baƙuwar ta shigo ɗakin nan shi ne na shigo don na sanar mata cikin gida ake zaman makokin, wallahi na sha'afa ban ji ki ba." Mommy ta faɗaɗa murmushi tana kallon Intisar ta ce, "Ƴanmata sannu da zuwa." A kunyace Intisar ta sunne kai haɗe da tsugunnawa har ƙasa tana faɗin, "Mommy ina kwana?" Mommy ta dafa kafaɗarta tana ɗago ta, ta c: "Lafita ƙalau 'yata tashi tsaye." Intisar ta amsa da, "Mommy ina Raihan?" A firgice Mama Uwani ta ɗago cikin suɓutar baki ta furta, "Me Raihan za ta yi miki?"

Da sauri Mommy ta kalli Mama Uwani fuska babu walwala ta ce, "Mama Uwani ya haka ne?" Mama Uwani ranta ya sake ɓaci, ta russunar da kai tana faɗin, "Ayi haƙuri Hajiya." Mommy bata tanka mata ba, ta juya wurin baƙin da take tafe da su ta ce, "Ga baƙi nan ki wuce da su sashenku." Ta juya wurin Intisar ta ce, "Ni kamar Intisar nake gani." Intisar ta sosa kai a kunyace ta ce, "Ni ce Mommy, dama na ji abin da ya faru ne na zo in yi mata gaisuwa." Mommy ta sake goge hawayen fuskarta da yake zuba, don mutuwar Mama Hasiya ba ƙaramin dukanta ta yi ba, ta riƙo hannun Intisar don dama tun da ta ganta take yi mata kallon sani, abin da ya hanata gane ta sau ɗaya ta taɓa ganin wani zuwa da suka yi da Raihan. Intisar ta sake lafewa a jikin Mommy suka nufi hanyar fita, Mommy tana faɗin, "Allah sarki Intisar, ya su mommynku." Intisar ta ce, "Duk lafiya ƙalau ta ce a yi muku gaisuwa kafin ta shigo." Mama Uwani jiki a saluɓe ta ja baƙin suka nufi sashensu, Intisar tana tafe tana sakin wani shu'umin murmushi haɗe da bankawa Mommy harara a fakaice.

  Wuce mutane suka rinƙa yi duk in da ta keta sai gaisuwa ake yi mata, mommy har lokacin hawaye ne ɗauke a fuskarta. Suna zuwa ta wuce da ita sashen Raihan, Raihan na zaune da su Batula ƴaƴan ƙanne da yayyan mommy, suma ƴan mata ne kuma ta su ta zo ɗaya da Raihan.

Intisar na shiga Raihan ta faɗaɗa fara'arta tana miƙa mata hannu daga zaune, da sauri Intisar ta rungumeta tana faɗin; "Besti ya ƙarin haƙuri." Idanun Raihan ya ciko da ƙwallah, sai da ta sa hannu ta goge hawaye cikin shassheƙar kuka ta ce, "Besti wai Mama Hasiya ce ta mutu, idan kin tuna hirarmu da ke last ba nace miki ni na ɗauki alƙawarin Baby shower ba idan ta samu Ciki?" Intisar ta matso hawaye cikin sigar tausayi ta furta, "Kayya Besti ya za a yi na manta da hirar Mama Hasiya." Raihan ta ci gaba da kuka tana faɗin, "Intisar Mama Hasiya na sona kamar ita ta haife ni, wai ita ce ta mutu shi kenan mun rasata." Kamar haɗin baki lokaci ɗaya suka fashe da kuka mai ban tausayi, sai da ƙyar aka lallashe su musamman Raihan.

Bayan wani lokaci suna zaune tuni an sallaci Mama Hasiya an kaita makancinta, Mama Uwani ce ta turo ƙofar ta shiga saboda gabaɗaya zuciyarta ba ta aminta da Intisar ba, don tun ranar da ta fara ɗora ido a kanta ta fahimci ita ba alheri bace a rayuwar Raihan. Sai dai duk yadda ta so bin diddigin gano wacece ita abin ya faskara, don haka ko da ta shiga ɗakin sai ta hau goge-goge don ganin abin da yake faruwa. Intisar na ganin haka ta saki murmushi a fakaice don ta san tsiyar da za ta shukawa Mama Uwani, yamutsa fuska Intisar ta yi ta ce, "Besti pls ki ce Mama Uwani ba ni ruwa and takalmana suna waje ta kwasominsu." A hargitse Mama Uwani ta wurgawa Intisar mugun kallo saboda ɓacin rai har sai da ta so bayyana fushinta a fili, kai tsaye Raihan ta dubi Mama Uwani ta ce, "Mama Uwani ki ɗaukowa Intisar ruwa a falo na firij ɗina ya ƙare." Ganin rainin hankalin Intisar ya yi wa Mama Uwani yawa ya sa bata tanka wa Raihan ba ta  kalli Intisar, ta fara wani huci idanunta suka fara sauya lauyi ba tare da Raihan da sauran mutanen ɗakin sun lura ba.

Kofar toilet ɗin Raihan ta kalla lokaci ɗaya kofar ta buɗe da ƙarfi, wani tafkeken maciji ne ya fara silalowa bakinsa na fidda baƙin hayaƙi. Wata uwar ƙara suka ƙwalla a firgice kowa ya fara neman hanyar fita, kafin wani lokaci tuni duk sun fice daga ɗakin har Intisar don ko kaɗan bata yinƙurin yin wani abu a gaban Raihan da zai bayyana ita ainihin wacece.

    Mama Uwani nan take ta ɓace a wurin, macijin ra rabu gida biyu ɗaya ya rikiɗa zuwa siffar Raihan ɗaya kuma yana nan a siffarsa ta farko,  ita kuma Mama Uwani ta ɓace tare da Raihan ɗin ainihi. Kamar ƙiftawar ido haka Mama Uwani ta ɗira a wani tsibiri mai ɗauke da dogayen bishiyu masu duhun gaske, sai wasu korayen tsuntsaye masu yawan da wasu hallitu masu siffar ƙadangaru sai dai jelunar su gashi gare ta kamar jelar tunkiya. Raihan da take sume ta shimfiɗar, Mama Uwani ta zauna ta zura mata ido, nan take  ta rikiɗa zuwa surarta ta ainihi wato HUZAIFA. Miƙewa ya yi da surar wata ƙatuwar hallita mai matuƙar tsawo, fatar jikinsa kamar bayan kada ga wata zabgegiyar jela a bayansa mai ɗauke da kawunan macizai masu fidda aman wuta. Hannuwansa ɗauke suke da manyan farata sai harshensa da suke dalalar da wani baƙin ruwa mai yauƙi.

Kamar wancen karan da ya kaita daularsa ta ƙarƙashin ƙasa, a yanzu ma zuwa ya yi daidai wurin da take kwance ya zuba mata ido wata matsananciyar sha'awar Raihan na sake fisgarsa. A hankali Raihan ta sauke ajiyar zuciya sanyin shukokin wurin ya fara dukan gangar jikinta, motsi ta fara yi alamar za ta farfaɗo. Ruwan bakinsa ya ɗiga mata a saitin goshinta, a cen gefe ya je ya ɗauko wannan ƙaramar hallitar mai siffar kunkuru ya ɗagata da hannuwa biyu yana kallo yana jin daɗi, domin babu abin da ya fi saurin faranta ransa sama da ya ga ya haɗa Raihan da abin da ta haifa masa. Mayar da jaririn hallitar ya yi sannan ya dawo kan Raihan da ke kwance, a hankali ya fara mu'amala da ita yana sarrafa sassan jikinta ga wata irin kewarta da ya yi don ya jima bai kusance ta ba, tun ranar da ta haifi wannan mumummunar hallitar tun da ba ya iya ɗaukan kwana biyu cir ba tare da ya kusance ta har ya yi mu'amala da sassan jikinta ba.

   Yana tsaka da mu'amala da ita ya ji wata iska ta fara, kaɗawa mai tafe da sarewa. A hankali ya ɗago kansa yana  kallon abin da yake faruwa don ko ba a faɗa ba, ya san Mugaza ce za ta dira a wurinsu. Tun bai gama tunaninta ba ya ji kecewar dariyarta a tsakar kansa, miƙewa ya yi daga kan Raihan a lokacin ya bayan ya samu nutsuwa da ita, ya taka wurin Mugaza fuska a haɗe cikin wata irin murya ya furta, "Me ya kawo ki Turakata bayan kinsan hutawa nake yi?" Haushi ne ya sake rufe Mugaza da ke ɗauke da surar wani ƙaton tsuntsu mai kan angulu. Sai da ta yi tsalle-tsallenta sannan ta dira a gabansa rai a ɓace ta mayar masa da martani, "Akwai wani hutu da ya dace ka yi bayan bana kusa da kai?" Huzaifa ya ƙare mata kallo yana shirin magana ta ci gaba da cewa, "Sau nawa zan gaya maka ka fita daga rayuwar yarinyar nan, idan ba haka ba wallahi sai na halakata ta hanyar kisa mai muni." Wani uban tsalle ya buga haɗe da girgiza sannan ya rikiɗa zuwa surar matashin saurayin bil'adam, ya kalli matarsa Mugaza tare da sakin wani shu'umin murmushi ya ce, "Wannan yarinyar da kike gani na fansar da raina a gareta idan kin ga ban tsayawa rayuwarta ba sai dai bana numfashi, ita ɗin ta zama jinin jikina ko iyayen da suka haifeta idan suka nemi raba ni da ita sai na tarwatsa rayuwarsu." Jinjina kai Mugaza ta yi haɗe da sakin wata irin shu'umar dariya sannan ta ce, "Wannan shi ne gargaɗi na ƙarshe da na yi maka a kanta, tun da baka ji ba za ka ga ni a gaba kuma idan kwaɓarka ta yi ruwa karka yi kuka da ni. Sai dai zan ci gaba da baka kulawa a matsayina na matarka mai ƙaunarka, amma a kan wannan yarinyar babu wata kalma da za ta sake shiga tsakaninmu. Sai na ladaftar da ruhinta ta yadda za ta yi danasani, sai na azabtar da gangar jikinta domin sai na shayar da ita azaba mai raɗadi" Tana gama maganar ta tashi daga cikin tsibirin ta fice, ko a jikin Huzaifa ya ƙarasa wurin da Raihan take kwance ya sake rikiɗa zuwa siffar marigayya Mama Hasiya haɗe da sauya fasalin wurin, a hankali ya sa hannu ya fara tashinta tare da faɗin sunanta. Ahankali ta buɗe idonta tana kallon wurin da take da Mama Hasiya da take kanta a tsaye.

Bayan fitowar su Intisar a kan idonta Mama Uwani ta sauya Raihan da wata Raihan ɗin, murmushi ta yi don ta fahimci manufarta na yin haka kuma ita ma ta shiga nazartar yadda za ta ɓullo mata. Nan take gida ya ruɗe da maganar macijin da aka gani a ɗakin Raihan, hankulan mutane ba ƙaramin tashi ya yi ba. Lokacin da Mommy ta samu wannan labarin da sauri ta aika aka kira Kabiru (Matashin bafulatani Maigadin gidansu Raihan.)  Saboda Kabir bai da tsoro sam, bai fi sati biyu da fara aiki a gidansu Raihan ba. Tsayayyen namiji ne mara tsoro don akwai ranar da aka samun kulɓa a kitchen ɗin Mommy, Kabiru na zuwa ya fitar da shi. Kafin Kabiru ya zo Sulaiman ɗan ƙawar Mommy ya miƙe yana faɗin, "Daga wurin ina yake yanzu na fice da shi, ba wani shege kura ma mun kara da ita mun kaita ƙasa." Babu wanda ya hana shi don jikinsa na rawa ya nufi cikin gidan, saboda yana mutuwar ƙaunar Raihan don haka yake son ya yi wani abin bajinta ko ya samu ya ƙara samun masauki a zuciyar Raihan.

Yana zuwa duk matan da ke zagaye da ɗakin suka dare, ya tura ɗakin da ƙarfinsa. Yana shiga ya samu macijin a tsakiyar ɗakin ya naɗe wuri ɗaya kamar gammo ya fasa kai, bakinsa yana fitar da feshin wuta, a hankali ya waiga yana faɗin: "Wani ya miƙo min katako." Har rige-rigen tafiya mutane suke yi babu jimawa aka ɗauko masa wani ƙaton katako, kansa tsaye ya tunkari macijin cikin dakiya ya ɗaga ya buga masa a tsakiyar ka. Tsalle macijin ya yi, Sulaiman ya gantsare duniyar na juya masa. Sannu a hankali macijin ya rarrafo ya fara nannaɗe shi har sai da ya naɗe masa jiki, nan take Sulaiman ya hau kakari ƙwayar idonsa duka biyun ta faɗo ƙasa, jini ya fara zuba ta hancinsa da bakinsa. Tun Sulaiman yana iya kakari har ƙarfinsa ya ƙare, tsokar jikinsa ta fara burtsowa daga jikin fatarsa nan take hallitar Sulaiman ta sauya tamkar ba bil'adam ba. Mutane na ganin haka suka fita da gudu cikin kururuwar neman taimako.

             ************

   Raihan ta shi ta yi zaune jikinta ba ƙaramin tsami ya yi mata ba, ta dubi Huzaifa da ke cikin siffar Mama Hasiya ta ce, "Mama Hasiya kece? Dama baki mutu ba?" Huzaifa ya gyaɗa wa Raihan kai yana furta, "Ban mutu ba amma na dawo nan wurin da zama za ki zauna da ni?" Raihan ta yi shiru tana nazartar maganarsa jiki a sanyaye ta ɗago tana cewa, "Gaskiya ban yarda ba ina su Mommy?" Huzaifa ya riƙo hannunta lokaci ɗaya ta ji wani yaarrr a cikin jikinta, tana kiciniyar ƙwacewa sai gani ta yi ta fisgo da ƴan yatsu biyu na jikin hannun Huzaifa, a tsorace ta wurgar da su ta fara ja da baya jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya ta ce, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni." Ganin haka ya sa Huzaifa ya fara ƙyaƙyacewa da wata irin dariya har sai da ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnuwanta, kakin yawu ya yi ya tofar nan take ƙasar wurin ta fara rozayewa ya sa ɗan yatsa ya nuna mata wurin yana faɗin, "Ki bar wahalar da kanki domin ba za ki taɓa guje min ba, ki zo ki shiga wurin nan idan ba haka ba za ki dauwama a wurin nan."

       *********

     Al'ummar da ke zaman makoki kusan rabi da kwata kowa ya cika wandonsa da isa, don ceton rayuwarsa. Hatta Inno da Goggo cikin ayarin ƴan ceton rai suke ba tare da su mommy sun farga ba. Hankalin Daddy ba ƙaramin tashi ya yi ba da ganin abin da ya faru, a hankali Kabiru ya fara takawa cikin gidan dukda yana ta cin karo da mutane masu guduwa hakan bai hana shi sake kutsawa cikin falon gidan da zai sadaka da ɗakin Raihan ba, a bakin wata ƙofa ya ci karo da Intisar da ke tsaye ƙyam babu alamar tsoro a tattare da ita. Suna haɗa ido ya ji kansa ya sara juwa ta fara ɗibansa, sama-sama ya fara jin wata irin hayaniya har sai da ya dafa kansa da hannuwansa, a hankali ya fara karanto addu'o'in tsari yana karantawa duk wacce ta zo bakinsa. Lokaci ɗaya ya ji komai ya ɗauke masa, ya dawo cikin hankalinsa sai dai tuni jikinsa ya jiƙe da gumi sharkaf. Idanu ya kafe Intisar da su har ya gagara sarrafa kansa, ya fara takawa zuwa gabanta cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba ya ce, "Washeshe kai?" Intisar ta saki murmushi ta ƙarasa gaban Kabiru ta ce, "Kai bafulatanin ƙauye, karka shiga abin da babu ruwanka." Yana shirin sake magana Daddy ya ƙaraso wurin hankali a tashe yana faɗin, "Kabiru mu je ka ga abin da yake faruwa meye abin yi?"  Kabiru ya yi gaba yana waiwayen Intisar haɗe da ɗora mata zarge-zarge a kanta.

Da ƙarfin gaske Kabiru ya tura ƙofar ɗakin cikin zuciyarsa yana ci gaba da karanta ayoyin tsari dana kariya, Jabun Raihan ce ta ƙaraso ƙofar ɗakin. Abin da ya ji da farko a lokacin da yake tare da Intisar haka ya ƙara ji a wannan karon a haukace ya juya, ya shaƙi wuyan Raihan cikin wani irin ƙaraji ya furta.

"Washeshe kai? Me kake yi a wurin nan?"

DA ALAMA KABIRU YA YANKI TIKITIN BARIN AIKIN GADIN DA YAKE YI A GIDANSU RAIHAN😂 TO WAI SHI MA KO YANA DA ALAƘA DA SU NE😂  SHIN DADDY ZAI ZURA IDO YA GA AN MAƘURE GUDAN JININSA? SHIN SU DADDY ZA SU FARGA DA MAMA UWANI BA MUTUM BACE SHI NE AINIHIN ALJANIN DA KE RAYUWA DA ƳAR'SU? KO KUMA HUZAIFA ZAI ƘYALE KABIRU HAR YA TONA MUSU ASIRI🤭🤭🤭

TAFIYAR FA HAR YANZU BA A FARA BA DOMIN LABARIN TAFE YAKE DA SARƘAƘIYA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️  KARKU MANTA HAR YANZU RAIHAN BATA SAN MAMA UWANI CE TA KAWO WANNAN TSIBIRIN BA, ITA DAI TA BUƊI IDO DA MARIGAYYA MAMA HASIYA. WAI INA LABARIN INNO DA GOGGO NE INA SUKA BAZAMA WAYE ZAI TARO SU? 😂😂

Share Fisabillah🌚
[7/12, 10:15 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 6

   Raihan kallon ramin ta yi da yake ci gaba da rozayewa ƙasar wurin na ruftawa, ya yin da ramin yake ci gaba da ƙara girma yana tunkaro wurin da take. A hankali ta riƙa ja da baya cikin rawar jiki, firgici da tashin hankali. Tuni hawaye ya wanke fuskarta ta ci gaba da yin baya ba tare da ta fahimci wurin da take jefa ƙafarta ba, bata yi aune ba ta ji wani dutse ya tokareta ƙasar da ke zaftarewa ta ƙaraso har wurinta har sai da ya rage bai fi taku ɗaya ba ta dakata bisa bin umarnin Huzaifa da ke cikin surar Mama Hasiya. Cikin kuka Raihan ta dubi shi tana faɗin, "Don Allah ki yi haƙuri karki cutar da ni, ban san abin da na yi miki ba kika kawo ni wurin nan alhalin mommy ta ce mini kin mutu." Huzaifa ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya ya fara takowa wurinta yana tafe yana zare sauran ƴan yatsun hannunsa yana zubarwa, kafin ya ƙarasa wurinta tuni ya tsinke yatsun hannunsa sai iya dungulmin kaɗai ya rage, daga guraben ƴan yatsun wasu baƙaƙen farata ne suka fara tsirowa a hankali har sai da suka fito zaƙwa-zaƙwa da su, ta cikin ramin ya shiga kamar ƙiftawar ido ya dira a gabanta cikin wata irin murya mai amsa kuwwa ya sake ce mata. "Ki biyo ni cikin ramin nan idan ba haka ba za ki dauwama a nan." Raihan ta sake girgiza masa kai tana cewa, "Don Allah ki mayar da ni wurin su Mommy." Baki ya buɗe zai fara dariya wasu dogayen fiƙoƙi suka fara fitowa, da sauri Raihan ta runtse ido tana ƙwallah wata razananniyar ƙara. Wata iska ta ji mai sanyi na ratsa jikinta a hankali ta buɗe idonta, ga mamakinta sai na yi ta yi wurin ya sauya mata ta ganta wani kogon dutse mai ɗauke da ƙananan bishiyu, a hankali ta fara takawa har zuwa bakin kogon dutsen don ta hango hasken rana daga bakin dutsen. Tana fita daga cikin dutsen ta fara gudu da iya ƙarfinta don ganin ta ceci rayuwarta.

   Daga nesa-nesa ta fara jiyo kukan jarirai haɗe da haniniyar doki, a hankali ta fara rage gudunta don yadda ta lura hanyar da take tunkara a nan take jin sautin kukan jaririn na sake karaɗe kunnuwanta. Tana tafe tana waiwaye ta bata yi aune ba ta ji ta yi karo da wata murgujejejiyar hallita, hallitar riƙe take da wasu ƙananan jarirai masu surarta, tsayin hallitarta ya ninka ta sau biyu, tana da ƙiba sosai don kaurin cinyar hallitar ya yi kaurin Raihan sau huɗu. Tana ɗauke ƙafa da hannuwa irin na birrai sai ƙaton kai irin na dorinar ruwa. Bakinta tsayi gare shi idanunta kwala-kwala masu ɗauke da launin ja, Raihan na shirin ja da baya Hallitar ta ƙurawa Raihan Ido tana miƙa mata hannu alamar ta zo gare ta. Da gudu Raihan ta juya don ta koma cikin kogon dutsen, karaf ta ji ta yi karo da Hazaifa da ke ɗauke da surar Mama Hasiya sai dai kammanina sun sake munana.

Ajiyar zuciya ta sauke don ko ba komai ta ji daɗin ganinsa, hankalinta ya fi kawanciya da shi a kan na wannan mummunar hallitar. Hallitar na ganin Huzaifa ya ɗauke Raihan sun koma zuwa kogon dutsen ta juya ta koma daga wurin da ta fita, Huzaifa ya saki malalacin murmushi bayan sun koma ciki ya zaunar da Raihan akan wani faffaɗan dutse, ya zauna a gabanta yana kallonta. Tana shirin yin magana ya katseta da cewar, "Kina son komawa gida?" Da sauri Raihan ta gyaɗa masa kai. Jinjina kai ya yi sannan ya ce, "Zan mayar da ke gida amma da sharaɗin..." Da sauri ta katse shi da cewar, "Na amince da kowanne sharaɗinki indai za ki mayar da ni gida."

Wannan jaririn hallitar ya ɗauko mata mai shige da siffar kunkuru ya ce, "Ya zama wajibi ki shayar da wannan domin shi ɗin jininki ne." Idanunta ne suka firfito waje ta ƙarewa hallitar kallo tana yamutsa fuska, bai saurari abin da za ta faɗa ba ya ci gaba da cewa. "Ya zama wajibi ki yanke alaƙarki da wannan yarinyar Intisar." A hargitse Raihan ta sake ɗagowa ta yi tana kallonsa don a duniya bata da aminiya sama da Intisar, bata da wacce tasu ta zo ɗaya sama da ita amma lokaci ɗaya ya ce dole ta rabu da ita.

        *********

    A haukace Daddy ya yi kan Kabiru ya rufe shi da wani mahaukacin duka, sai da ya gaji don kansa sannan ya janye Jabun Raihan ya rungumeta yana sauke ajiyar zuciya. A cen gafe Kabiru ya faɗi yana sauke ajiyar zuciya yana sauke numfashi cikin wahala, ɗagowa ya yi suka haɗa ido da Jabun Raihan a fakaice ta sakar masa wani malalacin murmushi ta fara motsa baki tana magana ba tare da ta wani ya ji abin da take faɗa ba. Duk maganganun da Jabun Raihan take yi a kannen Kabiru, ransa ne ya sake ɓaci ya dubi Daddy da yake jifansa da mugun kallo, cikin bagwariyar hausarsa  ya ce, "Alhagi shi wannan yaron ba mutumin kirki ba ne, azzalumi ne so yake ya shushe ki." Daddy ya sake dunƙule hannu ya kaiwa Kabiru naushi a baki ya ce, "Don uwarka a gabana kake ce min ƴata ba mutuniyar kirki ba ce, ina maka kallon mai hankalin ashe kaima ɗan iska ne, wallahi a yau ba sai gobe ba sai an rufe min kai na ga gatanka mahaukacin banza mahaukacin wofi." Raihan da ke maƙale da Daddy ta sake langwaɓewa tana ɗangale ƙafa. Alhaji Mustafa Indabawa ne ya dubi Daddy yana faɗin, "Abokina don Allah ka yi haƙuri, yanzu mu ƙarasa wurin da gawar yaron nan take." Kabiru ya yunƙura da kyar bakinsa na ɗigar da jini. Daddy na leƙa cikin ɗakin ya yi tozali da gawar Sulaiman, da sauri Daddy ya ja da baya jikinsa na tsuma don ba ƙaramin tsorata ya yi ba. Alhaji Mustafa shi ma yana leƙawa a zabure ya ja da baya har suna gware da Daddy. Lokaci ɗaya Daddy ya yi zuru-zuru hankali a tashe ya furta, "Wannan tashin hankalin ne ya faru a ɗakin Raihan?" Intisar da ƙarasowarta kenan ta amshe maganar da cewar,  "Daddy tun da nake ban taɓa ganin maciji mai muni irin wannan ba." Daddy da jikinsa ya gama sanyaya ya fara jinjina kai, suna nan tsaye macijin nan ya fara warware kansa daga jikin Sulaima. Ganin haka ya sa mutanen wurin suka fara darewa, Kabiru ne ya dafa ƙofar a hankali ya zura ƙafarsa ɗaya cikin ɗakin.

   Kallon-kallo aka fara yi tsakanin kumurcin macijin nan da Kabiru, a hankali Kabiru ya fara karanta duk wata addu'ar tsari da ta zo bakinsa. A zabure macijin ya fara ja da baya Kabiru na sake tunkararsa, wani kofi Kabiru ya hango da ruwa a jarka da sauri ya ɗauka ya zuba ruwa a kofi ya fara  karanta ayoyin tsari yana tofawa. Daddy ban da leƙe babu abin da yake yi. Kasancewar Jabun Raihan ta san irin soyayyar da Mahaifin Raihan yake yi mata ya sa ta kwaɓe baki a lokacin da ta ga Kabiru ya tasamman halaka Macijin da ubangidanta ya turo, ta ƙwalla wata ƙara tana faɗin, "Daddy wuyana." Kabiru ya waiwayo yana kallonta, Daddy ya kai hannu kan wuyanta yana faɗin, "Mu je asibiti a duba ki, wallahi duk abin da ya samu ƴata ka kuka da kanka." Daddy ya ƙarasa maganar yana watsawa Kabiru mugun kallo. Raihan ta sake langwaɓewa ta ce, "Daddy don Allah a bar korar macijin nan kar wani ya ƙara mutuwa kawai ka kira fire service." Daddy ya kalli wurin da Kabiru yake ya ce, "Kai maza fito daga ɗakin nan kar kaima ka yi mana mushe." Intisar ta kalli jabun Raihan ta watsa mata harara, sannan ta mayar da kallonta wurin Daddy ta ce, "Daddy amma naga kamar macijin ya fara ja da baya mai zai hana a bari a ga ƙoƙarinsa..." Alhaji Mustafa ya katse ta da cewar, "Tabbas ni ma haka na gama ayyanawa don yaron nan kamar akwai wani taimako da zai yi mana." Kabiru bai bi ta kansu ba ya sake tunkarar wurin macijin, lokaci ɗaya ya watsa masa ruwan tofin hannunsa bakinsa na ci gaba da ambaton Allah. Nan take macijin ya faɗi gefe yana wani iri  gurnani, zaburowa ya sake yi da niyyar kai wa Kabiru sara da sauri Kabiru ya watsa masa sauran ruwan da ke hannunsa. Wata dariyar farinciki Intisar ta saki don ko ba komai ta san an yi wa Mama Uwani illa,  jikinsu Daddy ba ƙaramin sanyi ya yi ba da ganin gwagwarmayar da suka yi tsakanin Kabiru da macijin.

  Jabun Raihan ta sake kallon Intisar ta saki ƙwafa a takaice, ta so ace Huzaifa ya bata umarni da tuni ta nunawa Intisar iyakarta. A wahalce Kabiru ya sa hannu ya hanyo macijin, ya fito daga ɗakin fuskarsa ɗauke da gumi lokaci ɗaya Daddy ya ji Kabiru ya birge shi saboda jarumtar da ya nuna, wannan ne karo na farko da ya ji ba zai iya ɗaukan mataki a kan wanda ya taɓa gudan jininsa ba, saboda yana matuƙar son mutum mai dakakkiyar zuciya. Sai dai har lokacin yana jin haushin Kabiru saboda abin da ya yi wa Raihan a idonsa.

   Kusan tare suka tarkata suka fito daga sashen, kowa da abin da yake faɗa. Kabiru fita ya yi da macijin can bayan gidan Daddy ya kai ya wurgar da shi, Daddy da kansa ya sa aka rufe sashen Raihan tare da cewar sai ya kira ma'aikata sun yi wa ɗakin feshin magani, a ɓangare ɗaya yana tunanin barinsu daga gidan gabaɗaya.

            *************

   Raihan bata da zaɓi don haka ta gyaɗa masa kai tare da faɗin, "Duk abin da kika faɗa na amince don Allah ki mayar da ni." Huzaifa ya yi murmushi jindaɗi don shi kansa ya lura da yadda Raihan ta gama tsorata da shi. Lokaci ɗaya ya ji ta bashi tausayi,  ya sa hannu ya zaro fiƙoƙin bakinsa waɗanda suka tsiro ya wara hannuwansa da niyyar Raihan ta rungume shi amma fir ta ƙi. Ya kalli fuskarta ya ce, "Kina ƙaunata." Raihan bata da zaɓi duk abin da ya faɗa sai dai ta amsa masa da amincewarsa. Tana tsaka da tunani ta ji ya ce, "Rufe idonki." Kallon hagu da dama ta fara yi a hankali ta furta, "Don Allah kar ki yi min komai." Huzaifa ya yi murmushi ya ce, "Kina rufe ido za ki ganki a gida." Tun bai rufe baki ba Raihan ta rufe idonta da ƙarfi, bata jima da rufewa ba ta ji tashin hayaniya na tashi sama-sama. Tana buɗe ido ta ganta zaune a falon Daddynsu, a hankali ta fara bin wurin da kallo, ta hango Intisar da sauran ƴanmatan da suke tare da su a ɗakinta. Suna haɗa ido da Intisar ta ji gabanta ya faɗi rass musamman da ta tuna irin gargaɗin da Mai siffar Mama Hasiya ta yi mata, a hankali ta miƙe ba tare da furta komai ba. Tana fita ta nufi sashen Mommy a kan step ɗin bene ta ci karo da Mama Uwani, tana ganinta ta washe baki ta ce, "Barka da hutawa uwar ɗakina." Sama-sama Raihan ta amsa, "Yauwa Mama Uwani ina Mommy take?" Mama Uwani ta nuna ɗakin mommy ta ce, "Tana ciki yanzu na kaiwa baƙi abinci ko na yi miki jagora." Raihan ta dakatar da ita da cewar, "A'a Mama Uwani ki je kawai." Mama Uwani ta yi murmushi tana faɗin, "Hutawarki lafiya uwar ɗakina." Raihan bata amsa ba ta wuce cikin ɗakin. Kafin Mama Uwani ta sauka daga kan bene Intisar ta doshi wurin, kallon-kallo suka fara yi wa junansu don ma mutane na zaune a falon, Mama Uwani ta saki wani malalacin murmushi ta wuce ba tare da ta tanka wa Intisar ba.

   Intisar na shiga ta yiwa Mommy sallama don a cewarta za ta tafi gida, amma koda ta yi wa Raihan magana ko ƙurarta bata kalla ba balle ta tanka mata. Tun da ta ga haka ta sha jinin jikinta, don haka tana fita daga gidan ta ɓace daga ƙofar bata tsaya a ko'ina ba sai a tsibirin ƙungiyar asirinsu.

   Raihan na zuwa jiki a sanyaye ta zauna, tana son sanarwa da mahaifiyarta cewar Mama Hasiya bata mutu ba amma tana tsoron abin da zai sake faruwa da ita. Tana nan zaune Daddy ya kira wayar Mommy ta waya yake sanar da ita, ɓacewar su Inno da Goggo sannan ta ce ta haɗa duk wani kayan sakawarsu don ya sa a ɗauke su daga gidan da suke zuwa gidansa da ke Unguwar sharaɗa. A cewarsa gidan cike yake da miyagun dabbobi, ba za su ci gaba da zama a ciki ba.

(Abin da bai sani ba duk in da zai je indai yana tare da Raihan tana tare da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ😂 Idan kuma yana tare da Mama Uwani yana tare da JINNUL-ASHIQ😂 Mu je zuwa.😎)

  Duk yadda Daddy ya so hukunta Kabiru ya ji zuciyarsa ta gagara ɗaukan mataki akansa, sai dai abu ɗaya ya riƙe duk abin da ya samu Raihan sai ya ɗauki mummunan mataki a kansa.  A wunin ranar suka tare a sabon gidan Daddy da ke sharaɗa, da sauran ƴan gaisuwa suka tare. Ɗakin da ke jikin gate aka bawa Kabiru, yana shiga ɗakin ya ga akwai komai na buƙata sai dai lokaci guda ɗakin ya rikiɗe masa zuwa tafka-tafkan maciji masu fasalin irin wanda ya kashe a ɗakin Raihan. Yana shirin ja da baya ya ji wani ya faɗ masa a gadon baya lafin ya yi wani yunƙuri, ya fara nannaɗe masa jikinsa.
       

  Intisar na zuwa ta kwashi gaisuwa wurin Hatsabibiya bungulu, bayan ta yi gaisuwa Hatsabibiya ta dubi Intisar ta ce, "Me yake tafe da ke da tsakar rana?"

Fuska ba walwala ta ce, "Hatsabibiya akwai tarin matsaloli domin Huzaifa ya saka ni a gaba, bayan Huzaifa akwai wani bafulatanin maigadinsu da alama zai kawo mana matsala. Amma wanda ya fi kawo mana matsala Huzaifa ne, don haka na ce ba zan yi ƙasa a gwiwa ba sai mun san abin yi don yanzu haka..."

Tun Intisar bata rufe baki ba Hatsabibiya Bungulu ta katseta da cewar, "Duk na ga abin da ya faru har ɗaukan Raihan da ya yi zuwa tsibirinsa." Intisar ta jinjina kai cikin huci tana cewa, "Da alama ya tsoratar da ita kuma a kowanne lokaci tana gabda bijirewa umarninmu."

"Sai mu kashe Huzaifa idan zai kawo mana matsala." Hatsabibiya ta faɗa kanta tsaye ba tare da ji shakku ko shayi ba." A firgice Intisar ta ɗago cikin tashin hankali ta zubawa Hatsabibiya ido, bakinta na rawa ta furta. "Kin manta wanene Huzaifa a wurina? Mijina ne fa." Hatsabibiya ta wara hannuwa cikin halin ko'inkula ta ce, "Ci gabanki ya fi zamantakewarki da shi don haka bana ganin zai amfane ki da komai." Intisar ta turɓune fuska ta ci gaba da cewa, "Ba zan lamince a kashe mijina kuma uban ƴaƴana ba, amma tabbas dole a nemi wata hanyar da za a samu mafita."

🤭 NA SAN DA YAWA ZA KU YI MAMAKIN JIN INTISAR MATAR HUZAIFA CE, KO KUN TUNO MUGAZA😂 ITA CE INTISAR. AMMA MAI YA SA HUZAIFA BAI GANE TA BA HAR SUKE TAKUN-SAƘA, SHIN WACCE RIBA MUGAZA ZA TA CI DA TA JEFA RAIHAN A ƘUNGIYAR ASIRI? IDAN SU MOMMY SUKA KOMA SHARAƊA SUN TSIRA KO DA SAURAN TAFIYA?

Share pls🌚
[7/14, 5:09 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 7

    Daddy yana tafe Raihan na riƙe a hannunsa har suka shiga cikin gidan  ayyane-ayyane yake yi, yana mamakin wane irin macijine da nan take zai naɗe mutum ya kashe shi, kuma a ce ya fito daga ɗakin Raihan ɗin sa. Kwafa ya yi yana tunanin irin matakan tsaron da zai ƙara akan na da, har suka shiga ciki. Mommy jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don tun lokacin da abin ya faru ta fahimci macijin ɗakin Raihan ba ainihin dabba ba ne. Sai dai a wannan karon ta ci alwashin faɗawa Daddy gaskiya duk irin ɓacin ran da zai yi, don haka suna zuwa ta nemi ganawa da shi a sabon ɗakinsa dama gidan ya gina shi ne da sunan bayan wasu watanni su tare, amma kasancewar ba a gama masa ƙaƙale-ƙaƙale ba ya sa suka dakata da komawar, amma dole ta sa suka tashi a rana tsaka suka koma. A gaggauce Daddy ya dubi mommy ya ce, "Faɗi ina jin ki, kin san yanzu aka yi mini waya wai ankai su Inno da Goggo Hisba dole sai na zo, wani tashin hankali wai an tsinci su Inno a cikin masallacin Malam Isa na ƙarshen layi." Sai a lokacin Mommy ta zaro ido don bata san abin da yake faruwa ba, ganin ta shiga tashin hankali ya sa ya dube ta fuska ba walwala ya ce, "Ba fa wani abu ne na ɗaga hankali ba, komai ya zo da sauƙi yanzu dai ina zuwa." Yana gama maganar ko jiran cewarta bai yi ba ya fice daga ɗakin, jigum Mommy ta yi abu goma da ashirin ya haɗe mata.

   Wani irin zafi Kabiru ya fara ji a jikinsa kamar wanda yake gaban wuta, hajijiya ya ji ta fara ɗaukansa ga wata irin matsa da macijin yake yi masa, tun yana daga tsaye har ya durƙushe a wurin yana son furta ayar Allah, amma macijin ya matse masa maƙogaronsa. Kakari ya fara yi kamar wanda ransa zai fita, a zuciyarsa yana son biya ko da ayatulkursiyyu ce amma wani abu mai nauyi ya ji ya tokare masa ƙirji kamar dutse. Yana cikin wannan halin ya ga ɗaya daga cikin macizan ya miƙe tsaye cak ya fasa kai, a hankali fatar jikin macijin ta fara saɓewa tana fita daga jikinsa sai kuma ya fara rikiɗa daga siffar maciji zuwa siffar bil'adam. A hankali wata matashiyar mace ta bayyana ilahirin jikinta gashi ne tun daga kanta har zuwa ƙugunta, ya yin da ƙugunta yake a nannaɗe cikin surar maciji. Harshe ta fara zaro masa nan take wani jaririn maciji ya faɗo, ta damƙe shi a hannunta ta kalli Kabiru da yake cikin mummunan hali ta fara magana, "Kai matashin bafulatani, wa yace maka takun saƙa da ni sauƙi gare shi? Ka san wa ka illata kuwa? Ka san wa ka kashe min kuwa? Ko kana tsammanin ka ci bulus ne?" Kabiru ya ɗago yana sauke numfashi da ƙyar idanunsa jawur ga gumi na ci gaba da tsiyaya daga jikinsa. Baki yake son buɗewa amma ya kasa, ganin haka ya sa ta sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya sai da ta yi mai isarta sannan ta fashe da matsanancin kuka, ta jima tana yi sai ta tsagaita da kuka ta sake kallonsa ta ce, "Ba kai kana taƙama da addu'a ba ka yi ta mu gani, har za ka kashe min miji kana tunanin za ka zauna lafiya?" Macijiyar na gama maganar ta fara rarrafowa zuwa gaban Kabiru, ganin ta nufoshi gadan-gadan ya sa Kabiru ya ƙara yunƙura yana ja da baya, ya fara bude baki yana ƙoƙarin karanta addu'a haɗe da motsa baki sai dai ko kaɗan muryarsa bata fitowa, tana tunkararsa hushin numfashinsa ya doki gangar jikinta ba shiri ta ja da baya saboda wani irin zafi da ta ji yana fita daga bakinsa. Kallon-kallon suka fara yi a tsakaninsu, bata daddara ba ta sake yunƙurowa a kashi na biyu da niyyar hallakashi. Duk yadda Kabiru ya kai ga buɗe muryarsa ya yi addu'a abin ya gagara. Dabara ce ta faɗo masa ya fara biya ayatulkursiyyu a zuciyarsa, tana tunkaro shi ya fara tofa masa. Ganin tana niyyar hallaka ya sa ta sake yin baya, nan take macizan da ke gewaye da shi suka ɓace. Ƙaton da ya naɗe shi tuni jikinsa ya saki da ƙyar ya rarrafa ya bi ta jikin bangon ɗakin ya ɓace. Ɗakin Kabiru ya rage daga Macijiyar sai Kabiru, ya yin da ta sake kafe shi da ido tana ƙare masa kallo don ta fahimci makasar da za ta samu a jikinsa ta yi masa illa. A wahalce Kabiru ya faɗi can gefe yana mayar da numfashi, jikinsa gabaɗaya ya yi ja saboda irin tsananin matsar da macijin ya yi masa. A hankali jikinsa ya fara raɗaɗi, yana kai idanunsa kan fatarsa ya lura da yadda ta fara sauya launi zuwa fatar maciji. Macijiyar kallon Kabiru ta yi ta fara ƙyaƙyacewa da wata irin shu'umar dariyar ƙeta, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi da ganin abin da yake faruwa da fatar jikinsa ba. Yana tsaka da tunani ya riski muryar macijiyar tana faɗin, "Ka kashe min mijina ba tare da wani dalili ba, Huzaifa ya nemi tallafin mijina akan ya zo taimakonsa ka kashe shi, zafin mutuwarsa ta sa na ji tamkar na kashe ka amma ba zan kashe ka yanzu ba sai na gama wahalar da ruhina da gangar jikinka sannan na hallaka da hannuna. Ka je ko da wannan hallitar fatar macijin na barka ƙuncin rayuwar duniya ya ishe ka." Tana gama maganar ta sake naɗewa ta koma murtukekiyar macijiya, juyi ta fara yi daga wurin da take nan take ta baje a ƙasa ta fara nutsawa cikin ƙasa har ta ɓace ɓat. Ilahirin jikin Kabiru ban da rawa babu abin da yake yi, babban tashin hankalinsa yadda ya ga fatar jikinsa ta koma ta maciji illa iya fuskarsa, hannu da ƙafarsa ne kaɗai basu rikiɗa ba da yake macijin bai taɓa masa nan ba.

      

      A fusace Hatsabibiya ta ɗago da ta sake kallon Intisar ta ce, "Idan ba mu kashe shi ba kina da hanyar da za mu ɓullo masa? Ko kuma kina da shawara akan yadda za mu kawar da tunaninsa akan Raihan?" Intisar ta yi shiru tana nazari don ita kanta ta san wanene Huzaifa da tsananin bincike irin nasa, ta san tun da ya kafa mata ƙahon zuƙa dole zai bi diddigin wacece ita da asalinta. Ta san muddin ya gano ta ba ƙaramar ƙura ce za ta tashi a tsakaninsu ba, a baƙar zuciya irin tashi yana iya hallakata. Don ma tana amfani da sirrin tsafi da sihiri ko a yanzu yadda ya ɗora ransa akan Raihan da tuni ya gama da ita. Tana cikin tunani ta sake riskar muryar Hataabibiya ta ci gaba da cewa, "Idan har baki da wata dabarar ga tawa shawarar." Intisar ta dubi Hatsabibiya tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina jin ki Uwargidana maganin kukana, da ke da Abar bauta ku kaɗai na dogara da ku duniya da lahira (Wa'iyazubillah) ke kika saba ɗauke min duk wata damuwata a yanzu ma ina biye da ke don jin mafitar da za ki kawo mana kafin abar bauta ta bayyana."

   Hatsabibiya kanta ya sake girma, ta miƙe daga wurin da take ta ɗauki wani dogon ƙaho mai faɗi da tsawo ta kafa shi a bakinta sannan ta durƙushe a gurin. Ta kafa tsinin ƙahon a doron ƙasa sannan ta busa shi da ƙarfinta, lokaci ɗaya tsibirin ya ɗauka tsananin ƙararsa kamar zai tsaga dajin gida biyu. Tun bata rufe baki ba aljanu masu ɗauke da munanan hallitu suka fara fitowa wasu daga ƙarƙashin ƙasa wasu daga cikin duwatsu ya yin da wasu suka fara fitowa daga ɗakin tsafi. Kafin wani lokaci tuni sun taru suna masu sujjada a gabanta, tare da yi mata kirari kamar yadda suka saba sannan suka ƙame wuri ɗaya suna jiran umarninta.

   Wani irin kuka haɗe da dariya ne ya fara tashi, lokaci ɗaya tsibirin ya fara girgiza suna nan tsaye wannan mummunar hallitar mai ɗauke da kawuna (Abar bauta.)  Ta ziro kawunanta zuwa harabar wurin da take. Suna yin tozali da ita suka kwanta a wurin har hatsabibiya suna masu yi mata sujjada, haɗe da kirari.  Kafin ƙiftawar ido Wani baƙin aljani ya dira a gabanta cikin girmamawa yana tambayarta.

  "Ya ke uwargijiyata shin jariri kike buƙata, uwar jariri tsoho ko tsohuwa kike buƙata." Ɗago da kawunanta ta yi, sai ta saki kuka kamar na bujimin sa. Jin kukan San ya sa aljanin sake rissunawa yana faɗin, "Kin samu kin gama." Yana gama maganar ya ɓace daga wurin.

    Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara magana da murya mara daɗin sauraro, "Duk abin da kuka tattauna mun saurara don haka babu amfanin maimaitawa sai zartar da hukunci." Jikin Intisar tuni ya fara tsuma nan take gumi ya rufe ta, don bata san irin hukuncin da Abar bauta za ta yanke a kan Huzaifa ba. Tana tsaka da nazari ta riski muryarta tana ci gaba da cewa, "Ba za mu kashe Huzaifa ba sai dai dole a sauyawa taku salo, sanin kanku ne a da ɗanyan kifi yana haukatata. Sakamakon ɗan da ta haifawa Huzaifa yana da haɗin jinsi da hallitar kifi. A yanzu za mu sake haukatata fiye da lokacin baya, a cikinku waye zai iya aiwatar da abin da muke buƙata?" Wata aljana da ta miƙe tsaye tana faɗin, "Abar bauta zan riƙa haukatata da surar mahaifiyarta..." Tun bata rife baki ba Abar bauta ta katse ta cikin tsawa tana cewa, "Kina tunanin wannan mafita ce? Idan kika yi haka dole za su nema mata lafiya, mu kuma duk wanda zai nuna hanyar lafiyarta sai mun tsotse jininsa." Haka aljanun da ke wurin kowa ya riƙa ɗaga hannu yana faɗin abin da zai aiwatarwa Raihan. Duk acikinsu shawarar guda biyu aka ɗauka, ɗaya daga ciki ya ce zai riƙa shiga jikin maguna yana haukatata, sai wacce ta ce za ta riƙa shiga jikin ƙadangaru sai dai kowanne da abin da zai aiwatar.

   Abar bautarsu ta ji daɗin abin da suka yi, don haka ta yi na'am da wannan shawarar. Suna nan zaune aljanin da ya tafi ɗauko mata jinin da za ta sha ya dawo hannunsa ɗauke da wani Dattijon tsoho, suna shigowa tun ba su ƙarasa gaban abar bauta ba, ta miƙa hannunta guda ɗaya ya warto Dattijan haɗe da ƙwaƙule masa ido tun bai ƙarasa gabanta ba ya yi fata-fata da shi, sauran kawunan da ke jikinta suka kafa kawunansu nan take suka gama da Tsohon. Aljanin ya sake russunawa yana faɗin, "Abar bauta ya isa ko a ƙaro wani." Gyatsa ta yi, tana lashe jinin bakinta, sai da ta tsotse ƙashin ƙoƙon kan tsohon sannan ta ɗago ta ce, "A ina ka samu wannan hallitar mai daɗi?" Aljanin ya washe bakinsa yana murmushi bakinsa ya yi girman rijiya saboda wannan ne karona na farko da abar bauta ta yabi naman ɗan'adam. Ya russuna yana faɗin, "Fansar iyayena na mallaka miki abar bauta, ki fanshi wanda kike so. Ke kika hallakawa kike tseratarwa kike kashewa kike rayawa, na samu hallitar bil'adam a cen bakin wata ƙatuwar bola fitowarsa kenan daga wurin Boka Harisu, yana shirin saka laƙanin asirin da aka bashi a ƙarƙashin shara na ɗauko maka shi." Hatsabibiya ta sake kallon wurin da ƙoƙon kan Dattijon yake tana hura masa iska nan take ƙoƙon kan ya fara mirginawa, har sai da ya yi sau uku sannan hallitar tsohon ta sake dawowa kamar yadda take har da kayan jikinsa. Abar bauta ta kalli Aljanin da ya kawo Dattijon ta ce, "A ɗauke shi a mayar da shi wurin da yake rana ita yau a sake dawo min da shi jinin jikinsa bai ishe ni ba." A firgice tsohon ya kalle su nan take jikinsa ya hau tsuma, ya tsugunna yana roƙo da magiyarsu, yana cikin haka ya ga anɓace da shi daga wurin.

     Abar bauta ta dube su ɗaya bayan ta ce, "Na wakilta guda ɗaya daga cikinku da ƙadangare da mage, kuma ya zama wajibi a yau ba sai gobe Raihan ta kawo mana ziyara, shi kuma Huzaifa ku bar min lamarinsa a hannuna amma ba zan cutar da shi ba ko halaka shi alfarmar Mugaza da take kawowa ƙungiya ci gaba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Intisar/Mugaza ta saki tana lumshe ido, ɗaya bayan ɗaya suka fara darewa daga wurin, Hatsabibiya ta yi wa abar bauta rakiya zuwa turakarta sannan ita ma ta ɓace daga wurin.

    
      Daddy shi da abokinsa Alhaji Mustafa suka ƙarasa ofishin Hisbar da su Inno suke, yana zuwa ya samu su Inno a zaune duk sun yi zuru-zuru kamar waɗanda suka wuni suka kwana basu ci ba, musamman Inno da take tsaka da jin mutuwar Hasiya. Suna ganinsa Inno ta fashe da kuka ta kalli ɗan hisbar da ke gefe tana faɗin, "Amma dai kai ƙaramin ɗan sanda Allah ya watsa maka albarka, wallahi ku bar ni a ofishinku amma ni da gidan Audullah sai a lahira ma sadu da juna." Daddy yana shirin yin magana Goggo ta tsugunna a gaban ɗan hisban ta ce, "Yaro ka dubi Allah ka dubi Ma'aiki  ko tasha ne ka kaini na wuce albasu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inno me yake faruwa zuwa na yi mu tafi fa." Inno sunne kai ƙasa ta yi kamar ba ta ji me yake faɗa ba, ta kalli Goggo ta ce, "Don Allah ki duba min hallitar jikin Audullahi ta cika ko akwai nasaka, ada na ƙaryata ki amma Allah ya sani gidan Audullahi Makarai ne suke cin karensu babu babbaka a ciki." Daddy zai yi magana ɗan hisbar ya dakatar da shi, don labarin abin da ya faru tuni ya karaɗe ko'ina musamman da ƴan jarida suka samu zancen yaɗawa, Likitoci suka shiga binciken gawar Sulaiman a ya yin da suke neman Kabiru babu inda ba a duba ba amma basu ganshi ba.

Ɗan hisban da kanshi ya yi wa su Inno nasiha, ya sake faɗarkar da su da cewar duk wani abu yana faruwa ne da izinin Ubangiji kuma addu'a takobin mumini ce. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu su Inno suka bi Daddy gidan har sai da ya tabbatar musu da cewar ya sauya musu wurin zama.
Lokacin da su Inno suka koma gida tuni gidan ya yi shara-shara babu mutane sosai, don tun a tsohon gidansu ganin abin da ya faru ya sa mutane da dama kowa ya yi ta kansa. Su Goggo a ɗaɗɗare suka shiga sabon gidan, suna tafe bakinsu na motsi da alama addu'a suke yi don ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Mommy da kanta ta kaisu ɗakinsu, kowacce ta zauna shiru don ƙawayensu da suka zo gaisuwa tuni kowacce ta cika wandonta da iska.

   BAYAN MAGRIBA.

     Raihan na kwance a ɗakin mommy lamo kamar mara lafiya, don gabaɗaya wani sukuku take jin ta kamar ba ita ba tun da ta dawo daga duniyar aljanu. Tana daga zaune ta ga wurgawar abu, da sauri ta tashi zaune tsigar jikinta na tashi. Wani ƙadangare ta gani yana buɗe mata baki alamar dariya, sai kuma ya fara ƙada mata jela yana yi yana tunkarota. Ƙura masa ido ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, ta fisge ɗankwalin kanta nan take gashin kanta ya hargitse, ƙananan kifaye ne suka fara fita daga bakin ƙadangare. Lokaci ɗaya ta yi kukan kura ta fisgoshi haɗe da ƙwalla uwar ƙara, tana ɗaukansa ta tura kansa cikin bakinta nan take ta fisge masa kai ta wurgar a wurin gangar jikin ƙadangaren yana hannunta. Mommy da wata ƙanwarta har rige-rigen shiga ɗakin suke saboda duk wanda yake gidan babu wanda bai ji ihunta ba. Suna tura ƙofar suka ganta a tsaye tana riƙe da gawar jangwalagwada jini yana ɗiga, ga kansa can gefe sai zare ido take tana faɗin, "Duk wanda ya ce zai hallaka mini Ɗana wallahi sai na fidda masa kai.

  🤭🤭🤭🤭 WUYAR AIKI BA'A FARA BA, HAR YANZU FA ASHAFI NA BAKWAI AKE😎😎 KUN GA KUWA AKWAI SAURAN TAFIYA, AKWAI ƘURA A GABA.🤸🏻‍♀️💃🏼

Share Hilis🌚
[7/16, 12:01 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 8

     Ilahirin jikin mommy rawa ya ɗauka Aunty lubna ta zaro ido hankali a tashe don ko a mafarki bata taɓa cin karo da wannan mummunan abin da Raihan ta aikata ba. Mommy tana son tunkarar Raihan amma tana gudun hukuncin da za ta zartar a kanta, murya na rawa ta dubi Raihan ta ce, "Raihan lafiya me kike yi haka? Ƙadangare ne fa a hannunki." Raihan da har lokacin idonta jawur suke ta sake kai kallonta kan ƙadangaren hannunta, ta sake saka wurin jelarsa a baki ta cisgeta da ƙarfin tsiya ta kalli saitin da su Mommy suke ta tofar a wurin. Wani irin huci ta fara yi idanunta na sake firfitowa ta ce, "Ɗana yake shirin cinye min don haka dole na hallaka shi." Mommy ta tunkari wurin tana son Raihan ta wurgar da ƙadagaren hannunta amma tsoron abin da kaje ya zo ya hanata. Don a lokacin da take da shekara goma ntana da makamancin ciwon ta ya tashi ta taɓa cirewa wani almajiri ɗan yatsa, a lokacin shi ma zuwa ya yi zai ƙwaci agwagwar malaminsu da ta fito kiwo Raihan da Mommy sun fito daga mota, a lokacin da suka kai ziyara Albasu. Tuno da haka ya sa mommy take son tunkararta amma tana jin tsoro. Daga nesa da ita Mommy ta leƙa fuskarta tana faɗin, "Raihan ki yarda abin hannunki." Cikin wani irin ƙaraji ta nufo wurinsu gadan-gadan da ihu tini ba shiri su Mommy suka fice a guje kowa yana gudun ceton ransa.

Hankali a tashe mommy ta nufi sashen Daddy tana ƙwala masa kira. A bakin ƙofa ta ci karo da shi tana ganinsa ta fara nuna masa hanya tana faɗin, "Alhaji Raihan ce..." Maganarta ta maƙale saboda yadda take sauke ajiyar zuciya. A zabure Daddy ya kama kafaɗarta yana jijjigawa yana faɗin, "Me ya samu Raihan ɗin ki faɗa min tana ina?" Hanya ta riƙa nuna masa tana faɗin, "Tana can ta tsintsinka ƙadangare da haƙoranta." Da gudu ya nufi hanyar ɗakin Raihan hankali a tashe. Nan take ragowar mutanen da ke cikin gidan suka yi tsilli-tsilli, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci tana cikin matsanancin tashin hankali.
Daddy kai tsaye ɗakin da Raihan take ciki ya tunkara yana shiga ya same ta a cen gefe ta faɗi da alama bata numfashi. Kallon ɗakin ya fara yi saboda yadda jinin ƙadangaren ya ɓata saman carpet ɗin ɗakin, daga gefen hannunta ya hangi gangar jikin ƙadangaren hannunta ya jiƙe sharkaf da jini. A hankali ya ƙarasa wurin ya mirgino da ita yana ambatar sunanta muryarsa a raunace, shiru ne ya ratso a ɗakin babu abin da yake tashi sai karar AC da saukar numfashin Daddy. Tsugunnawa ya yi a gabanta ya tallafo da kanta zuwa kan cinyarsa, murya na rawa ya furta: "Me yake samunki ne Raiha? Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da ke?" Kuka ne ya ci ƙarfinsa ya kafa kansa a jikinta yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Daga bakin ƙofa Mommy ce ta shiga jiki a sanyaye, ita kanta lamarin Raihan ya fara bata tsoro. Kusan shekara goma sha biyar kenan suna fama da abu ɗaya, babban tashin hankalin da ciwon kullin gaba yake yi baya raguwa. A sanyaye ta zauna a gefen Daddy ta ce, "Daddyn Raihan." Ɗagowa ya yi ya dube ta idonsa na ci gaba da zubda ƙwallah, ita ma hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta sa hannu ta share sannan ta ci gaba da cewa, "Ka daina kuka don yanzu babu buƙatarsa a gurbin halin da muke ciki..." Tun bata rufe baki ba Daddy ya katseta da cewar, "Ido yana zubda hawaye ne ba don gangar jiki da ruhi suna buƙata ba, sai don samun sauƙi ga raɗaɗin ƙunan zuciya. A da na ɗauka rashin haihuwa babban masifa ne a gare ni sai ga shi a yau na wayi gari Allah ya bani gudan jinina ga kuma masifar da tafi min rashin haihuwar..." Da sauri Mommy ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce, "Bai kamata ka riƙa furta irin kalmomin nan ba, domin duk abin da ya samu bawa yana daga Ubangiji shi ya fi mu sanin dalilinsa na yin haka." Mommy ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa, "Ya zama wajibi ciwon yarinyar nan a koma yin da Islamic don wannan yana da alaƙa da shafar aljanu..." A razane ya katse ta yana faɗin, "Kina hauka ne? Na gargaɗe ki da ki daina danganta jinina da jinsin aljanu." Wanna karon mommy ita ma hassala ta yi ta ci gaba da cewa, "Kar ka sake furta kalma ta ƙasƙanci a kaina, don duk taƙamar da kake yi ba kai kaɗai ka haifeta. Raihan ƴata ce idan kai ba za ka nema mata maganin Islamic ba dole ni zan nema mata." Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Daddy ko a jikinsa tana fita ya ɗauki waya ya kira likitan da ke duba Raihan, zayyana masa komai ya yi sannan suka yi sallama ya ci gaba da zubawa Raihan ido yana tunane-tunane a zuciyarsa.

    
    Lokacin da Macijiyar ta ɓace daga ɗakin Kabiru, daga gefen hagunsa ya fara jin wani irin gurnani irin na riƙaƙƙun kumurcin maciji, a hargitse ya sake miƙewa yana kalle-kalle bakinsa na furta Amanarrasulu don a tunaninsa macijin ne zai sake bayyanar masa. Ya jima yana jin wannan gurnanin daga baya ya ji shiru komai ya ɗauke daga dodon kunnensa, daga jikin hannun rigarsa wata fata ya ga ta kwakkwaɓo irin saɓar fatar maciji wacce yake yi. Da sauri ya ɗago ta cikin tashin hankali don lamari ya fi ƙarfin tunaninsa, ido ya zurawa gwiwar hannunsa ta wurin da fatar ta faɗo ya ga wurin ya sake yin sheƙi tamkar bayan maciji. Kwalla ce ya ji ta zubo masa saboda duk wanda ya lura da halin da yake ciki ba zai taɓa zama a kusa da shi ba, kallo ɗaya za ka yi wa jikinsa ya firgita ka don bambamcinsa da maciji kai, hannu da ƙafafuwa. A hankali ya ƙarasa wurin buhun kayansa, nan take ya fara zazzagewa yana birkito kayan da zai saka don ya rufe jikinsa. Sanin kansa ne ko masu aikin gidan suka fahimci halin da yake ciki zamansa a cikin gidan ya ƙare balle kuma a ce Alhaji ya lura da yadda surar jikinsa ta koma. Sai da ya tura ƙofarsa ya rufeta ruf don kar wani ya turo, sannan ya tuɓe rigar jikinsa da yake mai gajeren hannu ce. A jikin mudubin ya tsaya yana ƙarewa jikinsa kallo fatar jikinsa ta koma sak irin ta maciji, wani hawayen ne ya sake gangaro masa ya sa hannu ya share sannan ya ɗauko wata tsohuwar rigar shadda mai dogon hannu, ya ɗauko wani tsohon mayafinsa da wanda ya gada a wurin mahaifiyarsa ya naɗe wuyansa da shi. A jikin bango ya jingina a fili ya fara magana cikin karyewar zuciya, "Allah sarki Baffajo ba don rashin lafiyarka ba, da babu abin da zai hanani barin wannan gidan, don da alama wannan ba wurin zama ba ne." Kabiru ya ɗaga hannu sama ya ci gaba da cewa, "Allah ka bawa Baffajo lafiya, da yardar Allah sai na bar gidan nan don na nemawa kaina lafiya." Daga gefensa ya ji an bushe da dariya, yana juyawa ya hangi matashiyar budurwa tana tsaye tsirara babu kaya a jikinta. Hannuwa biyu ta wara masa tana faɗin, "Ina da hanyar da zan kawo maka mafita matuƙar za ka bani dama." Kabiru ya kauda kansa gefe yana faɗin, "Wa'iyazubillah." Ɓangaren da ya juya fuskarsa ta sake komawa tana faɗin, "Indai akan matsalar abin da ya faru da jikinka ne zan warkar maka da shi matsawar za ka bani haɗin kai." Kabiru ya ɗago da kansa yana shirin yi mata magana, karaf idonsu suka haɗu wuri ɗaya nan take ya ji tsigar jikinsa na tashi.  Da ƙyar ya iya saita kansa sannan ya furta, "Ki taimaka min ki raba ni da wannan fatar macijin, ki gaya min me kike buƙata daga wurina yanzu na aiwatar miki?"

  
     Duk wani shige da fice da su Mommy suke yi akan idon Mama Uwani, lokacin da ta ji labarin abin da ya faru ta shiga tashin hankali don ta san wannan abin da Raihan ta aikata baya daga cikin abubuwan da take saka Raihan tana aikatawa. Fitowa ta yi ta fara kaiwa da kawowa nan take wata dabara ta faɗo mata, sai da ta shige ɗakinta da yake babu kowa a ciki sannan ta ɓace daga ɗakin. A lokacin da ta ɓace Dr Hamza yana gidansa ya gama shiri don zuwa gidansu Raihan, Huzaifa na zuwa da ya ga haka don kar ya kawi masa matsala ya bige shi a kan gado nan take bacci ya yi gaba da Dr Hamza. Cikin siffar Dr Hamza ya kira lambar Daddy bugu ɗaya kawai ya yi ya ɗauka, a gaggauce Daddy ya furta, "Dr ka ƙaraso ne?" Huzaifa da ke ɗauke da surar Dr Hamza ya amsa masa, nan take Daddy ya bashi umarni da ya shiga. Daddy da Huzaifa a harabar gidan suka haɗu, Huzaifa sai murmushi yake ƙasa-ƙasa don ko ba komai ya samu damar da zai aiwatar da abin da yake ransa. Suna shiga Raihan tana nan kwance kamar gawa bata numfashi ko hannunta baya motsawa,  ido ya zura mata yana son sanin musababbin abin da ya sa ta tsinka ƙadangare gida biyu don ko kaɗan babu sa hannunsa a ciki. Yana tsaka da nazari ya riski muryar Daddy yana faɗin, "Dr don Allah ayi wani abu ciwon nan sai ƙara gaba yake yi." Huzaifa ya miƙe tsaye yana zare gilashin idonsa, ya yi jim kamar wanda yake damuwa sannan ya fara magana, "Gaskiya yanayin ciwonta ya fara bani tsoro Alhaji, amma abin da ya fi akwai wani abokina a India ina tunanin sai an fita da ita, amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama."
Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi:

  "Saboda Allah haka kawai ace duk wani tashin hankali bai faru ba sai a ranar da Ƴata Hasiya ta kwanta dama, ina dalili yarinya sai rikiɗa take kamar wahainiya. To Allah ya sani idan ban watsa mata albarka ba Mamman mai ƙawa'idi bai haife ni ba, ku bar ni yau ko ni ko Rihanu a gidan nan." Daddy ya waiga wurin Inno da niyyar zai yi magana, suna gano halin da Raihan take ciki da sauri su goggo suka yi baya cike da tashin hankali. Goggo ta dafe ƙirji jikinta sai tsuma yake yi kaɗan ya rage fitsari bai zubo mata ba, ta nuna wurin da Raihan take ta fara faɗin, "Laƙadi ja'akum yau na shiga uku. Allah ya sani duk garin Albasu babu mayya ko guda ya aka yi aka samu maita a zuri'ata, a'a wannan lamarin dole akwai ayar tambaya wallahi idan Raihanu bata shiga ƙungiyar asiri ba Na koma Albasu a ƙafa." Huzaifa ya waigo wurinsu yana faɗin, "Iya don Allah ku yi shiru ina kan Patient bana buƙatar hayaniya." Inno ta riƙe haɓa saboda takaici don gani take abin nasa kamar har da cin fuska, ƴarta ta mutu ba a yi zaman makoki yadda ya kamata ba kuma a kawo mata maganar Patient. A zuciye ta ƙarasa gaban Huzaifa sai da saita daidai fuskarsa ta wara hannunta a kai tana faɗin, "Ƙaniyarka ka ji, fitsararre kana fama da fuska kamar teba." Huzaifa ya kalli Inno a zuciyarsa yana ayyana idan da ya ga dama wurgi ɗaya zai yi da ita ta baje a ƙasa. Bai dawo daga tunani ba ya ji ta sake nuna shi da yatsa tana ci gaba da cewa, "Kai baƙin munafuki ka gaya min idan da ƴarka ce ta musu waɗannan masifun suke faruwa me za ka yi?" Daddy ya zagayo ta wurinta yana cewa, "Inno don Allah ki yi haƙuri shi fa wannan babu ruwansa a ciki." Goggo ta leƙa fuskar Huzaifa tana kwaɓe baki ta ce, "Akan wannan baƙin munafukin kake shiga gaban mahaifiyarka?" Ta waiga wurin Huzaifa ta ci gaba da cewa, "Wallahi ka fito ka gaya masa gaskiya ko na watsa maka albarka, ka san dai ciwon Yarinyar nan bana mai jan kunne ba ne." Huzaifa ya dubi Daddy kamar abin bai dame shi ba ya ce, "Alhaji a kawo min ruwa." Daddy na jin haka da sauri ya fita daga ɗakin, yana fita Huzaifa ya warto su Inno a hannu ya matse su wuri ɗaya. Kamar waɗanda aka naɗe su da igiya aka ɗaura haka su Goggo suka ji, suna shirin yin ihu bakinsu ya yi musu nauyi. Sai da ya yi hajijiya da su sannan ya watsa su can gefe kamar kayan wanki, zannuwa da ɗankwalen su Inno tuni suka maƙale a saman fanka.

    
      Lokacin da Raihan ta faɗi a lokacin ne Abar bauta ta bada umarnin ga Raihan da ta kawo mata ziyara, nan take ruhinta ya fita daga jikinta zuwa tsibirin da ƙungiyar asirinsu take. Tana zuwa ta russuna ta yi gaisuwa ga Hatsabibiya, a take ta turɓune fuska ta dubi Raihan tana faɗin, "Mun aika kiran gaggawa ne don Abar bauta na buƙatar ku sha jinin mai naƙuda tare da ke, kuma yau ita ce ranar da za a yi miki wankan tsarki dole ke ce za ki kawo mana jinin da za mu sha daga jikinki, Muna buƙatar jinin mahaifiyarki daga yau zuwa gobe idan ba haka ba Abar bauta za ta iya yi wa danginki ɓarna." Ruhin Raihan wata irin zabura ya yi da jin wacce aka ce ya kawo daga cikin danginta, sai dai hakan bai hanata amincewa da buƙatarsu ba. Cikin girmamawa Raihan ta russuna tana faɗin, "Fansar Mahaifana yana gare ku na baku wuƙa da nama, mai naƙuda a ko'ina take zan kawo mana ita yanzun nan." Tana gama maganar ta bi ta iska ta fice daga tsibirin.
Ruhin Raihan na fita bai tsaya a ko'ina ba sai cikin wani babban asibiti, kai tsaye daƙunan majinyata ta fara shiga har za ta fice ta hango wata tsohuwa da alama tana jin jiki, a kan ruwan cikinta ta dira har ta kafa bakinta za ta tsotsi jini majinyaciyarta ta ƙaraso gabanta tana karanta mata ayatulkursiyyu tana tofa mata saboda tuni sun samu bacci ya ɗauketa, ta karanta mata addu'a saboda ita ma bacci take son yi. Da sauri Raihan ta tashi daga kanta ta matsa gefe tana sauke numfashi,  daga can gadon ƙarshe ta hango wata mara lafiya bata jinkirta ba ta hau kanta tuni ta kafa bakinta a kanta ta fara zuƙar jini. Nan take jikin matar ya rikice ganin haka ya sa majinyaciyarta kiran nurses, sun kai mutum huɗu a kanta duk yadda suka kai ga bakin ƙoƙarinsu abin ya ci tura, nan take rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce can ɗakin haihuwa. Raihan na shiga ta hangi mata kusan uku masu naƙuda, a kan idonta ɗaya ta haihu ta cikin mutum biyun ta dira a gadon ta tsakiya. Tana niyyar kafa kanta a ƙirjinta daga bayanta ta ji an ce, "Jinin Matata ya fi ƙarfinki." A zabure ruhin Raihan ya waiga don ganin wanda ya dakatar da ita ga abin da take shirin aiwatarwa.

A MIN SHARE FISABILILLAH🌚
[7/18, 4:07 PM] Ameera Adam🌚: *ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

              FREE PAGE 9

       Rangaji ta fara yi tamkar bishiyar dalbejiyar da take kaɗawa da iskar damuna, a hankali Kabiru ya ɗan fara ja baya don ko kaɗan hankalinsa bai kwanta da ita ba. Cikin wata irin murya mai jan hankali ta fara magana, "Ka amince min da buƙatata ƙwaya ɗaya ce tal na yi maka alƙawarin yaye maka wannan matsalar da take jikinka." Kabiru da yake jin wani abu yana yawo a zuciyarsa game da ita ya runtse idonsa sannan ya fara magana cikin wata irin kasalalliyar murya, "Ba na buƙatar ganinki cikin wannan yanayin." Tun bai rufe baki ba ta ƙarasa wurinsa ta sa hannu tana ƙoƙarin taɓa shi ta furta, "Laƙani aka bani domin cikar burina a kan Daularmu ta Daulatul jinnul-Turabiy. Idan har ka amince min za ka kusance ni kuma zan warkar da kai, idan ka yi min haka zan mallaki Daularmu da abin da yake cikinta, na zo a sirrance ne ta sanadi ƴar uwata wacce ta yi maka haka..." Tana tsaka da magana ya katse ta da furta, "A'uzubillahi minnasshaiɗanirrajim." Da sauri ta ja da baya tana hakki saboda yadda ta ji wani irin hucin zafi daga jikinsa. A hankali ya tattaro jarumta ya ci gaba da karanta ayoyin kariya da duk wata addu'a da ya san ya taba biyata. Nan take ta ɓace daga gabansa don yadda take ji tamkar zai halakar da rayuwarta, ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa saboda yadda hankalinsa ya sake tashi fiye dana da. A wannan lokacin ya yanke ƙauna don ji ya yi zama a gidan ya fice masa daga rai, gani yake zai iya haƙura da zaman gidan idan ya so duk wata sana'a da ya sani zai fita ya nema don ganin ya ci gaba da nemawa mahaifinsa lafiya. Yana gama nazarin ya miƙe ya ɗauki buhun kayansa, sai da ya leƙa ta window ganin hankulan mutane baya wurinsa ya sa ya yi zaraf ya fice daga ɗakin sannan ya zare sakatar gate ɗin ya fice daga gidan. Gudu-gudu sauri-sauri haka Kabiru ya fara tafiya, kasancewar unguwar shiru babu mutane ya sa bai haɗu da kowa a hanya ba, ta bayan wata doguwar katanga ya raɓa yana tafiya ba tare da ya san inda yake saka ƙafarsa. Yana tsaka da tafiya ya ji ya ci karo da mutum a gabansa, a hankali ya fara ja baya yana ƙoƙarin sake hanya ya ji mutumin da suka yi karo da juna yana faɗin, "Assalamu alaikum." Kabiru da ya fara tsorata a ɗan ja da baya sannan ya amsa masa sallamar, don gabaɗaya a rikice yake. Mutumin da har lokacin Kabiru bai tantance ko shi waye ba ya ci gaba da cewa, "Bawan Allah da wa ka dogara?" Kabiru ya fara sakin jikinsa don ya fahimci ɓoyayyan baƙonsa ne, murya can ƙasa ya ce, "Da Allah na dogara." Mutumin ya ƙara taku biyu zuwa gaban Kabiru ya ce, "Ka dogara da shi a ko'ina kake shi zai isar maka." Kabiru ya jinjina kai yana shirin yin magana, mutumin ya ci gaba da cewa: "Ina ƙaunarka fisabillahi don haka zan baka shawara karka ji tsoron kowa idan ba Allah ba." Kabiru na jin haka ya zaburo da sauri da niyyar kama hannun mutumin yana faɗin, "Don Allah wanene kai da kake yawan zuwa kana gaya min maganganu masu daɗi, da shawara akan al'amuran rayuwata?" Tun bai ƙarasa wurinsa ba mutumin ya ɓace, da sauri Kabiru ya hau waiwaye don neman wurin da zai ƙara ganin ɓullowarsa. Daga can bayansa ya ƙara jin muryarsa yana faɗin, "Karka damu da sanin wanene ni domin mai ƙaunarka na tare da kai a koyaushe, ni masoyinka ne ina mai ƙara tunasar da kai muhimmanci dogaro ga Allah." Yana gama maganar ya sake ɓace wa daga wurin. Jiki a sanyaye Kabiru ya jingina a jikin katangar, ban da kukan kwaɗi da ƙananan ƙwari babu abin da yake tashi a wurin. Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta aminta da nasihar da bawan Allahn nan ya yi masa, nasihar da Mahaifinsa yake yi masa ta sake dawo masa, a fili ya fara furta Astagfirullah sannan ya koma ya nufi hanyar gidansu Raihan.

  

     Inno kusan suma suka yi ban da juwa babu abin da suke ji, Huzaifa ya ƙarasa gabansu ya ya zaro musu ido. Suna haɗa ido suka ga ƙwayar idonsa na ci da wuta, kakin yawu ya yi ya tofar a kan tafin hannunsa nan take wuta ta tashi. Goggo tuni ta saki fitsarin da take matsewa ta sunne kai ƙasa cikin tashin hankali, Huzaifa ya buga musu tsawa yana faɗin, "Duk wacce ta sake gangancin shiga lamarin Raihan sai na banka mata wuta ta ƙone ƙurmus, kuma duk wacce ta sake ta furta wata magana a kaina da abin da ya faru sai na hallata shi cikin dare." Huzaifa ya ɗago ya damƙi wuyansu sannan ya ci gaba da cewa, "Kuma duk wacce ta ce za ta bar gidan nan tana fita zan ɗaye fatar jikinta." Inno da idonta yake runtse ta ce, "Babana mun gode, ko a ɗakin nan ka ce mu dauwama har ranar mutuwarmu mun bar sauka ƙasa." Huzaifa bai bi ta kansu ba ya ɗebe su ya watsa a saman fanka, sai ga su Inno a maƙale jikin fanka sai ciccila ƙafafuwa suke yi. Sai da suka jigata sannan ya miƙa hannunsa ya ɗauko su yana nuna musu zannuwansu dake can gefe ya ce, "Maza ku ɗaura zaninku ku fice daga ɗakin nan." Tun bai rufe baki ba Su Inno suka fara wawurar zannuwansu suna yi suna layi kamar waɗanda suka maku saboda juwar da take ɗibansu. Suna zuwa bakin ƙofa Daddy ya turo ya shigo mommy tana biye da shi Inno ta kusa tafiya luuuu za ta faɗi da sauri Daddy ya ruƙota yana faɗin, "Inno lafiya?" Inno ta fisge jikinta tana faɗin, "Sake ni ka ji Audullahi, jeka kan Raihanu Allah dai ya watsawa Likitanan albarka." Daddy ya yi murmushin jin daɗi don ya ga sauyi a wurin Tsofaffin saɓanin kafin fitarsa da ya tafi suna kwashe wa Likita albarka. Su Inno na fita suka zube a bakin ƙofa suna mayar da numfashi, Goggo ce ta fara rarrafawa tana sauka daga ƙafar bene, Inno ta leƙa tana faɗin: "Kai jama'a yanzu a daren nan za ki rarrafa Zinaru sai makarai sun makeki a hanya." Goggo da ta gama zuwa wuya a zuciye ta juyo ta ce, "Yooo shi wanda kika kuɓuto daga hannunsa Mutum ne? Ki yi ta kanki daga nan ni kam Albasu zan wuce don na tabbata ko ba aljani bane yana cikin ƙungiyar asiri, don wallahi mutum ba zai aikata abin da ya yi ba idan ba haka ba Malam mai allo bai haife ni ba." Nan take cikin Inno ya sake kaɗawa da sauri ta fara rarrafawa ta bi bayan Goggo suka sauka, suka wuce ɗakinsu.

   Su Inno na fita Huzaifa ya koma kan Raihan tare da gayyato Jabin Raihan don ta maye masa gurbin Raihan ko ya samu ya sake dulmiyar da su Daddy ga zuwa ƙasar Indiya, saboda matuƙar suka je Indiya hakan zai taimaka masa wurin gano takamaimai abin da yake faruwa da ita. Kafin ƙiftawa ido sai ga Jabin Raihan ta fara motsawa tana sauke ajiyar zuciya, Sai dai babban abin da ya fi ɗaga masa hanakali da ya so ɗaukar gangar jikin Raihan zuwa Tsauninsa abin ya gagara, wannan ya sake tabbatar masa da akwai ɓoyayyan al'amari a dangane da ciwon Raihan, tashin farko Mugaza ce ta faɗo masa don ya san akan baƙin kishinta tana iya aikata komai don biyan buƙatarta. Daddy ne ya tsinke masa tunanin da yake yi yana faɗin, "My Raihan barka farkowa." Mommy da ke gefe ta ce, "Sannu Raihan." Da ido take bin su da kallo tana gyaɗa musu kai tamkar ƙadangaruwa. Mommy ce ta koma daga ɓangaren Raihan ta tsugunna ta fara karanta ayatulkursiyyu tana tofa mata, da sauri Huzaifa ya zabura ya matsa gefe cikin huci a gaggauce yana faɗin, "Shi kenan yanzu zan wuce Alhaji duk abin da ake ciki za ku ji ni saboda akwai wani patient da yake jirana." Daddy ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin jin daɗi ya ce, "Ba damuwa na gode sosai Dr." Da sauri Huzaifa ya yi gaba har ya je bakin ƙofa Daddy ya ce, "Dr babu wani magani da za a ƙara mata akan na da ka san fa wancen ya ƙare." Huzaifa ya fara sosa kai sannan ya ce, "Babu damuwa zan turo maka text ta waya." Tun bai jira cewar Daddy ba ya fice daga ɗakin.

A hankali Mommy ta ɗago Jabun Raiha tana yi mata sannu, Daddy ya zauna a ɗaya ɓangaren sannan ya riƙo hannunta ya ce, "Allah ya baki lafiya My Raihan." Jabun Raihan ta ɗago tana gyaɗa kai. Mommy ta miƙe tana faɗin, "Mu je na raka ki, ki yi sallah kin ga Magriba ta wuce ga Isha'i ita ma tuni an yi ta." Ras gaban Jabun Raihan ya faɗi don ko kaɗan bata ƙaunar sallah ba abin da ta ƙi jini irin ta ji an ambace ta. Idan aka ce ta yi ma bata san ta inda za ta fara ba tun da ba addininta bane, tana cikin nazari ta riski muryar Daddy yana faɗin, "Haba Zainab yaushe yarinyar nan ta farfaɗo, don Allah ki bari ta huta ta ci abinci ta sha magani tukunna." Mommy ta ɓata fuska tana faɗin, "Daddy babu wani uzuri game da mara lafiya a kan sallah, hatta majiyacin da yake kwance baya iya tashi matuƙar yana cikin hayyacinsa dole a yi masa alwala ko yana daga kwance ya gabatar da sallah..." Daddy ya katse Mommy cikin ɓacin rai yana faɗin, "So kike ki kafirta mu ni da Ƴata kenan? Ce miki na yi ba za ta yi sallah ba? Ki fita idona Zainabu akan katsalandan ɗin nan da kike min yana neman wuce gona da iri." Mommy ta miƙe cikin fushi ta fice daga ɗakin don ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba.

 

     A hargitse Raihan ta waiga don ganin wanda yake shirin dakatar da ita ga cika umarnin Abar bauta, tana waigawa ta hangi Alhaji Ƙarami abokin mahaifinta. A hankali ya fara takowa gabanta cikin izza yana faɗin, "Matata ce irin dana dasa don ya ci gaba da yaɗo domin samun farinciki da rayuwa mai morewa." Raihan cike da ƙarfin gwiwa ta juya wurinsa tana cewa, "Wa'adin yabanyarka ya zo ƙarshe don a yanzu ba sai gobe ba zan sallamawa abar bauta jininta, ko mahaifana basu isa su dakatar da ni ga aiwatar da wannan kudurin ba." A zabure Alhaji Ƙarami ya fisgo Raihan da niyyar illata ruhinta, da sauri ta kauce ya kaiwa ƙasa duka. Duk abin da yake faruwa babu wanda ya lura daga masu naƙudar dake cikin halin naƙuda har zuwa Nurses ɗin da suke taimaka musu. Raiha ta kalle shi a fusace ta nuna shi da yatsa tana faɗin, "Ka fita a ido tun ban hallaka ruhinka kai da matarka ba, ka barni na yi abin da ya kawo ni tun ban fusata na yi ɓarnar da za ta girgiza ruhinka ba." Ko ba a faɗa ba Alhaji Ƙarami ya san wacece Raihan a cikin Daular ƙungiyar asiri, dukda ba ƙungiyarsu ɗaya ba ya samu labarinta da jimawa a wurin Babban Dodo, tun da jimawa ya so ya ringajayi ruhinta zuwa ta su ƙungiyar amma Huzaifa ya yi kaka gida ya hana shi aiwatar da abin da ya yi niyya. Amma dukda ya san wannan ƙarfin iko nata ba zai hana shi tsayawa tsayin daka don ganin ya ƙwato rayuwar Matarsa ba don ita ce komai na shi a rayuwa. Ya kalleta cikin dakiya da ƙarfin zuciya ya ce, "Na salwantar da rayuwar Mahaifana don cimma burina, na sadaukar da ƙwayoyin haihuwar  jikin matata don samun farincikina, duk wani ɗigon numfashi da matata take yi ƙarin arzikina ne, matsawar babu ita duk wahalar da na yi ta tsawon shekaru ta kau don haka dole na dakatar da ke." Raihan na cikin sauraronsa ta ji kuka jariri a gefenta tana dubawa ta ga ta biyun ce ta haihu sai Matar abokin mahaifinta da suke taƙaddama akanta ita kaɗai ta rage, Raihan ta bushe da wata mahaukaciyar dariya haɗe da dukan ƙasa wurin, nan take wasu manyan kunamu suka fara fitowa suna tunkarar wurin da Alhaji ƙarami yake, da sauri suka fara rarrafawa har suka mammaƙale a jikinsa suka fara kai masa sara ta ko'ina. Da sauri ta koma kan matarsa da take cikin wani hali tana nishi da alama ita ma kan jariri ya fara hararamar fitowa, juyawa ta yi wurin da Kunamun nan suke fitowa ta sa hannu ta ɗauko guda ɗaya ta leƙa ƙarƙashin matar ta tura mata kunamar ta cikin gabanta. Lokaci ɗaya matar ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara, Raihan ta saki wani shu'umin murmushi ta waiga wurin da Alhaji Ƙarami da yake ta ƙoƙarin ganin ya ƙwaci kansa ta hanyar amfani da tsafi da sihiri, amma tuni kunamun suka kaishi ƙasa. Takawa ta yi har gabansa ta tsugunna a saitin furkarsa ta furta, "Da ka barni na yi abin da yake gabana da ka ceci rayuwarka, ba na son shisshigi a lamurana don haka bana jira ga duk wanda zai kawo min matsala." Tana gama maganar ta miƙe zuwa gaban Matar Alhaji ƙarami da Nurses suka rufu a kanta don ganin sun kawo mata ɗauki, tana nan tsaye Likita ya ƙaraso kanta don har ya fara tunanin a yi mata CS Raihan ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo sannan ta ɗauki ruhin Matar Alhaji Ƙarami ta wuce da ita zuwa kogon tsafinsu.

   A gaban abar bauta ta ɗire ta a lokacin tuni ta fara fita daga hayyacinta saboda irin saran da kunamar take yi mata, Abar bauta ce ta miƙa hannunta ɗaya daga cikin hannuwa sama da Ashirin cikin ƙasan matar, da ƙarfi ta fisgo kunamar da aka saka mata. Wata uwar ƙarar ta sake ƙwallawa kamar ranta zai fita, Abar bauta ta sake tura hannunta a karo na biyu ta fisgo jaririn cikinta da tuni ƙungiyar asirin Mijinta suka zuƙe masa jini. Abar bauta wurgi ta yi da jariri zuwa ɗaya daga cikin kawunan jikinta nan take suka yayyage shi da haƙwaranta suka fatattaka namansa. Abar bauta ta dubi Raihan da ke tsaya ta fara magana da muryarta mara daɗi, "Aiki ya rage naki yau mun baki wuƙa da nama." Raihan na zuwa ta kafa kanta a ƙirjin matar za ta zuƙu jini da sauri abar bauta ta dakatar da ita da cewar, "Ba iya jininta kaɗai muke buƙata ba, muna buƙatar ki ɗebo mana kayan cikinta kafin mu sha jini, a cirowa Autan kai zuciyarta ya cinye." Raihan na gama sauraronta ta tsugunna tana kallon hannunta nan take wasu irin manyan farata suka fara tsiro mata a hannu masu kaifi da tsini kamar mashi, waɗansu manyan fiƙoƙi masu kama da fiƙoƙin zaki suka fara tsiro wa a cikin bakinta. Hannuwanta ta tura cikin gaban matar faratanta na ratsa cikin jikinta har ta samu nasarar kwaso kayan cikinta, wata irin gigitacciyar ƙara take kwararawa iya ƙarfinta tun tana cikin hayyacinta har ta fita daga hayyacinta. Kamar yadda harshen kare yake lallagi hara Raihan ta zaro harshenta ta fara lasar jinin jikin kayan cikin. Tana gama siɗewa ta wurgawa Abar bauta ta karɓe ta haɗiyesu. Hannuwanta ta ƙara sawa a daidai ƙirjinta a lokacin tuni rai ya fita daga jikin matar, da zaƙwa-zaƙwan faratanta da farke kirjin matar ta zaro zuciyarta ta miƙawa Autan kan da ke jikin Abar bauta, ta saka kanta a saitin wurin da ta ciro zuciyar ta fara zuƙar jinin jikinta.

Raihan sai da ta sha jini ta yi ƙat sannan ta ɗago, tana sauke ajiyar zuciya. Hatsabibiya na zuwa ta ja gawar matar zuwa ɗakin arziƙi ta wurgata ciki. Wata irin guɗa ce ta tashi a wurin mai haɗe da walƙiya nan take ƙofar ɗakin ta shafe kamar ba'a taɓa ƙera ƙofa a wurin ba. Abar bauta ta dubi Raihan cikin farinciki ta ce, "Kin haure mataki na farko a cikin ƙungiya yanzu za ki wuce zuwa mataki na gaba, muna buƙatar jinin Mahaifiyarki. Za mu sassauta miki don ba za mu bari ki hallakar da ita da kanki ba, ungo wannan." Abar bauta ta miƙawa Raihan wani kaifaffan ƙashin bil'adama, sai dai kafinsa tamakar kaifaffiyar wuƙa haka yake. Ba musu Raihan ta ƙarasa ta amsa da hannu bibbiyu tana jiran umarninta.

Abar bauta ta miƙe tsaye tana faɗin, "Wannan da kike gani ƙashin bayan mahaifiyata ne, ki je da shi ki yanki ɗan ƙaramin yatsan mahaifiyarki ki kawo mana sauran aikin yana gare mu idan kika yi haka kin haure mata ki na biyu idan kika tafi mataki na ƙarshe tayuwu matsayinki ya zarce namu domin ke ɗin ta musamman ce, kina da bambamci da mu ƙungiya tana alfahari da ke." Raihan ta russuna cikin girmamawa sannan ta fice daga kogon dutsen.
    A lokacin da ta koma gida, gidan ya yi tsit babu kowa da alama duk sun yi bacci. A can gefe ta hangi Mama Uwani da wata mai siffarta a cikin ɗakinta. Ko kaɗan bata damu ba don a baya ma ta ga irin haka, sai ta yi tsammanin duk yana daga cikin aikin abar bauta ne. Kai tsaye ɗakin Mahaifinta ta wuce don tasan a cen mahaifiyarta take kwana, Daddy ta hanga a kan kujera yana danne-danne a laptop ɗinsa a gefe ɗaya ga cool misic yana tashi don idan yana aikin dare ya fi jin daɗin aiki yana jin sanyayyar waƙa musamman ta turawa. Bata bi ta kansa ba ta ƙarasa gefen gadon da Mahaifiyarta take kwance.

😰RASHIN TAUSAYIN RAIHAN YA FARA YIN YAWA, INA TSORON TA ZAMA SHUGABA A WURIN. WAI INA LABARIN KABIRU KUMA WANENE MAI YAWAN BASHI SHAWARAR NAN? SHIN ABOKIN DADDY YANA MUTUWA KO ZAI ƊAUKI FANSA AKAN MUTUWAR MATARSA? WANNE DALILI NE YA SA HUZAIFA ZAI SA A KAI RAIHAN INDIA? IDAN YA KAITA INDIA TA FITA DAGA ƘUNGIYA NE KO YAYA?🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️ CHAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE YI😂 MAZA HANZARTA KI BIYA NAKI KAR A YI BABU KE DON WANNAN SHI NE SHAFI NA BIYUN ƘARSHE💃🏼

Share Fisabilillah🌚
*ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

©  *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

      LAST FREE PAGES 10

     Ilahirin jikin Mommy ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda tsananin tsoro, firgici da tashin hankali. A takure take a ƙuryar gado ta sunkuyar da kanta ƙasa saboda tozali da ta yi wata shirgigegiyar mummunar hallita, girman hallitar ta zarce goggon biri ga wasu irin ƙwala-ƙwalan idanu da suka zazzago kamar za su faɗo ƙasa. Bakinta ban da fiƙoƙi babu komai a ciki sai ƙaton hancinta mai ƙofofi takwas, tare da manyan ƙahunhuna guda biyu. Sautin takun Hallitar kan iya nakasta dodon kunne don haka Mommy ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnenta da take jin sa kamar zai tarwatse, Hannuwan hallitar kama suke da ƙafafuwan doki don haka a duƙushe take tafiya rafkeken kanta shi ne a gaba. Jin shirun takunta ya sa Mommy ta ɗago da kanta a zatonta ko hallitar ta ɓace daga wurinta, sai dai tana ɗagowa suka haɗa ido da hallitar nan take ta hango Raihan maƙale a hannun hallitar tana kuka tana miƙawa Mahaifiyarta hannu, jikin mommy har rawa yake yi ta yunƙura don zuwa wurin hallitar tana faɗin, "Don Allah ki bani ƴata ita kaɗai na mallaka karki hallakata, Hallitar ce ta fara ja da baya tare da Raihan ta fara yunƙurin kai kan Raihan zuwa bakinta don ta laƙumeta, da sauri Mommy ta yunƙura cikin tashin hankali ta furta, "Raaaaihaaaaan."

(Allah sarki Uwa kenan😰 Duk tsanani Mahaifiya ba za ta so ganin abin da zai cutar da Ƴarta/Ɗanta ba.)

   Firgigita Mommy ta farka daga mummunan mafarkin da take yi, har lokacin da ta farka jikinta ban da rawa babu abin da yake yi. Da allon gado ta jingina a hankali bakinta na furta Ayatulkursiyyu don ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin ba. Raihan na gabda da yankar ɗan yatsan mahaifiyarta ta ji wani irn turiri ya yo kanta da sauri ta ja da baya don kaɗan ya rage bata ƙone ba. Farkawar da Mommy ta yi ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba don ta yi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta aiwatar da abin da yake tafe da ita. Daddy ne ya ajiye takardar hannunsa ya ɗago yana kallon wurin da Mommy take ya ce, "Lafiya dai Mommyn Raihan na ji kina ambatar sunan Raihan cikin dare." Mommy ta yunƙura da ƙyar jikinta gabaɗaya a sanyaye yake ta zauna a kujera mai kallon ta Daddy ta ce, "Daddyn Raihan wani mummunan mafarki na yi akan Raihan, ina jin tsoro matuƙa kar wani abu ya faru da ita. Maganar gaskiya ina tunanin babu shaiɗanu a lamarinta kuwa, kana gani ƙa'ida bana iya kwanciya ba tare da alwala ba kuma addu'a bakin gwargwado ina yi amma idan mummunan mafarki na tashi yi sai na da yarinyar nan a ciki..." Daddy ya yi murmushi sannan ya katseta da cewar, "Zainabu kenan, duk fa abin da kafi sawa zuciyarka yana tare da kai. Ba tun yau ba na sha gaya miki ki bar danganta ciwon yarinyar nan da wasu shaiɗanu, ki gaya min Raihan ina take zuwa da za ta kwashi shaiɗanu? Ƴarmu a killace take ban da makaranta tana zuwa wani wurin? Karki manta silar ciwon yarinyar nan tun bata fi shekara biyar a duniya ba muka wayi gari da shi, ta yaya za a ce wai wasu shaiɗanu suna bibiyarta kamar wacce take bin kwararo tana jari bola a kan sharar kasuwa." Mommy ta yi guntun tsaki tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Na rasa ya akayi idonka ya rufe haka, kana tunanin shaiɗanu sai a waje ake samun su Daddyn Raihan? Ganin su muke yi da za mu shaida kamanninsu? Idan a baya ta wayi ido da ciwo shin muna da lasisin da za mu tabbatar da cewar babu haɗin jinnu a jikinta..." Daddy ya ɗaga mata hannu da cewar, "Zainabu ni da ke muka haifi yarinyar nan, don haka ki nema mata maganin Aljanu tun da so kike ki jawo mana wata masifar muna fama da wannan, shi kenan ki sakar min mara na yi fitsari." Daddy ya ƙarasa maganar a fusace yana tattara kayan gabansa, ya miƙe ya wuce kan gado, jiki a sanyaye Mommy ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala sannan ta saka hijabinta ta nufi ɗakin Raihan don zuciyarta ta gara amincewa ta bari har gari ya waye, a hankali ta fara sauka daga bene sai dai duk taku ɗaya idan ta yi sai ta ji kamar ana bin ta a baya don sai ta ji takun tafiya, sai da ta kusa sauka daga bene ta yi ƙarfin halin juyawa amma wayam babu wanda ta gani. Idanunta ne suka sauka a kan agogon bangon da ke jikin bango wanda ya yi nuni da ƙarfe biyu da rabi na dare, wucewa ta yi hanyar da za ta sadata da ɓangaren su Raihan don gabaɗaya sashensu ɗaya idan aka cire sashen Daddy da yake ɓangarensa daban, a hankali wata sanyayyar iska ta fara kaɗawa mai haɗe da walƙiya tun iskar na kaɗawa kaɗan-kaɗan har ta fara ɗaga labulaye, ƙofofin ɗaki da na window suka fara rufewa da buɗewa a ƙarfi, da sauri Mommy ta fara waigawa don har lokacin bata daina jin alamun takun tafiyar da ake bin ta a baya ba. Tana cikin tafiya ta ga ƙwan fitilar ya fara ɗaukewa yana kawowa, ba shiri ta fara lalube har ta samu ta taɓa jikin bango ta ci gaba da tafiya a jikin bango. Daga bayanta ta ji ƙarar fashewar kwalba tuuuush, a firgice ta fara lalube tana ƙwalawa Daddy kira don iya tsoro ta gama tsorata uwa uba ga shi har lokacin bata daina jin takun tafiya a bayanta ba. Ƙwan fitilar ne ya tsaya cak ya daina ɗaukewa, mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da tafiya a gaggauce cikin sauri. Tana zuwa ta wurin windon da ya fita ta harabar gidan ta hango wata matashiyar budurwa a zaune ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, da mamaki Mommy ta tsaya tana kallonta sai jikinta ya fara bata kamar Raihan ɗinta don kusan yanayin jikinsu ɗaya, hatta doguwar rigar baccin irinta Raihan ce. Gashin kan yarinyar a barbaje yake ya rufe fuskarta ta yadda ba kya iya ganin ainihin fuskarta.

   Duk abin da yake faruwa tsakanin Raihan da Mommy Abar bauta tana kallo a cikin Kogon dutsen ƙungiya, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi da ganin Mommy na son bata matsala ba. Abar bauta na ganin Mommy ta fito don zuwa ɗakin Raihan ta yi wa Raihan  magana da cewa, "Ki hanzarta domin samun nasararki, a yanzu a wanni ne kaɗai suka rage miki don samun ci gabanki. Mahaifiyarki za ta fita ki yi ƙoƙari jan hankalinta zuwa harabar gidanku, sauran aikin ki bar min komai a hannuna ki dawo min da ƙashin bayan mahaifiyata don sauran aikin yana gare ni." Raihan da ke biye da a bayan Mahaifiyarta ta furta, "Biyayya gare ki ta zama wajibi fansar iyayena na gareki ya abar bauta." Raihan na rufe baki ta ci gaba da bin bayan Mommy, tana zuwa ta zauna a harabar gidan kamar yadda abar bauta ta tsara mata.

   Alhaji ƙarami ba ƙaramar azaba ya ci a hannun kunamun nan ba, sai da suka ga ya daina motsi sannan suka dakata da azabtar da shi, sakamakon umarnin da uwar ɗakinsu ta basu. Daga wurin da yake Dodon tsafinsu ya ƙarasa cikin takaici don ba ƙaramin haushi ya ji ba ganin ƴan wata ƙungiyar sun azabtar da ta su ɗan ƙungiya ba. A fusace ya kafawa Alhaji Ƙarami haƙora tun yana masa magiya har rai ya yi halinsa, sai da ya tabbatar da baya numfashi ya ɗaga shi yana faɗin, "Da ka mutu ta sanadin wasunmu gara mu ƙarasaka da hannunmu." Kusan lokaci ɗaya Alhaji Ƙarami da matarsa suka Mutu, Likitoci na kan matarsa ta jima tana wani irin fisge-fisge daga ƙarshe ta ce ga garinku nan.

     Kabiru yana tafe cikin zuciyarsa yana saƙa da warwara har ya ƙarasa cikin gidan, a lokacin da ya je ƙofar gidan a buɗe ya samu gate ɗin don haka yana turawa da ya shiga ya wuce ɗakinsa da yake a bakin ƙofa yake idan baka lura ba ma ba za ka san ya fita ba. Yana shiga ya ajiye buhun kayansa ya fito ya ɗaura alwala ya gabatar da sallar Isha'i ya yi shafa'i da wuturi . Ya jima yana addu'a da kaiwa Allah kukansa akan mummunar ƙaddarar da ta same shi daga ƙarshe bayan ya idar ya zauna ya fara tilawar alƙur'ani. Ya kusa awa guda yana karatu sai da ya gama sannan ya fito harabar gidan da babu mutane kowa ya kama gabansa, sai da ya kira Daddy a waya ya tambaye shi ko zai ƙara fita ya tabbatar masa da ya rufe gidan babu inda za shi kuma baƙi duk masu tafiya sun tafi.

  Sama-sama Mommy ta fara jin kamar ana ambatar sunanta, har ta yi kamar ta wuce ta ji ba za ta iya giftawa ta bar yarinyar da take ji kamar Raihan ɗin ta ba, don tuni zuciyarta ta fara ayyana mata ko ciwon Raihan ne ya tashi ta buɗe ƙofa ta fita harabar gidan ta zauna. Kai tsaye ta nufi hanyar da za ta sada ta da ƙofar fita, sauri-sauri ta fara yi har ta samu nasarar zuwa barandar harabar waje. Kamar wacce ake fisga haka Mommy ta fara jin zuciya da gangar jikinta na azalzalarta zuwa wurin da wannan matashiyar budurwar take bakin ta na furta, "Hasbunallahu..." Ta fara tunkarar wurin gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, lokaci ɗaya ta ji wani irin tsoro ya mamaye ta sakamakon jin kukan wasu irin tsuntsaye na tashi a saman kanta. Ta maza ta yi ta ci gaba da takawa har ta ƙarasa wurin da Raihan take zaune, Mommy ta fara ƙoƙarin kai hannu za ta taɓa gadon bayanta tana kiranta, "Raihan!" Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta amsa ba, Mommy ta sake sunkunyawa ta ce, "Raihan." A haukace Raihan ta ɗago tana bin Mommy da kallo, da sauru Mommy ta yi baya sakamakon tozali da ta yi da mummunar hallita. A madadin da ga fuskar irin ta bil'adam kamar yadda gangar jikinta ya nuna sai gani ta yi ta yage mata baki mai kamar na kura, cike suke da manyan haƙora da fiƙoƙi ga hancinta tamkar na kare haɗe da idanu jawur kamar garwashi. Mommy da ta faɗi can gefe ta fara ja da baya jikinta na rawa, Gadan-gadan Raihan ta fara takawa gabanta don ta bawa Abar bauta damar aiwatar da abin da yake gabanta. Cikin gigita Mommy ta fara karanta duk wata addu'a da ta zo bakinta, tana yi tana kiran sunan Daddy don ya kawo mata ɗauki.  Tana cikin wannan halin sai gani ta yi wannan hallitar da ɓace daga gabanta, da ƙarfin gaske ta ji ana fisgarta kamar za a yagi naman jikinta.

Kamar wanda aka tasa daga bacci haka fitsari ya farkar da shi, kasancewar ƙafa ta ɗauke ya sa Kabiru ya fito bakinsa ɗauke da addu'a don ya kewaya banɗaki. Bayan ya fito daga can bayan ɗakinsa ya fara jin motsi, har cikin zuciyarsa ya ji kamar ya leƙa ya ga abin da yake motsi amma sai ya yi tunanin dare ne ta yuwu ɓeraye ne suke dabdalarsu. Mommy na jin motsin Kabiru ta riƙa ƙwalla masa kira amma a banza ko kaɗan bai san ana yi ba, sai dai har lokacin bakinta yana ci gaba da karanta ayoyin Ubangiji, da abar bauta ta zo kawo mata cafka sai ta ga mommy ta zille mata kamar tarwaɗa. Kabiru na shiga ɗaki ya koma ya kwanta sai dai fir idanunsa sun bushe bacci ya ƙaurace masa, tashi ya ƙara yi ya fito a ƙofar ɗakinsa ya ɗaura alwala yana shirin shiga ɗaki ya ji ƙusur-ƙusur ɗin ya yi yawa. A hankali ya fara takawa yana haske-haske da ƙaramar fitilarsa, daga can bayan ɗakinsa ya hango Mommy a kwance sai shure-shure take yi tana motsa baki da alama magana take yi. Tsoro ne ya kama shi don ko a mafarki bai taɓa ɗauka mommy bace a wurin, a tsorace ya fara faɗin, "Hajiya lahiya kuwa?" Mommy hannu ta fara miƙa masa tana kiran sunansa, ganin haka ya sa Kabiru ya fara ƙoƙarin miƙa hannu don ya taimaka mata amma tunowa da abubuwan da suka faru da shi ya sa ya ja da baya yana karanto aytulkursiyyu ya fara tofa mata tare da falaƙi da nasi. Kamar wanda aka yi wa wankin kunne raɗau ya ji maganar Mommy a kunnensa saɓanin da; da baya jin abin da take faɗa, tsugunnawa ya yi a wurin yana faɗin, "Hajiya me ya fito da dake a tsakar daren nan?" Mommy da ta ji jikinta ya fara sarara mata ta ce, "Kabiru taimaka min ka kaini ciki kar su halaka ni." Kabiru ya zaro ido yana dube-dube yana shirin magana mommy ta dafo hannunsa da sauri ya yi baya yana kurma ihu don ya gama tsorata gabaɗaya. Abar bauta da take laɓe ta fara Allah-Allah akan Kabiru ya basu wuri don ta dawo ta ci gaba da abin da take niyyar aiwatarwa, donma ita kanta Mommy ba ƙaramar wahala suka sha akanta ba amma so take ko ta wanne hali ta samu ta lakuci jinin jikinta idan ya so ko da sihiri ne in sun kaiwa ɗakin arziƙi jininta magana ta ƙare. Kabiru har zai shige ɗaki da gudu sai wata zuciyar ta ayyana masa ta yuwu ita ma shaiɗanu sun yi mata abin da suka yi masa ne har suka tsorata ta fito. Bakinsa ɗauke da addu'a ya sake tunkararta Mommy ta dafa kafaɗarsa ta miƙe tsaye tana layi, da ƙyar ta iya tsayawa a kan ƙafarta ta fara takawa da ƙyar kanta na ci gaba da sara mata. Kabiru na raka ta bakin ƙofa zai juya fir mommy ta ƙi yarda don har sa da ta saka Kabiru ya rakata har ƙofar ɗakin Daddy sannan ya koma ɗakinsa, tana shiga ta zube a bakin ƙofa tana ci gana da karanta duk ayar da ta zo bakinta. A lokacin da ta koma ɗakin tuni Daddy ya yi bacci, da rarrafe ta fara rarrafawa zuwa bakin gadon tana kiran sunansa. Sai dai babban abin da ya sake firgitata yadda ta ji yana sauke wani irin munshari mai ban tsoro, ga ƙwan ɗakin da fara ɗaukewa yana kawowa.

   Raihan da abar bauta kusan tare suka koma kogon dutsen ƙungiya kowannensu fuska babu walwala, abar bauta ta dubi Raihan rai a ɓace ta ce: "Mahaifiyarki za ta bamu matsala domin tana da riƙo da addini. Sannan wannan Bafulatanin yana ƙoƙarin wargaza shirinmu tabbas za mu ɗau mummunan mataki a kansa, amma fa duk da haka Mahaifiyarki bata sha ba domin za mu ɓullo mata ta sigar da ba za ta taɓa tsammani ba. A yau saura kwana biyar ta fara al'ada don haka zan yi amfani da wannan lokacin, domin alƙawarinta na yi ga ɗakin arziƙi." Raihan ta jinjina kai cikin girmamawa, abar bauta ta nuna wata ƙaramar ƙorama ta ce,: "Ki ɗebi ruwan wanke zunubi ki yi wanka domin kin karya ƙa'idoji da dokar ƙungiya." Raihan na yin wanka kamar yadda Abar bauta ta umarceta ta fice daga kogon dutsen.

Intisar ce ta ɓullo daga ƙarƙashin ƙasa ta yi gaisuwa ga abar bauta, kusan cikin haɗin baki suka furta, "Huzaifa zai aika da Raihan ƙasar India don bincike na musamman akan Raihan." Abar bauta ta yi murmushin takaici ta ce, "Na san da haka shi ya sa na nemo ki yanzu. Zai kaita India ne wurin Kakansa Jibbul-Ƙasi don ya yi mata bincike a kanta, ya ɗora zarge-zarge akanta ciki kuwa har da ke." Intisar ta jinjina kai sannan ta ce, "Tabbas na san za a yi haka domin na san wanenen Huzaifa da bin didiginsa."  Abar bauta ta miƙe tsaye sai da ta yi zagaye wurin sau uku sannan ta ce, "Ba zai yi nasara a kanmu ba, domin za mu mallakawa Raihan duk wani ƙarfin iko, idan a da bata san wacece ita ba ya zama dole mu sanar da ita ta hanyar sakata a ɗakin arziƙi." Hankali a tashe Mugaza ta ɗago tana faɗin, "Kina nufin tun yanzu za ta mallaki shuɗaɗɗan ruhi ba sai nan gaba ba ya Abar bauta." Abar bauta ta ci gaba da tafiya tana jinjina kawunan jikinta ta ce, "Alƙawarin ƙungiya baya tashi, matsawar Huzaifa ya kaita wurin kakansa tabbas sai ya gane shirinmu kuma sai Kakansa ya wargatsa ƙungiyar nan. Idan kuwa muka saka mata shuɗaɗɗan ruhi dole zai zama garkuwa a gare ta, za ta gagari Jabbul-Ƙasi da dukkan wani shirinsa.

WASAN YA FARA ƊAUKAN ZAFI🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ RAIHAN TA KUSA ZAMA SHUGABA LIKAFA TA CI GABA😂😂  MENENE ALAƘAR SHUƊAƊƊAN RUHI DA RAIHAN, SHIN DAMA RAIHAN NA DA WANI A ƘUNGIYAR ASIRI NE DA HAR RUHINSA ZAI MAYE GURBINTA KO YAYA? WACCE ALAƘA CE TSAKANIN SHUƊAƊƊAN RUHI DA KAKAN HUZAIFA JUBBUL-ƘASI? CAKWAKIYAR ƘARA GABA TAKE🥵  MAZA HANZARTA KI BIYA DON JIN YADDA ZA TA KASANCE GARA KI BIYA 300 KI KARANTA AMMA IDAN NA KAMMALASHI SAI KIN SAKA 500 ZA KI SAME SHI🥱🥱🥱  WANNAN SHI NE SHAFIN ƘARSHE WATO SHAFIN ƘAUTA😎 MU JE ZUWA ƳAN GROUP ƊIN *ZAUJATU PAID* A CI GABA DA GASH SUYA SAI RANAR BIKIN NAƊIN 👸🏻 RAIHAN A ƘOGON DUTSEN ƘUNGIYA🤸🏻‍♀️💃🏼

SHARE HILIS🌚

No comments